Friday 22 September 2017

A Matsayin Ki Na Budurwa Ki Kula da Wannan Kafin Ki Fara Yin Soyayya

Tura Wannan Zuwa Ga
1.K tsayar da saurayi guda daya tak na kirki
bisa la akarai da ayyukan sa da halayensa na
zahiri.

2. Ki tabbata kina sonsa sosai kuma shima yana
sonki sosai.

3. Kada ki yarda kidade da saurayi, ko kishaku
dashi ko ki nuna masa tsananin so batare da
iyayensa sun gana da iyayenki ba.
In yaqi turosu kirabu dashi tunkafin yagama sace
zuciyarki.

4. Kizama mebin shawarar iyayenki, da neman
shawararsu a harkar soyayya, kada kibi shawarar
Qawaye ko saurayi kobin shawarar zuciyarki.

5. Kada kiyarda a kawo miki gulmar saurayinki
ke kuma kidauka koki kama zargin sa.
A'a sai kinyi bincike na adalci ko kingani da
idonki.

6.K ki kuskura kiyiwa saurayinki qarya
kizama me fada masa gaskiya ,da yimasa
bayanin komai iya saninki.

7. Ki zama me yawaita addu'ah da bawa Allah
zabi a dukkan lamarinki..

8. Ki kiyaye zargi da binciken laifinsa matukar ya
sanar dake komai bai 6oye miki gaskiya ba.

9. Ki dauka dan adam tara yake bai cika goma
ba, kinga zai iya kuskure, dan haka sai kiyi masa
afuwa.

10. Kizama me kare mutuncin kanki ,da kuma
kulada matsayinki batare da girman kaiba ko jan
aji ga masoyi...

JAN AJI A SOYAYYA BA ABIN DAYAKE
HAIFARWA SAI NADAMA.

idan saurayinki ya tsaneki ko yagudu yabarki ko
kin rasa wani abu da yake baki, kiyi haqury kada
kijuya masa baya, kisa masa shakka a ransa
yadinga tunanin anya kuwa kina son sa da
gaske ???

KEDAI KAWAI KI KARE MUTUNCINKI DA IYA
TAKUNKI

11. Kada kiyarda ki sakarwa saurayinki fuska
yana shigo miki da kalmomin da basu daceba ko
dabi'u.
kamar yace zai samiki zobe, ko zaiga awar
waronki ko zaisa miki jaka, ko zaiga fulawarki ,ko
zai auna kaurinki dadai sauransu.

SABODA HAKA KIZAMA ME BATA RAI ADUK
SADDA KIKAGA HAKA, KODA YATAFI KIRABU
DASHI, DAMAN BA NAGARI BANE, SOYAKE YA
BATAKI.
Wakilin shaytanne.

12. Kizama me yiwa saurayinki Al-qawarin nuna
masa soyayya bayan aurenku, sannan dayi masa
biyayya dai dai gwargwadon
iyawarki.

KISANI DAYAWAN SAMARI AKWAI
MAKIRCI.

Wani yasan ba aure zaiyi ba amma zaizo yabata
miki lokaci.

Wani soyake yakoyi zance sai kawai yazo
wajenki yayi tayi miki qarya batare dakin fargaba
zai dasa miki ciwon so, YA KORAR MIKI
SAMARIN KI NAKIRKI.

Wani kuma kawai so yake yana zuwa wajen fati
dake.

Saboda haka zaina saya miki kaya kala kala yana
fira da ke zai fake da cewa SAI YAGAMA School
KO SAI BAYAN YAGAMA KARATU ZAI TURO
KUYI AURE.

Duk fati ko fikines zai daukeki kutafi.
Wani kuma soyake kawai yana taba jikinki yaji
dadi koda bai kwanta dakeba, saboda
haka zaita binki sauda qafa yana
soyayya dake.

Wani kuma so yake ya bataki.

Irin wadannan samarin sunfi kowanne hatsari.

Idan yaganki yana sonki yana fara karantar
halayenki IDAN YAGA KE USTAZIYACE TO ZAIYI
SHIGAR USTAZAI HARDA
LITTAFIN SA A HANNU ,HAKA ZAITA KAFA MIKI
TARKO HARSAI KIN FADA.

Idan yaga 'yar BOKOCE zai fito miki a dan boko.

Idan yaga ke 'yar duniya ce toshima a hakan zai
fita.

Irin wadannan samarin har kayan mungani
munaso suna kaiwa budurwa, har iyayensu suna
turowa daga qarshe daya kwanta dake shikenan
yabiya buqatarsa, bazai bari kisami cikiba zaibaki
ƙwaya da zarar yaga baki da ciki yasan yayi free
tunda yasami abinda yake nema, zai ƙirƙiri laifi
yalaƙa miki domin ku6ata a karbo kayan sa daga
gidanku, koma yabar miki kayan...

Irinsu akwai makirci da nuna tsagoran soyayya
ga budurwa, domin sukanyi kukan hawaye a
gaban budurwa duk da sunan so amma yawanci
domin ya raunana zuciyar kine.

Yakan maqale miki har unguwa yana rakaki koda
yaushe.

YAR UWA IN SOYAYAYYA TAI GARDAMA WAYE
YAFI SHAN WUYA DA
TOZARTA ???

SHIN ANAIWA NAMIJI CIKIN SHEGENE KO
BUDURWA AKEWA ???

IDAN ABIN KUNYA YAFITO WAYE ZAI ZAUNA A
GIDA KO MAQOTA BAI ZUWA
DAN KUNYA NAMIJI KO MACE ???

MEYASA NAMIJI ZAI IYAYIWA YAN MATA BIYAR
CIKI BATARE DA AURE BA AMMA INYAZO
NEMAN AURE SAI ABASHI ???

IDAN KUWA MACE TAYI CIKI SAU DAYA DA
KYAR TAKE AURUWA KOMA SAI TABAR
GARIN ???

MEYASA MACE INTAI CIKI AGIDAN SUMA
TSANARTA AKEYI ,AMMA NAMIJI DAYA KAWO
RAGO DA KUDIN ICE SHIKENAN ???

MATA NAWANE SABODA CIKIN SHEGE
SUKABAR GARINSU KO RAYUWARSU
TA GURBATA AMMA SHI NAMIJI KAMARMA
BAIYI KOMAI BA ???

KO KAMUWA KIKAI DA MUGUN CIWO
WAZAI KULA DAKE YABAKI KUDIN MAGANI DUK
WATA ???

KINTABA GANIN ANSA WUQA A
WUYAN NAMIJI ANCE INBAKA FADI WACCE
KAYIWA CIKIBA SAINA YANKAKA ???

AMMA WA AKEWA HAKA ???

'Yar uwa kada dadin soyayya, ko dan kudin da
saurayi zai baki kodan zai saki a gaban mota
,kodan wasu yan riguna dazaina saya miki
HAKAN TASA KIBASHI DAMA HAR YASANKI
'YAMACE WALLAHI KIN KADE.
IN HAKAN TAFARU TO KITUBA GA
ALLAH (S.W.T) DOMIN SHI MAI GAFARANE.

FATAN "TAFARKIN TSIRA" ANAN SHINE, ALLAH
YASHIGA TSAKANIN NAGARI DA MUGU.

ALLAH YAHADA KOWACE YA MACE DA SAURAYI
NAGARI DA ZATA KAISU
GA AURE NAGARTACCE.

MUMA MAZAN ALLAH YABAMU MATA NAGARI.


Source: Tafarkin Tsira
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user