Friday 22 September 2017

An hana malamin Saudiyya wa'azi saboda cin fuskar mata

Tura Wannan Zuwa

An haramtawa wani shaihin malami yin wa'azi a
Saudiyya sakamakon bayyana rashin dacewar
barin mata su tuka mota, a inda ya bayyana
hakan da shashanci.

A wani bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada
zumunta, Sheikh Sa'ad al Hajari ya ce kaifin
tunanin mata rabin na maza ne, kuma da zarar
sun kammala cefane idan suka je kasuwa to
aikin kwalkwalwar tasu na zama rubu'in na
namiji.

Daman dai ba a amince wa mata su yi tuki ba a
kasar duk da cewa babu wata doka kan hakan.
Tsokacin da Sheikh Sa'ad al- Hajari ya yi kan
batun haramtawa mata a Saudiyya tuka mota, ya
yi ta yawo a shafukan sada zumunta da
muhawara.

Al Hajari ya fara ne da cewa an halicci mata da
kankanuwar kwakwalwa, don haka maza suka fi
su kaifin fahimta.

Bai tsaya a nan ba sai da ya kara da cewa:
"Mata ba su da cikakkiyar kwakwalwa, rabi aka
ba su, da zarar kuma sun kammala sayayya a
manyan shaguna, rabin kwakwalwar na koma wa
kwata."

Don haka ya dasa ayar tambaya, "Shin za a bar
mutumin da ba shi da cikakkiyar kwakwalwa ya
tuka mota?"

Martanin da mabiya shafinsa suka mayar ba mai
dadi ba ne, hasali ma wasu na ganin bai kamata
a matsayin da ya ke da shi na babban malamin
addinin musulunci, ya yi kalami irin haka ba.

Wasu ma na ganin ya kamata ma hukumomin
Saudiyya su dakatar da shi daga yi wa al'umma
wa'azi ko yin Limancin Sallah.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: