Monday, 26 May 2025

Halayen Mace A Soyayya Da Aure

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan mace tana halayen yara da ƙuruciya a wajen namijin da take so, hakan na faruwa ne idan ta samu tsayayyen namiji, tana jin aminci da kwanciyar hankali a soyayyar.


Halayen Mace A Soyayya Da Aure
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Idan mace tana jajircewa kamar namiji tana ɗaukar ɗawainiyar da namiji ya kamata ya ɗauka , to saboda tana tare da namiji mai rauni ne wanda bai jajirce ba akan al'amuran ta, hakan ya tilasta mata zama jagora.


Idan mace ta fara ƙoƙarin barin soyayya to ta fara hango cewa wanda take tare da shi ba zai cika mata wasu manufofinta ba ne.


Idan mace kullum tana wahalar aiki fiye da kima, to tana tare da namiji mai sakaci. Tana jin babu kariya a ɓangaren kuɗi, tana ƙoƙarin cike giɓin da ya gaza samu.


Muhimmin abin lura shi ne, halayen mace sau da yawa amsa ne ga irin ƙarfi ko rauni da take samu daga namiji.


Halaye mace sukan canja ne kuma su ta'allaƙa ga irin namijin da take tare da shi.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user