Friday 22 September 2017

Jagoran IPOB ya garzaya kotu

Tura Wannan Zuwa Ga

Kungiyar IPOB mai fafutikar kafa jamhuriyar
Biafra a Najeriya ta kalubalanci umarnin kotun
da ya ayyanata a matsayin kungiyar ta'addanci.

Lauyan kungiyar, Ifeanyi Ejiofor, ya shaida wa
BBC cewa kungiyar ta shigar da kara a kotu
domin kalubalantar matakin da gwamnatin
Najeriya.
Takardar karar wadda kungiyar ta shigar a ranar
Juma'a, ta ce IPOB ba ta kaunar tashin hankali.

Ta ce saboda haka hukuncin da wata kotun
tarayya da ke Abuja ta yanke na ayyanata a
matsayin kungiyar ta'addanci "ya ci karo da
doka."

Har ila yau Mista Ejiofor ya ce ba a yi wa Kanu
adalci ba domin bai halarci zaman da kotu ta yi
kafin a ayyana kungiyarsa a matsayin ta ta'adda
ba.

A ranar Laraba ne dai gwamantin Najeriya ta
samu hukuncin kotu da ya ayyana IPOB a
matsayin kungiyar ta'adda.

Hakazalika a ranar Laraba rundunar sojin saman
kasar ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu
maso gabashin Najeriya mai suna 'Operation
Python Dance II.'

A ranar Litinin tawagar gwamnonin arewacin
Najeriya, suka yi wani rangadin shiyyoyin kudu
maso gabas da kudu maso kudancin kasar, a
wani kokari na shawa kan rikicin.

A baya-bayan nan dai rikicin kungiyar IPOB mai
fafutukar kafa kasar Biafra a yankin ya yi
kamari.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: