Friday 16 November 2018

KARANTA FALALAR ZIKIRI

Tura Wannan Zuwa Ga
Allah Madaukakin Sarki ya ce:

فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُواْ لِي وَلاَ تَكْفُرُونِFazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni.

Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152].

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْراً كَثِيراً

Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran.

Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41).

وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيراً وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْراً عَظِيماً

Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman.

Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35]

وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعاً وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالآصَالِ وَلاَ تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ

Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna.

Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205].

Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).)

Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku?

 Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki". (Tirmizi (5/459), da Ibn Majah (2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139).)

Kuma ya ce: "Allah madaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin ransa zan ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin jama'a zan ambace shi a cikin jama'ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni taki daya zan kuance shi tsawon gaba guda, in ya zo min ya na tafiya zan zo masa ina gaggawa".( Bukhari (8/171), da Muslim (4/2061). Lafazin ruwayar na Bukharine.)

Daga Abdullahi Ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce; Ya Ma'aikin Allah! Shari'o'in Musulunci sun yi yawa a gare ni, saboda haka ka nuna wani abu da zan yi riko da shi. Ya ce: "Ku harshenka ya gushe face yana danye daga ambaton Allah". (Tirmizi (5/458). Da Ibn Majah (2/1246).

Duba Sahihul Tirmizi (/139), da Sahih Ibn Majah (2/317).)

Kuma mai tsira da amincin Allah yace;

"Wanda ya karanta harafi daya daga littafin Allah yana da (ladan) kyakkyawan aiki daya saboda shi, kuma dukkan kyakkyawan aiki daya yana da (ladan) misalinsa goma. Ba ina cew Alif Lam Mim harafi ba ne. A'a, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne".( Tirmizi (5/175) Duba Sahihul Tirmizi (3/9), da Sahihul Jami'us Sgir (5/340).)

Kuma daga Ukbata ibn Amir, Allah ya yarda da shi, ya ce; "Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi, ya fito alhali muna cikin rumfa, sai yace; "Wane ne daga cikinku zai so ya fi kullum da safe zuwa koramar Budhan ko Akik, ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna, ba tare da yin wani laifi ba ko yanke zumunta?"

Muka ce: muna son haka. Ya ce; "Dayanku ya je masallaci ya nemi sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah Mabuwayi Mai Daukaka, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku, ayoyi hudu sun fi masa taguwa hudu, da kwantankwacin adadinsu na rakuma". (Muslim (1/553))

Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; "Wanda ya zauna a wani waje bai ambaci Allah a wajen ba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. Wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajen ba, shi ma zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. (Abu Dawud (4/264), da waninsa. Duba Sahihul Jami (5/342).)

Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce: "Babu wasu mutanen da suka zauna a wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya, in Allah ya so ya yi musu azaba, in ya so ya gafarta musu".( Tirmizi, duba Sahihul Tirmizi (3/140).)

Kuma Mai tsira da amincin Allah yace; "Babu wasu mutane da zu su tashi daga wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan mushen jaki ne, kuma zai zamanto musu abin da-na- sani".( Abu Dawud (4/264). Da Ahmad (2/389). Duba Sahihul Jami' (5/176).)

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user