Friday 4 October 2019

ALLAHU AKBAR: DAGA KARSHE SUNYI KWANCIYAR DA BABU RANAR TASHI

Tura Wannan Zuwa Ga
Sun tafi sun kwanta acikin kasa ba dan suna so ba, sai dan ajali yayi kira kuma kwana ya kare, anyi ciwo an sha wahala rayuwa tayi ƙunci daga karshe sun yi kwanciyar da babu tashi.


Rayuwar Duniya Kenan


Marubuci: Abdulhadi Isah Ibrahim

Haka kwanaki suke karewa akan mu, za muyi ta tafiya har zuwa ranar da za'a yi mana sallar da babu ruku'u balle sujuda, nayi zaton kwanaki zasu rike mun amana, nayi zaton shekaru za suyi yawa a kaina, sai naga sun kare mun a wannan rana.

Na yi burin abubuwa a rayuwa amma burin bai cika ba gashi ajali ya sauka a kai na, nayi burin na faɗi wadansu maganganu ga masoya na amma numfashi yayi tsada a yau, yau nine cikin Makara na shigo a makare Ya rabbi ka yafe ni, da ace na san Mala'ikun mutuwa suna hanyar zuwa gare ni dana bayyana password dina ga yan uwa na, bayan sun dawo gida daga rufe ni su rufe Facebook dina, in sun rufe ni su rufe WhatsApp dina.

Sai dai rai yayi halin sa, makomar mu gun Allah, lallai naso ace kafin raina ya fice na nemi yafiyar wadanda na bata musu, sai dai mutuwa ta sanya min ankwa, da ace nasan wannan shine ramin da za'a sanya ni da na koma zuwa ga Allah tun kafin yau da aka komar dani zuwa ga Allah, lallai jiki yayi nauyi, kwanaki sun juya zuwa tunanin ranar haihuwa ta.

Yau ce ranar da zan kwanta kwanciyar da Umma ta baza ta iya tashi na ba, balle masoyiya ta, tashi na sai ranar tashin Shugaban halittu annabin da aka aiko zuwa gare ni (S.A.W), laifukan da nake yi nayi tunanin gyarawa da zuciya ta amma gaɓoɓi na sun ci amana ta, buri ya yaudare ni, nayi tunanin Zan samu shekaru masu yawa sai gashi ajali ya sauka a kaina.

Tunani nake yi, yaya cikin gidan mu zai kasance idan za'a fitar da gawa ta zuwa ga sallah? zan zamo abin labari, za'a rinka cewa a lokacin da wane yake raye kaza da kaza, amma fa ada nine nake labarin matattu, yau nine ake labari, naso na rike sallolin Nafila da farillai akan lokaci, rayuwa ta rude ni, yau nine ake wa sallah, nine ake tunawa, kafin sati guda nasan zasu daina tunawa dani.

Za suyi hawaye za su yi kuka dangi na, yau itace ranar karshe ta zama a wannan duniyar, ranar farko ta rayuwar ƙabari, yau dai ido zai rufe rufewar karshe, nayi burin na zamo kamar wane, ashe shi wane yana da sauran rayuwa tawa ce ta iso gare ni da gaggawa.

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA KADAN DAGA CIKIN MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'UMMA GABA DAYA CIKIN GAGGAWA

SHIN KO KASAN ZA KA IYA SABAWA ALLAH AMMA DA SHARUDA GUDA BIYAR?

KARANTA YADDA RAYUWAR AURE TA LALACE A WANNAN ZAMANIN DA MUKE CIKI

Da ace nasan kwanaki na sun kare da banyi burin wasu abubuwa ba, ciwo yayi tsanani, ya ku 'yan uwana ku dai na sayo magani ku daina nemo likita, wannan ajali ne ba ciwon tashi bane, sai dai rashin sani yasa kuke wahala akai na, da ace kun Sani zaku jira fitar rai ne kawai, daga nan ku kai ni kushewa ta, Ya Allah gashi za'a miƙa ni gare ka cikin ƙabari na Ya Rabbi ka yafe ni ka kauda kai daga zunubbai na, rayuwa tayi nisa ga dukkan mai dogon buri da ace yasan ajalin sa na kusa".

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user