Monday 14 October 2019

Tsohuwar Jarumar Kannywood Mansura Isah ta Yiwa Jaruma Sadiya Haruna Nasiha Mai Zafi

Tura Wannan Zuwa Ga
Fitacciyar tsohuwar jaruma, kuma matar jarumi/mawaƙi Sani Musa Danja, wato Mansurah Isah, ta tsoma baki kan cece-kucen da ake yi kan rigimar Sadiya Haruna da Isa A. Isa.

Mansura Isah da Sadiya Haruna

A rubutun da ta yi a Instagram a yau ɗin nan, Mansurah ta bayyana takaici kamar haka:

"Subhana Subhana llah. Sadeeya bana tausayin ki ko kadan wallah, ban damu dake ba ko kadan, domin kin yankewa kanki rayuwar da kike so da halin da kike son ki tsinci kanki. Damuwata, kukana yaranki da wayenda zaki haifa a nan gaba da basu ma duniya a lokacin da kika wulakanta kanki. Duk abinda mukayi yana nan a social media and it will stay sadiya.

Even after u delete all your post, the damage has already been done. Banzan ce bazaki samu mijin aure ba, akwai masu imani. But just imagine your children in sunyi fada da mutane, zagin da zaayi musu na irin abinda mamansu ta aikata lokacin da take budurwa. Komu da bamuyi haka ba, film kawai mukayi muka fita lafia, ana zagin yaran mu ana kiran iyayen su suna, suna kuka kuma basu jin dadi. Balle ke.

Nasan Allah ne mai shiryawa kuma zaki iya shiryuwa, but imagine the consequences on your family n children. Wallah wani lokacin dan yarana ina hakuri da abinda nake so kuma nasan bashi da alheri, dan yarana nakan kai zuciyata nesa dan siya musu musu mutunci a idon duniya. Ana cewa equality for all. But duk abinda mukayi a matsayin mu na mata wallah yana nunawa ajikin mu.

Mansura Isah da Jarumi Sani Danja

Mufa ba yan america bane, we are blacks, we have culture, we have religion and we have manners. Inma ana zugaki ne, kice musu su tayaki yi bazaki yiba, kiga ko zasuyi. In kinyi abu mara kyau kuma Allah ya rufa miki asiri, to Allah yana sonki da rahama ne, sai ki cigaba da tuba, domin Allah baya son tozarta ki, amma Allah ya rufa miki asiri, kinyi abu a boye kuma Allah bai tona miki asiri ba, amma baki gode mishi ba, dole sai kin tonawa kanki asiri. Tam Allah ya baki saa. Amma ki guji duniya. After knowing all this things u did, who will want to associate himself with you? Knowing komin dadewa in mukayi fada zaki tonawa kawarki asiri? Re think about your life. Stop all this nonsense on social media.

Zargin Luwadi a Kannywood: 'Yan sanda Sun Kama Sadiya Haruna

Go to YouTube and see all your videos. Hotunan nonon ki a waje, duk jikin ki a waje, duk wani abu da kika taba posting a page dinki yana YouTube , weather You delete them or not. Be wise and live in peace. Forget about been famous, nothing last for ever, zaa dawo a manta dake adaina yayinki komin dadewa, but what about your future generation?"

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user