Sunday 2 June 2024

Karanta Ainihin Tarihin Bitcoin Da Amfanin Shi Da Matsalolin Shi Da Hukuncin Mu'amala Da Shi A Musulunci

Tura Wannan Zuwa Ga

Bismillahir Rahmanir Rahim


Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa bakiɗaya.


Bayan haka, a yau Alhamis 15 Jumada Akhir, 1442 H.-28 Janairu, 2021 M., zan amsa tambayoyin da na samu ta fuskoki da yawa game da mu’amalar zamani ta Bitcoin da sauran mu’amala irinta. Daga cikin tambayoyin akwai waɗanda suka turo da cewa: “Malam ina tambaya ne game da halaccin cinikin online da ake na su bitcoins, cdmx, cdx da sauransu. Malam menene halaccin kuɗin a addini. Na gode. Allah ya saka da alheri”.  Zan dan faɗaɗa kaɗan a wajen bada amsar har na shigo da yadda tsarin yake domin waɗanda ba su waye da shi ba daga cikin ‘yan uwa da suke cikin lugunan birane da karkara su fahimci yadda Bitcoin yake. Ina fatan yin haka ya buɗe damar tattaunawa da gano wasu hukunce-hukuncen da suke cikin wannan sabuwar mu’amala mai cike da rintsi da sarƙaƙiya, wadda malamai har yanzu suna kaiwa, suna komowa wajen yanke hukuncin da ya dace da ita. A kan wannan aka rubuta wannan amsa.


TARIHIN BITCOIN DA AMFANIN SHI DA MATSALOLIN SHI DA HUKUNCIN MU’AMALA DA SHI A MUSULUNCI
Hoto: Cryptonomist


MarubuciAhmad Murtala Mansur


Mai son ya gane wannan bayanin da kyau, to aikin karatawa gaba ɗaya ya same shi. Insha’allah kuma za a fahimta. Da fatan Allah ya ba mu sa’a da dacewa.


1- A kowane lokaci yana da kyau a riƙa sanin tarihin abubuwa da tsarin da suke tafiya a kansa, musamman irin waɗannan sababbin mas’aloli na zamani waɗanda ake kiransu da sunan "النوازل", domin a fayyce yadda za a bada amsa a kansu.

 
i- Tun a shekarun 1990, mutane irinsu Nick Szabo suka fara zuwa da wani tunani na ƙulla cinikayya a kan intanet da sunan ‘Bit Gold’. Sai dai abin bai samu yaɗuwa ba sosai. Haka nan a 1998 Bernard von NotHaus ɗan Jihar Hawai a Amurka ya yi irin wancan tunani ya ƙiriƙiro ‘Liberty Dollars’. Amma ya firgita gwamnati don haka sai da aka ɗaureshi a kan wannan aika-aika tasa. A wannan shekarar dai, gwanaye a kan kwanfiyuta ba su daddara ba, sai da wani ɗan China mai suna Wei Dai ya ƙirƙiro ‘B-Money’. Bayan haka, a 2007, jami’an tsaro a Amurka suka rufe wata manhaja a kan intanet mai suna ‘E-Gold’. 


Wannan duk bayanai ne a taƙaice na irin yunƙurin da wasu suka yi don samar da tsarin hada-hadar kuɗaɗe a kan intanet ba tare da sa hannun gwamnati ba. Amma ba su sami cimma burinsu ba. Irin waɗannan kuɗaɗen na kan intanet kurum ake kira da sunan “Cryptocurrency”.


ii- Kalmar ‘Bitcoin’ kalmomi biyu ne na turanci a haɗe. ‘Bit’ tana nufin kaɗan ko gutsure. ‘Coin’ kuma tan nufin tsabar kuɗi masu kamanni da kwabo ko ƙwandala. An fara ƙirƙiro da tsarin Bitcoin da kuma yi masa rijista a kan yanar gizo-gizo a 2008. Babu takamaimai a kan wanda ya fara ƙirƙirar wannan tsari. An zaton mutum ɗaya ne ko kuma gungun wasu mutane da sunan Satoshi Nakamoto. Takardar da mai ko masu wannan suna ya/suka rubuta da taken “Bitcoin: A Peer-to-Peer Electronic Cash System”, kusan ita ce ta fito da wannan suna na Bitcoin a fili. Amma dai an san cewa yana daga cikin irin tsarin mu’amalar kuɗaɗe ta zamani a ƙarƙashin taken ‘Cryptocurrency’. An fara ɗora manhajar Bitcoin wadda kowa zai iya amfani da ita a watan January na 2009. A cikin wannan wata ne kuma aka fara hadahadar kuɗi ta wannan manhaja da kuɗi kaɗan. Amma 2010 hadahadar kuɗin ta fi bayyana sosai.

