Monday 28 October 2019

Karanta Tarihin Kafuwar Masana'antar Kannywood

Tura Wannan Zuwa Ga
Kannywood Itace Masana'antar Shirya Fina Finai da Harshen Hausa, Yaren da Jama'ar kabilar Hausawa Suke yin magana dashi a Nahiyar Africa.


Tarihin Kafuwar Masana'antar Kannywood

Kasancewar Hausawa Sunfi yawa a Kasar Nigeria, Hakanne yasa Kannywood Ta Samu tushenta a Babban Garin Kano Na Kasar ta Nigeria.

Zaman Cibiyar Masana'antar a Kano, shine yasa ake kiranta da (KANNYWOOD) a inda KANNY Take Nufin Kano ita Kuma Wood daga (Bollywood) Sai Aka bi salo iri Daya Da Yadda Sinimar India ta Bollywood ta samo Sunanta na Bolly daga Bombay da kuma Wood daga (Hollywood)

An Fara amfani da Kalmar kannywood ne Shekarar 1999 Kuma Wanda ya Fara amfani da ita Shine danjarida "Sunusi shehu" Ma'aikachi a Mujallar "Tauraruwa"

Tarihin Kannywood ya Fara Ne Sama da Shekaru Hamsin (50) da suka Wuce, a Lokacinda Gidan Talabijin na RTV da Kuma Gidan Radio Kaduna Suka Fara Gabatarda Wasan Kwaikwayo a cikin Shirye shiryen su. Daga Nan Yan Wasa irinsu Kasimu yero da Dalhatu bawa Suka Shiga fagen Shirya Wasan Kwaikwayo A mizani Mai Girma.

A shekarun 1970s Zuwa 1980s ne Usman Baba Pategi da Mamman Ladan Suka Fara Gabatarda Wasan Kwaikwayo Mai Salon bandariya (Comedy) Ga Masu Kallan wasannin Kwaikwayo na Hausa.

Duk a Wancan Lokacin, wasannin Kwaikwayo sun kasance a Gidajen Radio Ne Kawai da Kuma Gidajen Talabijin, Amma Sun Samu Karbuwa Sosai A wajen Makallata da masu sauraro. Wannan daliline tare da wasu dalilai Yasa aka Fara Film din hausa (Home videos) Da ake iya Siyan Kaset a Kalla a cikin gidaje.

Daga Cikin Manufofin Fara film din Hausa akwai Kawar da kan Al'umma daga Kallon Fina finan kasashen waje Musamman na America, China   da Kuma uwa uba India Wanda Saboda Tasirin Fina finansu Ga Hausawa, Har yau kannywood Su take Kwaikwayo.

An Fara (Home videos na Hausa) A Lokacin da Al'umma suke Tsananin Kallon Wasannin Talabijin na NTA da CTV a 90s irinsu :

Hadarin gabas
Zaman Duniya
Hana wani Hana Kai

Da sauransu.

Film din Hausa na farko da aka Fara saki Shine "TURMIN DANYA" a 1990, Daga Nan Sai Fina finai irinsu "Gimbiya Fatima, In da so da kauna, Gagare, Sumbuƙa, Munkar, Badaƙala, da sauransu.

MAKALOLI MASU ALAKA:

SHIN SHIGOWAR JARUMA MARYAM YAHAYA KANNYWOOD CE SILAR KWARAROWAR KANANAN JARUMAI A KANNYWOOD?

Tsohuwar Jarumar Kannywood Mansura Isah ta Yiwa Jaruma Sadiya Haruna Nasiha Mai Zafi

KARANTA KAMA DARACTAN FILM A KANO ZALUNCI KO ADALCI?

Daga Nan ne Aka Fara Samun manyan Jarumai irinsu; Ibrahim Mandawari da Marigayiya Hauwa Ali Dodo (Biba) Sune Suka Fara Samarda Matakin Tauraro (Superstar) a Kannywood.

Mu Hadu a wani makon domin Jin ci gaban Shirin.

Mune Naku Habibu Maaruf Abdu Tare da 'Yar uwa abokiyar aiki Meenat Sulaiman .

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user