Friday 2 August 2024

Duk Wanda Bai Iya Turanci Ba A Matsiyaci Zai Dawwama - Maryam Labarina

Tura Wannan Zuwa Ga

A hirar kai-tsaye da ake yi a kan manhajar TikTok, ɗaya daga cikin jaruman masana'antar Kannywood Fatima Hussain wadda aka fi sani da Maryam Labarina ta mayar wa da ɗaya daga cikin mabiyan ta martani kan cewa "Dole ne ka iya Turanci, saboda Turanci shi ne harshe na duk duniya, saboda ana sa ran iyayen ka ba su haifi matsiyaci ba, sun haifi mai kuɗin da zai dinga kasuwanci daga ƙasar Dubai zuwa Amurka.".


Jaruma Fatima Hussain
Hoto: Fateeema Hussain


Fatima Hussain ta yi fice ne a wani shiri mai dogon zango na Labarina wanda kamfanin Saira Movies suke shiryawa, wanda ake tsaka da haska shi yanzu haka a kan manhajar YouTube da tashar talabijin ta Arewa24.


Kalli bidiyon kaitsaye anan....


Jarumar kuma ta ƙara da cewa laifin mutum ne idan bai da ilimi.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user