 
Zuwa January na 2021 akwai kusan kamfanoni 2,000 na crytocurrencies. Wanda aka fi sani a cikinsu shi ne ‘Bitcoin’. Ragowar kuma ana kiransu da ‘Altcoins’ ko ‘shitcoins’, waɗanda suka haɗa da ‘Ethereum’, ‘Litcoin’, Ripple, Stellar’, Chainlink, ‘Bitcoin Cash’, da sauransu.


Yawancinsu sun samo asali ne daga fasahar Bitcoin ɗin. A ɗan wannan lokacin, bincike yana nuna cewa Bitcoin su ne kan gaba da fiye da kaso biyu bisa uku na dukan mu’amalar juya ‘kuɗadɗn-gaibu’ (Digital Money) na cryptocurrency! Don haka duk hukuncin da aka faɗa a kan Bitcoin, ragowar ma ya hau kansu, sai dai in da ƙarin wani abin daban da ya daɗa cin karo da ƙa’idojin Shari’a!

 
iii-Abin mamaki dai har yanzu shi ne, tun a 2011 mai wancan suna Satoshi Nakamato, wanda ya yi kama da sunayen mutanen Japan, aka daina jin ɗuriyarsa. Kafin ya ɓuya ya turo da bayanin cewa shi fa ya janye jiki yanzu ya bar wannan harka. Ya yi bayani ta hanyar email cewa ya miƙa wannan harka a hannun amintattu mutane kamar su Gavin Andresen da Mike Hearn. Waɗannan mutane da ma wasu da aka yi zargin ko su suka ƙirƙiro manhajar duk sun musanta cewa suna da hannu a ƙirƙirota. Don haka har yanzu ba a gama gano waye wanda ya ƙirƙiro wannan tsari ba.

 
vi- Manufar ƙirƙiro da Bitcoin ita ce a bawa mutane dama su yi hulɗa da kuɗaɗe kai tsaye ba tare da wani banki ko kamfani ko wani mutum ya shiga tsakaninsu ba. Don haka tsarin Bitcoin ba ya kulawa da wata gwamnati ko wasu tsare-tsare. Mu'amala ce ta kuɗi tsagwaranta tsakanin mutane ba wani shinge kamar dai yadda suke kiranta da “Peer-to-peer”!

 
2- Abin la’akari shi ne an ɗora tsarin Bitcoin a kan abubuwa da yawa na ilimin kwamfiyuta da mu’amalolin yau-da-gobe. Amma akwai wasu abubuwa masu muhimmanci kamar haka:


i-An gina manhajar a kan amfani da ilimin lissafi da aka fi sani da “Algorithm”, tsarn lissafi ne da ake warware matsalolin lissafi masu wahala da shi. Ilimi ne mai muhimmancin da ɗaya daga cikin masana lissafi Musulmi da aka fi sani da Muhammad bn Musa Al-Khawarizmi (780-850 M.) ya ƙirƙiro shi. Gabadaya tsarin kwanfiyuta ma a kan wannan ilimi aka ƙirƙiro shi. Shi ma Bitcoin aka zuba shi a kan wannan ilimi.


ii- An ɗora manhajar Bitcoin a irin tsarin da manyan gidajen caca na duniya suke shirya injinan da ake gudanar da caca da su, wanda aka fi sani da “Lottery-Based System”.

 
iii- Waɗanda suka ƙirƙiro Bitcoin sun ƙaddara cewa zuwa shekara ta 2140 duk manhajar za ta tsaya cak ko kuma idan adadin ƙwandala da aka samo take miliyan ishiri da ɗaya. A halin yanzu ana da sama da miliyan goma sha bakwai.


3- Wanda yake son shiga hadahadar Bitcoin sai ya bi matakai daban-daban bisa yadda kamfanonin da suke taimakawa suka tsara. Domin dai a gane yadda abin yake ga hanya mai sauƙi kamar haka:


i- Dole sai mutum ya buɗe lalita “Digital Wallet” wadda take wuri ne mai kama da account na banki. Za a buɗe shi a ɗaya daga cikin manhajoji na musamman da suke kama da bankunan a kan internet.

Manhajar da take aiki sosai tare da Bitcoin ita ce “Blockchain”, wadda tana da sauƙin shiga da sarrafawa da buɗe wallet nan da nan.


