Showing posts with label Hausa Films. Show all posts
Showing posts with label Hausa Films. Show all posts

Friday, 15 November 2024

Zafafan Darussa 5 Daga Shiri Mai Dogon Zango Na Garwashi

Zafafan Darussa 5 Daga Shiri Mai Dogon Zango Na Garwashi

1. Rayuwa za ta iya sauya maka cikin gaggawa ba tare da ka shirya ba, kamar yadda mutuwar miji ya zama mabuɗin da munanan ƙaddarori suke faruwa da Asma'u.


Garwashi shiri mai dogon zango
Hoto: Yaseen Auwal/Instagram

MarubuciYahaya S. Kaya


2. Duk yadda miji yake son matar shi, matuƙar 'yan'uwansa da iyayensa ba sa son ta, za ta zama abar tausayi a lokacin da ba ya kusa, koda a ce ma ba mutuwa ya yi ba. 


Ya kamata a ce duk yadda za ka yi ka ƙirƙiri zaman lafiya a tsakanin danginka da matarka, don gudun rusa tarbiyyar 'ya'yanka a lokacin da ba ka raye.


3. Al'ummar mu suna taimakawa da kaso mai tsoka wajen lalacewar mutanen da ke kusa da su, maƙwabta ko kuma wanda yake da halin taimako amma ya ƙi taimakawa Dan Allah sai ya nemi ya keta haddi.


4. Samun iyaye nagari rahama ce. Gaskiya babu ta yadda za a yi yaron da ya taso a gidan su Asma'u ya samu tarbiyya, kullum da ashariya ake karin kumallo a gidan, da faɗa da hayaniya, ƙarami ba ya ma babba biyayya.


5. Duk mace mai kishi irin na Samira, za ta iya aikata komai, kuma a ƙarshe ta ƙare a nadama.

Monday, 7 October 2024

Zan Bar Muku Najeriyarku Na Koma Kasata - Fati Niger

Zan Bar Muku Najeriyarku Na Koma Kasata - Fati Niger

Fati Niger ɗaya ce daga cikin fitattun mawaƙan Kannywood, a ɗaya daga cikin sababbin waƙoƙin ta da ta saki na baya, bayan nan, tana mai nuni da yadda take fama da ƙalubale a zaman ta a Najeriya.


Zan Bar Najeriya Na Koma Ƙasata - Fati Niger

A saboda haka ne take tunatar da masoyan ta da maƙiyanta a fakaice cewa tana da ƙasa, za kuma ta je can amma za ta dawo.


Waƙar mai taken "Fati Fatima Fatiti.".


Ga kaɗan daga cikin wasu baitocin da ke bayyana irin halin da take ciki;


Ba ku zamtowa daidai da ni.


Maƙiyana dole ku bar mini.


Lokacin Allah ke yi da ni.


Ciwuka ba sa rasa magani.


Na riga ni nai nisa tuni, don ko sunana ya kai gurin da ni ma ban je ba.


Sanannen mawaƙin nan na Kannywood Ado Gwanja shi ne ya yi mata amshin waƙar, amshin da ke nuni da yadda yake lallashin ta kan yanayin da ta kasance a ciki.

Friday, 2 August 2024

Duk Wanda Bai Iya Turanci Ba A Matsiyaci Zai Dawwama - Maryam Labarina

Duk Wanda Bai Iya Turanci Ba A Matsiyaci Zai Dawwama - Maryam Labarina

A hirar kai-tsaye da ake yi a kan manhajar TikTok, ɗaya daga cikin jaruman masana'antar Kannywood Fatima Hussain wadda aka fi sani da Maryam Labarina ta mayar wa da ɗaya daga cikin mabiyan ta martani kan cewa "Dole ne ka iya Turanci, saboda Turanci shi ne harshe na duk duniya, saboda ana sa ran iyayen ka ba su haifi matsiyaci ba, sun haifi mai kuɗin da zai dinga kasuwanci daga ƙasar Dubai zuwa Amurka.".


Jaruma Fatima Hussain
Hoto: Fateeema Hussain


Fatima Hussain ta yi fice ne a wani shiri mai dogon zango na Labarina wanda kamfanin Saira Movies suke shiryawa, wanda ake tsaka da haska shi yanzu haka a kan manhajar YouTube da tashar talabijin ta Arewa24.


Kalli bidiyon kaitsaye anan....


Jarumar kuma ta ƙara da cewa laifin mutum ne idan bai da ilimi.

Wednesday, 17 July 2024

Hotuna Da Bidiyo: Yanzu-Yanzu 'Yan Garkuwa Sun Sako Mahaifiyar Rarara

Hotuna Da Bidiyo: Yanzu-Yanzu 'Yan Garkuwa Sun Sako Mahaifiyar Rarara

A kwanakin baya ne dai aka yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawaƙin nan Dauda Kahutu Rarara.


Rarara tare da mahaifiyarsa


A safiyar yau ne wakilin mu ya samu tabbaci na sako mahaifiyar mawaƙin.


Bayan dawowarta
Hoto: Dauda Kahutu Rarara


Jaruma Aisha Humaira ita ma kanta ta tabbatar da sakin mahaifiyar mawaƙin a shafin ta na Instagram, wanda kuma kowa ya san irin alaƙar da ke tsakanin su da Rarara.


