Thursday 17 October 2019

Karanta Yadda ake Yin Addu'ar Sallar Istihara Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai Aikata Wani Abu

Tura Wannan Zuwa
Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce; Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani.


Addu'ar Sallar Istihara (Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai Aikata Wani Abu)



Yakan ce, "Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce;

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ  حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.

Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta'lamu anna hazal-amr (say your need) khayrun lee fee deenee wama'ashee wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta'lamu anna hazal-amr sharrun lee fee deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee wasrifnee 'anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.

Addu'ar Sallar Istihara (Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai Aikata Wani Abu).

Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al'amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al'amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa. Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka  kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi".

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA FALALAR ZIKIRI

Karanta Yadda ake Yin Salatin Annabi Muhammad (SAW) a Mahangar Sunnah

Karanta Zikiri Bayan An yi Sallama Daga Sallah

Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;

(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)

(Washawirhum Fiyl Amri Fa'iza Azamta Fatawakkal Alallahi).

"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user