AMFANIN BITCOIN
Hoto: Coin68

 
ii- A wannan wurin ne mutum zai shigar da email ɗinsa sannan kuma ya ba wa abin sunan da ya ga dama. Za a iya amfanin da ɓoyayyun sunaye “Anonymity”. Bayan haka kuma ya ƙirƙiri “password” da yake so daga kalma 1 har zuwa 78, amma sai ya cakuɗa tsakanin lambobi da harufa. Idan mutum ya manta su, yana da dama har sau goma ya gwada lambobi daban-daban ko zai dace ya samu daidai ya buɗe. Idan har ya cikasa na goman bai dace ba, manhajar za ta garƙame lalitar tasa har abada, kuɗin mutum sun tafi kenan. Manhajar ba ta riƙe waɗannan lambobi, don haka mutum yana da buƙatar ya shigar da su a kowane lokaci kafin ya sami hanyar shiga manhajar.


iii- Manhajar za ta turowa mutum da wani shafi mai muhimmanci da zai kawo wasu kalmomi masu suna “identifier”.


Waɗannan suna da matuƙar muhimmanci. Idan sun ɓata shi kenan komai ya ɓata. Don haka ne ma Manhjar Blockchain take jan kunnen mutum ya riƙe waɗannan lambobi da ta ba shi da kyau sosai. Ya rubutasu a wuri na sirri. Kada ma ya kuskura ya yi wasarere da su ko ya rubutasu a wani wuri a kan intanet. Don wasu ‘yan fashi na kan intanet za su iya bincikosu, su kwashe abin da mutum ya saya na Bitcoin.


iv- Daga nan mutum zai koma kan email ɗinsa, zai ga sun aiko masa da wata gajeruwar wasiƙa da ta ƙunshi abin da zai danna don ya tabbatar musu da shi ne yake da wannan email ɗin. A wannan gajeruwar wasiƙa dai za a ga wasu lambobi da suke kira da sunan “confirmation code”. Suna buƙatar mutum ya kwafesu ya ajiye a gefe kamar waɗanda suka gabata. Domin wanna shi ne ‘code’ ɗin da mutum zai riƙa rubutawa a lokacin da zai aika kuɗi ko in zai cire kuɗi daga lalitarsa.


v- Sai mutum ya koma kan Manhajar Blockchain, a inda zai sami tabbacin cewa Manhajar yanzu ta sami alaƙa da email ɗinsa. Daga nan sai ya danna “Login Now” don ya shiga shafin lalitarsa “My Wallet”.


Daga can ƙasa in an duba za a ga wasu lambobin “Code”, waɗanda su ma za a kwafesu a gefe a ɓoye kamar waɗancan na baya. Waɗannan lambobi na me wannan wallet ɗin ne shi kaɗai. Su zai riƙa rubutawa ga duk kamfani ko wani mutum da suke hulɗar Bitcoin tare don karɓar kuɗaɗe daga wurarensu. Daga nan shi kenan mutum ya shiga tsarin Bitcoin.

 
4- Ana mallakar ƙwandalar Bitcoin ta fuska biyu kawai:


i- Hanya ta ɗaya mutum ya sayi gwargwadon abin da yake so na kuɗaɗen Bitcoin ta hanyar miƙa kuɗaɗen da aka saba da su kamar Naira ko Riyal ko Dollar da wani ya sayar masa. –Wato “exchange” kenan. Domin ana iya gutsura ƙwandalar Bitcoin zuwa gutsure-gutsure yadda ake so, a kuma sayar da ita. Ita kuma ribar da mai sayarwa ya samu sai ya ajiyeta a cikin lalita. Haka dai har lokacin da za a so shi ma ya sayar!


ii- Hanya ta biyu kuma ita mutum ya shiga “zabari” wanda suke kira da sunan “Mining”. Mutum ɗaya ko gungun wasu mutane ko wasu kamfanonin suna iya shiga wannan aiki da zabarin ta hanyar sayan manyan kwamfiyutoci don su gudanar da aikin. Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa aikin yana ɗaukar lokaci da amfani da ƙarfin wutar lantarki da data masu yawan gaske kafin a ce an sami ƙwandala ɗaya tak. 


5- Wannan Manhaja ta Bitcoin tana da matsaloli masu yawa da suka haɗa da waɗannan:


i- Tun a 2011 wasu gungun masu fataucin miyagun ƙwayoyi da sunan “The Silk Road” suka sanar da cewa wannan manhaja ta Bitcoin za ta zamo hanyar da za su riƙa musayar kuɗaɗen kayan maye wajen saye da sayarwa. Domin za a iya amfani da manhajar ba tare da an gane mutane ko an san dalilin da za su yi musayar kuɗaɗen ba. 


