Friday 22 September 2017

NA TSINCI NAIRA ₦500 KOZAN IYA AMFANI DAITA BATARE DA CIGIYA BA ???

Tura Wannan Zuwa
Tambaya

Assalamu alaikum malam wani bawan Allah ne
ya tsinci Naira 500, kuma baiga wadanda zai
yiwa cikiya ba...

Kuɗin Nigeria ₦1000,₦500,₦100,₦50,₦20,₦10,₦5


Yaya kamata yayi da wannan kudin tsintuwar ?

Suna ajiye yanzu haka kusan wata daya kenan.

(Daga Ibraheem Ishaq Rano).

AMSA:


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

To dan uwa idan mutum yayi tsintuwa ya wajaba
a gareshi yayi cigiya har tsawon shekara guda,
idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya
amfani da ita, amma idan mai ita yazo daga baya
zai biya shi.

Kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisinsa mai
lamba ta: 5761.

Amma idan abin daya tsinta dan kadan ne
bashida yawa, to ya halatta yayi amfani dashi
koda baiyi cigiya ba.

Saboda abin da aka rawaito cewa:

Annabi (s.a.w) yaga wani dabino akan hanya, sai
yace:

In banda ına tsoron kona sadaka ne da naci.
Muslim ya rawaito a hadith mai lamba ta:2527.

Sai hadişin ya nuna dan karamin abu baya
bukatar cigiya.

Malamai şun yi sabani wajan iyakance tsintuwar
da bata bukatar cigiya.

Wasu sun ce za'a koma al'adar mutane, duk abin
da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to
idan an tsince shi baya bukatar cigiya, Ibnu
Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa:
Bai wajaba mutum yayi cigiyar abin da bai Kai a
yanke hannu saboda shiba, wato daya bisa hudun
dinare.

Haka nan sayyadina Aliyu (R.A) ya tsinci dinare
daya yayi amfani da ita batare da yayi cigiya ba.

Abin daya gabata yana nuna cewa:
mutukar baka sami mai Naira (500) din da ka
tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta kayi amfani
da ita batare da cigiya ba, tunda ba kudine mai
yawa ba, kuma mai ita bazai kwallafa rai
Akantaba.

Domin neman karin bayani aduba: Al-mugni
6/351.

Allah shine mafi Sani.

Source By ©Tafarkin Tsira
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user