Monday, 7 July 2025

Gayawa Mutane Burin Ka

Tura Wannan Zuwa Ga

 1. “Ina so na fara kasuwanci, ai harkar shaddodi ana samun alkhairi sosai.". Zan fara siyar da takalma, akwai wani abokina da zai riƙa saro mun a kasuwar Wambai. ”


2. “Gaskiya ya kamata na koma makaranta, zan saka littafin Bulugul Maraam.”


3. “Watanni 8 kenan da na gama bautar ƙasa amma ban samu aiki ba, ya kamata na koyi wata sana'a ko ƙwarewa. Ina so na koyi yadda ake "Website Design."”


Gayawa Mutane Burin Ka
Hoto: istock photo

4. "Ina so, zan fara". "Ya kamata." "Nan da wani lokaci.". "Watarana," "Nan kusa". 


Waɗannan kalmomin da ire-irensu sun yi sanadiyyar salwantar da burikan mutane bila adadin.


Hakan ya faru ne saboda mutane suna musanya zance da aiki.


A rayuwa, abin da ke bambance tsakanin masu yin buri kawai da masu isa ga wannan burin shi ne aiki.


Abu ne mai sauƙi ka ɓata awanni kana tattaunawa da mutane akan manufarka, ko kan tsare-tsare, ko zancen zuci.


Amma fa ka sani, idan ba ka ɗauki wannan takun na farko ba, babu abin da zai canza a cikin rayuwarka.


Surutu da gaya wa mutane burinka kawai zai ƙara maka kasala ne da ruɗuwa da kanka, sai ka ji kamar kana samun ci-gaba, kamar har ka soma abin da kake ƙoƙarin aikatawa.


Ka bar bari ƙwaƙwalwarka tana yaudararka tana suranta maka kamar ga shi nan har ka cimma manufarka.


Ci-gaba na haƙiƙa yana zuwa ne daga farawa, da yin aiki ba daga surutu ba, kuma ba daga kyawun shawara ko kyakkyawan shiri ba kaɗai.


Tazarar da ke tsakanin inda kake da inda ka nufa, ba abin da zai cike ta face aiki, ba surutu ba.


Minti ɗaya na aiki ya fi awa guda na magana. Za ka iya yin shekaru kana faɗin burikan ka amma hakan ba zai canza komai ba daga haƙiƙanin halayyar ka. 


Surutu hali ne na ragwaye, aiki shi ne halin jajirtattu.


Ba laifi ba ne don ka yi shawara, ko ka tsaya tunani da yin tsare-tsare, amma fa ka sani; magana idan ta yi yawa ta kan koma shirme da soki-burutsu.


Tushe/Asali: Hausa Motivation

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user