A shekarun 2013 zuwa 2015, ma’aikatar leƙen asiri ta Amurka FBI sun bankaɗo lalitar Bitcoin masu yawa da suke da alaƙa da hadahadar miyagun ƙwayoyi..-(Characteristics of Bitcoin Users: An Analysis of Google Search Data na Matthew Wilson, University of Michigan, 2014).


ii- Tare da cewa Manhajar ba ta ba wa wani dama ya kutsa cikin lalitar wani haka kai tsaye, amma a shekarun 2018 zuwa yanzu, an sami yawan sace-sacen kuɗaɗen mutane da kutse a lalitarsu da kwashe musu kuɗaɗe.

 
iii- Mutum ba shi da tabbacin tsaro ga kuɗaɗensa sai dai idan abokan harkarsa waɗanda bai san su ba sun mutumta masa sun riƙe alƙawarinsu. Saɓanin bankuna da mutum yana da tabbas yadda za su kula da kuɗaɗensa. –(Engadget Primed: The Rise (and rise?) of Bitcoin na Daniel Cooper, 2013).


iv- Kimar Bitcoin ba ta tsayawa wuri ɗaya; tana mummunan tashi sannan katsahan/kwatsam ta sauka. A wasu shekarun sai ta yi tsada daga baya kuma sai nan da nan ta sauko ƙasa warwas. A farkon Janairu ɗin nan na 2021, ƙwandalar take Dala dubu arba’in da biyu ($ 42,000), sannan ta sauko ƙasa. A wannan sati na ƙarshen Janairu ta dawo Dala dubu talatin da biyu ($ 32,000).

 
v- wata matsalar kuma ita ce idan wani ya sayi kaya ta hanayar Bitcoin, amma sai ya ƙi tura kayan ga wanda ya saya, to ba wata hanya da za a dawo da kuɗin cikin sauƙi, domin ba wata masaniya a tsakaninsu, ba kuma wata kotu ko hukuma da za a ɗaukaka maganar da sunan kara.


vi- Idan an tura kuɗin Bitcoin ba za a iya shan kansu a dawo da su ba. Saɓanin banki wanda zai iya toshe kuɗin ya hana mutumin da aka aikawa amfani da su.


vii- Babu tabbas a yadda hadahadar crytocurrencies za ta kasance. Gold yana da tabbas, don ga shi a hannu za a ɗauka a taɓa, amma crytocurrencies, musamman Bitcoin daga cikinsu, ba su da wannan zarafi. Duk lokacin da tsarin manhajar ya ruguje a kan intanet, to kuɗaɗen mutane sun tafi kenan, kowa zai tsuguna ya yi jugum!


viii- Da yawa daga cikin kamfanonin da suke hulɗa da Bitcoin suna buɗe dama ga mutane don su shigo da kuɗaɗensu wajen wannan harka amma ba tare da sanin abokan haɗin gwiwar irin haɗarin da mu’amalar take da shi ba.

 
ix- Wani bincike ya nuna nuna cewa kusan kaso 20% cikin ɗari na kuɗaɗen da suke jibge a cikin babbar lalita ta Bitcoin, dukiyar mutane ce da suka kasa bude manhajar sakamakon manta lambobin buɗewar da suka yi!


6- A halin yanzu duk da waɗannan matsaloli amma akwai ƙasashen da suka huwace amfani da Bitcoin kamar su Jamus, Ingila, Sweden, South Korea, Kuwait, Oman, Jordon, da sauransu. Wasu manyan kamfanonin manhajar kwafiyoyutoci da kafofin sadarwa irinsu Microsoft da Google da Yahoo duk sun karɓi amfani da wannan ƙwandala ta Bitcoin. Haka nan wasu gidajen sayar da abinci da otel-otel duka sun yarda a biyasu ta hanyar amfani da ita. Takai ana sayan wasu tikitin na hawa jirgin sama da kuɗin Bitcoin. Sannan kuma an sami wasu jami’o’i kamar na Ƙasar Cyprus da suka yarda da a biyasu kuɗin makaranta da wannan kuɗi.


Duk da cewa ƙasar Jamus su ne suka fara yarda da tsarin mu’amalar Bitcoin, amma a zahiri ba wai a matsayin kuɗi ba. Sai dai kurum a matsayin ƙasar ta sami wata dama da za ta ɗora haraji ga manya da ƙananan kamfanonin da suke yin mu’amalar Bitcoin. Mutane kuma ɗaiɗaiku aka bar su ba tare da wani abu ba. Don haka sun yarda da shi ne don samun kuɗin shiga kurum.

 
A gefe guda kuma akwai ƙasashe masu yawa da suka hana amfani da Bitcoin kamar su Saudiyya, Dubai, Turkiyya, Misra, Morocco, Algeriya, Lebanon, Russia, da sauransu. Babbabn Bankin Ƙasar China ya hana hulɗa da Bitcoin tun 2013. Suka daɗa ɗaukar zafi wajen hana hulɗa da Bitcoin baki ɗaya a 2017 da 2018.-(Everything You Need to Know about Bitcoin: Its Mysterious Origins and the Many Alleged Identities of Its Creators na Zoe Bernard, 2018).


