Kuskuren da mace ta yi ma a soyayya ka tausaya mata kar ka yi abun da zai sa fitar hawaye a idonta. Ka duba rauninta kasancewarta mace.
Yadda Ake Kula Da Mace A Soyayya
Hoto: Business insider
Marubuci:- Muh'd Captain
Dukkan soyayyar da babu tausayin mace a zuciya tabbas soyayyar gangan jiki ake mata ba na ruhi ba.
Mace tana son mutum ne da zuciya ɗaya koda a ce shi mutum mai cutarwa ne a gurin ta.
Zuciyar mace da rayuwarta akwai rauni a ciki dole duk namiji ya koyawa kansa tausayawa mace.
Ita mace al'umma ce ba ta kulawa dole ce a gurin mu, tabbas masu girma ne mata, mu tausayawa raunin su.
Kuɗi, gida, kayan alatu ba su ne kawai abin da mata ke buƙata a soyayya ba, kulawa, tausayawa da kuma samun lokacin masoyi su fi buƙata.
Ita soyayya aba ce mai girma wadda take son kulawa da tausayawa.