Kalli bidiyon kai-tsaye


Dauda Kahutu Rarara da mahaifiyarsa
Hoto: Dauda Kahutu Rarara

Mawaƙi Rarara da mahaifiyarsa
Hoto: Dauda Kahutu Rarara


Sannan shi kansa ya bayyana tabbacin dawowar ta a shafin nasa na Instagram.


Kalaman sa


Ya yi godiya ga Ubangiji da masoyansa da 'yan uwansa da abokan sana'ar sa.

Sunday, 9 June 2024

Cikakken Sabon Bidiyon Da Sarkin Waka Ya Sake Caccakar Masu Jiran Ta Fashe

Cikakken Sabon Bidiyon Da Sarkin Waka Ya Sake Caccakar Masu Jiran Ta Fashe

A makon nan ne fitaccen mawaƙin Hausa na masana'antar Kannywood wato Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waƙa, a wata tattaunawa da aka yi da shi ya soki harkar Minig da Cryptocurrency, inda hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce mai yawa a shafukan sada zumunta.


Martanin Sarkin Waƙa
Hoto: Sarkin Waƙa


Biyo bayan hakan ne, sai ya fito ya mayar da martani tare da sake jaddadawa duniya abin da yake nufi.


Kalli bidiyon kai-tsaye anan..


Har yanzu dai masu harkar Minig da Cryptocurrency ba su daina nuna damuwarsu a kan kalaman nasa ba.

Wednesday, 10 April 2024

Dalilin Mutuwar Jaruma Saratu Daso

Dalilin Mutuwar Jaruma Saratu Daso

Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso, ɗaya ce daga cikin manyan jaruman Kannywood, waɗanda aka daɗe ana damawa da su a masana'antar.


Marigayiya Jaruma Saratu Giɗaɗo
Hoto: Real Ali Nuhu


Ta rasu a jiya talata, bisa larurar mura da ta yi fama da ita, daga lokaci bayan lokaci.


Marigayiya Jaruma Daso
Hoto: Zaharadeen Sani Owner


Mutane da dama, sun ji mutuwar ta, kasancewar ta mace mai yawan barkwanci da jama'a, tare da taimakon marayu.


Mu na yi mata fatan samun kyakkyawar makoma.

Tuesday, 2 April 2024

Kalli Zafafan Hotuna Daga Dandalin Daukar Shirin Gidan Sarauta Zango Na Biyu

Kalli Zafafan Hotuna Daga Dandalin Daukar Shirin Gidan Sarauta Zango Na Biyu

Gidan Sarauta, ɗaya ne daga cikin sababbin shirye-shirye masu dogon zango na masana'antar Kannywood, wanda aka kammala ɗaukar zango na biyun shi a halin yanzu.


Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy


Gidan Sarauta, ya samu karɓuwa yadda ya kamata, a kusan ko'ina.


Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

A yanzu haka, an kammala haska zangon farko na  shirin, har sai zuwa ga ranar 13-4-2024 za a dawo daga hutun da aka tafi, na kammala zangon farkon, domin ci gaba da haska zango na biyun, wanda ya kasance ci gaban na farkon ne.


Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Waɗannan wasu ne daga cikin hotunan dandalin ɗaukar shirin Gidan Sarautar.


Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy


Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:



Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Dandalin Ɗaukar Shirin Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Yayin Ɗaukar Shirin Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Gidan Sarauta
Hoto: Kibadash Photographyyyy

Fatan hotunan, sun burge ku.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun hotuna da labaran abubuwan da ke faruwa a dandalin ɗaukar shirye-shiryen wasan kwaikwayo, masu gajeren zango, har ma da na shirye-shirye masu dogon zango.

Monday, 25 March 2024

Kalli Zafafan Kyawawan Hotunan Jaruma Nana Firdausi Yahaya

Kalli Zafafan Kyawawan Hotunan Jaruma Nana Firdausi Yahaya

Firdausi Yahaya ko Nana Fiddausi Yahaya wadda aka fi sani da Zainab Labarina, ta kasance ɗaya daga cikin sababbin jarumai mata masu tasowa, waɗanda tauraruwar su take kan ganiyar haskawa a masana'antar Kannywood.


Jaruma Nana Firdausi Yahaya
Hoto: Firdausee Yahaya


Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.


Nana Firdausi Yahaya
Hoto: Firdausee Yahaya


Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan nata.


Jaruma Nana Firdausi Yahaya
Hoto: Firdausee Yahaya


Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:


Jaruma Nana Firdausi Yahaya
Hoto: Firdausee Yahaya


Jaruma Nana Firdausi Yahaya Labarina
Hoto: Firdausee Yahaya

Fatan hotunan, sun burge masoyan ta.


Ku ci gaba da kasancewa da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun sababbin hotunan jaruman ku.

Friday, 22 March 2024

Kalli Sababbin Kyawawan Hotunan Auta Waziri

Kalli Sababbin Kyawawan Hotunan Auta Waziri

Abdullahi Abubakar, wanda ya yi fice da sunan Auta Waziri, daɗadɗen mawaƙi ne a masana'antar Kannywood, wanda a halin yanzu tauraron sa yake ci gaba da haskawa a ko'ina.


Mawaƙi Auta Waziri
Hoto: Auta Waziri


Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.



Auta Waziri
Hoto: Auta Waziri


Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan sa.


Mawaƙi Auta Waziri
Hoto: Auta Waziri


Fatan hotunan nasa, sun burge masoyan sa.


Auta Waziri
Hoto: Auta Waziri


Ku ci gaba da kasancewa da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun sababbin hotunan mawaƙan ku.