7- Wannan ya kawo mu ga yadda za a kalli mu’amala da Bitcon a Musulunce. Akwai abubuwa da yawa da za a duba daki-daki don a fitar da hukunci da ya dace da yadda ake gudanar da Bitcoin a hain yanzu. Abin da malamai suka tsaya suna ta ƙoƙarin tantancewa shi ne ɗabi’ar waɗannan ƙwandalar ta Bitcoin shin ‘kuɗi’ ce ko kuwa ‘kadara’ ce? An sami waɗanda suke kallo da fahimtar Bitcoin da ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi. A kan haka kuma suka fitar da hukuncinsu game da shi, wasu suka halatta, wasu suka haramta.-(The Shari’ah Factor in Cryptocurrencies and Tokens na Shari’ah Review Bureau a Ƙasar Bahrain; Shari’ah Analysis of Bitcoin, Cryptocurrency and Blockchain na Mufti Muhammad Abu-Bakar). Amma a gaskiya in an dube ta da kyau za a ga ba ta faɗa cikin ma’anar wani daga ɗayan abubuwan nan guda biyu ba. Haka nan yanayinta bai dace da yanayin kowane ɗaya daga cikinsu ba.


i- Duk da cewa masu harkar Bitcoin suna amfani kalmomin da suke nuna kuɗi ne kamar ‘coin’ ko ‘currency’ ko  "عُمْلَة" da sauransu, amma a haƙiƙa ba kuɗi ba ne. Domin bai cika wasu daga cikin ƙa’idojin da Musulunci yake la’akari da su a matsayin kuɗi ba. Waɗannan sun haɗa da:


a- Sai gwamnati mai ci ta amince da wannan abu a matsayin kuɗi wanda duk mutane za su rika mu’amala da shi.


Malaman Musulunci sun bayyana haka a fili. Imamu Ahmad bn Hanbal yana cewa, “Ba wanda zai buga kuɗi sai gidan buga kuɗi (na gwamnati) da izinin shugaban. Saboda mutane in an yi musu rangwame a kansa, sai su wuce gona da iri”. Sai Imamu Abu Ya’ala ya ce, “Imamu Ahmad ya hana a buga kuɗi ba tare da izinin shugaban ba. Saboda yin hakan wani ta’addanci ne gareshi”.—(Ahkamus Suldaniyyah na Abu Ya’ala: 181; Mukaddimatu Ibnu Khaldun: sh/226; Annukud Wal-Bunuk Fin Nizamil Islami na Dr. Auf Muammad Al-Kafrawi:sh/20-56) 


قال الإمام أحمد:"لا يصلح ضرب الدراهم إلا في دار الضرب بإذن السلطان، لأن الناس إن رخص لهم ركبوا العظائم". فعلق الإمام أبو يعلى الحنبلي قائلا:"منع من الضرب بغير إذن سلطان لما فيه من الافتيات عليه".

Imamu Nawawi shi ma ya yi bayanin cewa duk malaman Mazahabin Shafi’iyya ba su yarda da wani ko wasu gungun mutane su ware su buga kuɗi ko su ƙirƙiro wasu kuɗaɗe daban, wanda gwamnati ba ta yarda da shi ba. Ya ce, “Ana ƙin wanda ba shugaban ba ya buga kuɗi (kamar dinare da azurfa) ko da kuwa masu kyau ne sosai. Saboda buga kuɗaɗe aikin shugaba ne. Sannan kuma ba za a sami aminci ba, don za a iya samun algus da ɓarna a ciki”.(Al-Majmu’u na Nawawi:6/11; Raudatud Dalibina na Nawawi:2/258).


قال الإمام النوي-رحمه الله-:"يكره لغير الإمام ضرب الدراهم والدنانير، وإن كانت خالصة. لأنه من شأن الإمام. ولأنه لا يؤمن فيه الغش والفساد". 

Wannan yana nuna cewa kamar yadda ba a son fito-na-fito da gwamnati a sha’anin mulki da gudanarwa, to haka nan ba a son a Musulunce a keta alfarmar gwamnati wajen buga kuɗaɗe ba tare da wani izini ba. Domin tsayuwa da daidaituwar kuɗi wata alama ce ta tabbatuwar gwamnati.


Ibnu Khaldun ya yi bayanin cewa abubuwa guda biyu su ne ginshiƙan duk wata daula. Su ne ƙarfi soja da kuɗi. Idan za ta ruguje tana rugujewa ne ta hanyar rugujewar waɗannan abubuwa.-(Al-Mukaddimah na Ibnu Khldun: sh/294).

 
A nan Nigeriya, dokokin Ƙasa sun hana amfani da Bitcoin da hulɗa da shi. A 17 na Janairu na 2017 Babban Banki Ƙasa (CBN) ya haramta amfani da shi ta kowace fuska. Ma'anar wannan da a ce za a sami wani ya kai ƙarar wani da sunan ya riƙe masa kuɗi ta hanyar Bitcoin, ba za a saurari ƙarar ba. Saboda ba ta saɓawa dokokin ƙasa ba.
Sai dai yana da kyau a sani cewa, a zamani irin wannan ba wai yarda ko rashin yardar wata ƙasa kaɗai shi ne abin la’akari wajen halatta wani abu ko haramtashi ba. Saboda a yanzu ƙasashe sun yarda da tsarin banki mai ruwa, amma wannan bai sa an ce shi kenan yin hakan ya halatta ba. A lokacin da Daular Musulunci take da ƙarfi da iko, ana gudanar da abubuwa a kan Shari'ar Allah, a lokacin ana iya cewa ba laifi ana iya la'akari da wasu abubuwan saboda gwamnati ta yarda shi. Amma ko a da can har da kuma yanzu, ana duba yadda abu yake cikinsa-da-bayansa, sannan sai malamai su bada fatawa da za ta bayyana matsayinsa a Shari’a na halasci ko haramci. Wannan wani abin dubawa ne da kyau.


b- Bayan gwamnati ta yarda da duk abin da take ganin za iya tsayawa a matsayin kuɗi, za a ga duk mutane sun yarda da su a mu’amalolinsu na yau-da-gobe. Wannan shi ne abin da Imamu Malik yana cewa, “Da a ce mutane za su yarda da fatun dabbobi a tsakaninsu a buga su a matsayin kuɗaɗe, da ba zan so a sami jinkiri ba idan sun yi canja fata da dinare da azurfa".-(Al-Mudawwanah: 3/5. A dada duba ra’ayin Hanafiyya a Littafin Tanbihur Rukud Ala Ahkamiln Nukud na Ibnu Ibidn: sh/25).


قال الإمام مالك:"ولو أن الناس أجازوا بينهم الجلود حتى تكون لها سكة وعين، لكرهتها أن تباع بالذهب والورق نظرة".

Ma’anar maganarsa ita ce duk abin da mutane suka haɗu a kan cewa kuɗi ne, kuma suka gina rayuwarsu a kansa, ya zama kuɗi. Duk hukunce-hukuncen Shari’a na kuɗi za su shafe shi. Kuɗi suna da sifar zamowa tsanin da kowa-da-kowa zai yi amfani da shi wajen  saye-da-sayarwa. Ba a la’akari da kuɗaɗen da suka zamo masu gudanawa tsakanin wasu tsirarun mutane.-(Al-Warkun Nakadi na Sheikh Abdullah bn Mani’i sh/17). Bitcoin ba kuɗi ba ne da kowa-da-kowa yake da ikon amfani da su cikin sauƙi ba. Kudade ne in har an yarda ma cewa kuɗin ne da suke yawa a kan intanet kurum. Waɗanda suke hulɗar su kaɗai suka san da su, kunzumin mutane ba su da alaƙa da waɗannan kudaden na ɓoye!


c- Kuɗi abu ne na zahiri da yake zamowa ma’aunin kimar abubuwa a faɗin duniya, ta yadda abin da aka saya ya zamo daidai da kimar kuɗin da a ka sayeshi da su.-(Al-Mugni na Ibnu Kudama:5/419). Don haka ne ake da kuɗi kala biyu:


Na ɗaya: Abubuwan da su da kansu kuɗaɗe ne kamar gwal da azurfa. Har yanzu ana ɗaukar gwal cikin manyan abubuwan da ƙasashe suke ajiyewa a matsayin (Foreign Exchange Reserve).

 
Na biyu: Abubuwan da gwamnati ta yarda da su a matsayin kuɗaɗe kamar takardun kuɗi na Naira, Riyal, Dollar, Euro da sauransu. Tuntuni Malamai suka tabbatar da karɓar takardun kuɗi. Kafin wannan zamanin ma Imamu Malik ya faɗi maganar da aka kawo a sama. Har ila yau kuma Shehul Islam Ibnu Taimiyyah shi ma ya yi bayanin da za a ɗora takardun kuɗi a kansa. Ya ce, “Dinare da azurfa ba su da wata wani iyaka ta al’ada ko ta Shari’a.


Makomar lamarinsu ba ta wuce al’ada da abin da mutane suka yarda da shi a tsakaninsu. Saboda su kudi tun asali ba manufarsu kenan ba. Manufar ita ce su zamo ma’auni na abubuwan da ake mu’amala da su kurum. Dinare da Dirhami ba su da kansu ne manufa ba. A na ɗaukar su ne a matsayin tsani kurum don a yi mu’amala da su. Don haka ne ma suka zamo kuɗaɗe, saɓanin sauran dukiya, waɗanda asalin manufar samuwarsu ita ce a yi amfani da su”-(Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiyyah: 19/251).


قال شيخ الإسلام ابن تيمية-رحمه الله-:"وأما الدرهم والدينار فما يعرف له حد طبعي ولا شرعي. بل مرجعه إلى العادة والاصطلاح. وذلك لأنه في الأصل لا يتعلق المقصود به. بل الغرض أن يكون معيارا لما يتعاملون به. والدراهم والدنانير لا تقصد لنفسها، بل هي وسيلة إلى التعامل بها. ولهذا كانت أثمانا؛ بخلاف سائر الأموال. فإن المقصود الانتفاع بها نفسها. فلهذا كانت مقدرة بالأمور الطبعية أو الشرعية".

Manufar kawo wannan don a nuna cewa Bitcoin bai sami irin wannan darajar ta karɓuwa a matsayin kuɗi ba a ƙasashe da yawa ba. Abin da yake faruwa dangane da shi shi ne wani mutum ko wasu mutane ne kurum suka ƙiƙiire shi a kan intanet, sannan tsakanin duhun-dare da sanyin-safiya suka ɓace aka kasa ma gano ko waye har yanzu!

 
d- Sannan kuma ana biyan kuɗaɗe idan wani ya salwantar da su. Ita kuwa ƙwandalar Bitcoin, in ta salwanta, ba mai biya ko ya dawo da ita. Don haka ciniki da hulɗa da ita ya shiga haramci saboda garari da haɗarin da yake ciki.


e- Bitcoin ya fi kama da kuɗin-ganye (Alfulus): Ana ƙirƙirar kuɗin ganye ne saboda dalilai da yawa, musamman don a shirgar da su cikin mutane su bada mai kyau a ba su mara kyau. Ibnul Kayyim ya yi bayani mai gamsarwa a kan yanayin kuɗin-ganye. Idan aka yi la’akari da bayaninsa a kan Bitcoin za a ga kamannin ya bayyana sosai. Ya ce, “Kamar yadda ka gani dangane da rugujewar mu’amalar mutane da irin cutuwa da take samunsu idan suka fara amfani da kuɗin-ganye (Alfulus) a matsayin kadara don samun riba. Yin haka sai ya kawo cutuwa da za ta game ko’ina, zalunci ya yaɗu. Da an ɗauke su a matsayin kuɗi na-bai-ɗaya, baya ƙaruwa ko ya ragu, wanda zai zamo ma’aunin abubuwa, amma ba a auna shi da kadarori, da an yi haka da lamarin mutane ya gyaru...Saboda ba a burin samun kuɗi su a karan-kansu, sai dai ana buƙatar su ne don akai ga sayan kadara/haja. Idan kuɗaɗe su da kansu suka zamo kadara, ana hanƙoron a same su kamar kadara, sai lamarin mutane ya lalace. Wannan bayani ne na hankali da ya shafi zallan kudi, ba zai tsallaka zuwa wasu Abubuwan ba”.-(I’lamul Muwakki’in An Rabbil Alamin na Ibnul Kayyim:2/156-157).


قال الإمام ابن القيم-رحمه الله-:"كما رأيت من فساد معاملاتهم، والضرر اللاحق بهم، حين اتُّخذَت الفلوس سلعة تعد للربح، فعم الضرر، وحصل الظلم. ولو جعلت ثمنا واحدا لا يزداد ولا ينقص بل تُقوّم به الأشياء، ولا تقوم هي بغيرها لصلح أمر الناس...فالأثمان لا تقصد لأعيانها، بل يقصد التوصل بها إلى السلع. فإذا صارت في أنفسها سلعا تقصد لأعيانها، فسد أمر الناس. وهذا معنى معقول، يختص بالنقود لا يتعدى إلى سائر الموزونات".

Malamai irinsu Imamu Gazali suna faɗa cewa, “Idan kuɗin-ganye suka sami karɓuwa kamar kyawawan kuɗaɗe, to sai su zamo kamar kadara, a maganar malamai mafi inganci”- (Nuzhatun Nufusi Fi Bayani Hukumit Ta’amuli Bil Fulusi na Ibul Ha’imi Ahamd bn Muhammad, sh/47).



ii- Duk da cewa Bitcoin ya so ya yi kama da ‘kadara/haja’ (Legit commodity/goods) amma ba kadarar ba ce. Domin ita kadara/haja tana zamowa a hannu sannan ta biyawa wanda yake da ita wata buƙata ta musamman kamar ya sa a cikinsa ko ci ko ya sha ko ya shiga in gida ne ko ya hau kamar mota ko keke da doki da sauransu. Haka nan kadara tana samun kula ta wajen tabbatar da kyau da tsari daga hukumomi. Bitcoin kuwa ba ta da irin waɗannan siffofi. Saboda Bitcoin tana gujewa hukumomi. Sannan kuma iyakacinta kan intanet ba ƙari. Shi ya sa bai dace ba a ɗauke ta a matsayin kadara har kuma a gina hukunci na halaccin tsarin bakiɗaya a kan haka.


MATSALOLIN BITCOIN
Hoto: Newsbit

 
iii- Bitcoin ba shi da zubi da tsari irin na katinan da ake ajiye kuɗaɗe a cikinsu kamar su Visa Card, Master Card da sauransu. Saboda su waɗannan katina suna da wasu kamfanoni da suke kula da su. Amma tsarin Bitcoin ya tsani duk wata hulɗa da za a ginata a kan wani kamfani a tsakiya tsakanin mutane!


8- Bisa irin bayanai da aka kawo a ƙarƙashin lamba ta 5 na matsaloli guda tara, da bayanan da suka zo a ƙarƙashin lamba ta 7, duka waɗannan suna nuna cewa wannan harka ta Bitcoin tana ƙunshe da abubuwa da yawa da suka isa a ce ‘Haram’ ce bisa dokokin Shari’a.


Ga bayanin dailan haramcin a dunƙule:


i- Riba: Riba tana shiga hadahadar Bitcoin musamman ta fuskoki biyu:


Fuska ta ɗaya ana sayar da ƙwandalar bitcoin da bitcoin da fifiko da ƙarin wata a kan wata, wanda yake riba ne. Sannan a wasu lokutan ana samun jinkiri, ba a samun hannu-da-hannu ko da ‘bayarwa ta ma’ana’ ce a wajen canji da ake yi tare da sauran kuɗaɗe.

 
Fuska ta biyu kuma, kamfanonin da suke saye da sayar da Bitcoin a kasuwannin kuɗi, wato (brokers), suna karɓar kuɗin mutan kamar ₦5,000, sai su ranta masa wasu kuɗaɗen masu yawa kamar ₦50,000 a kan waɗancan. Daga nan sai su zuba su a sayen ‘share’. Idan kuɗi suka haɓaka, aka ci riba, sai su ba wa mutum iya kason da ya dace da kuɗinsa, su kuma su riƙe ragowar a matsayin (commission). Wannan shi ake kira da ‘Leverage’, wanda yake haramun ne ta fuskoki da yawa. Daga ciki dai Akwai bashi da riba da aka yi da sunan wanda ya sa kuɗi tun farko. Sannan kuma ya yarda da ya taimaka a ci riba. Wannan duka haram ne.

 
Idan kuma an faɗi, to duk kuɗin mutum (₦5,000) ɗin baki ɗaya sun salwanta, ya yi asararsu! Wannan ɓangaren ya shiga tsarin caca tsundim!


ii- An gina Manhajar Bitcoin a kan tsarin caca. Shi ma wannan zai iya zamowa ta fuskoki da yawa, musamman gida biyu.
Fusaka ta ɗaya ita ce wadda ta gabata a misalin da aka faɗa a lambar sama cewa idan mutum ya sa kudi misali (₦5,000), shi kuma ‘broker’ ya ƙara, sai a ka sami asara, to kuɗin mutum sun nutse baki ɗaya, ba zai sami komai ba.

 
Fuska ta biyu kuma kamfanomin da suke fafutukar samo ‘coin’ ɗin ta hanyar ‘mining’ suna kashe ɗimbin kuɗaɗe su tsunduma cikin zabari tare da sauran masu nema, a ƙarshe sai guda ɗaya ne zai iya samu a cikin minti goma. Sauran ba wanda zai sami wani abu. Kowane irin abu suka kashe na dukiya ya tafi a banza.
 

 
iii- Cin dukiyar mutane ba-gaira-ba-dalili: Kula da dukiyoyin mutane da kiyayesu daga salwanta yana daga cikin manufofin Shari’a. Akwai sauƙi sosai ta hanyar Bitcoin a sami damar cin dukiyar mutane ba tare da wata wahala ba. Saboda yadda farashin Bitcoin yake gwauran tashi a ɗan ƙanƙanin lokaci, yana huwacewa wasu su azurta da kuɗaɗen mutane ba gaira-ba-dalili. Sannan kuma ya sauka a ɗan lokaci, ta yadda wasu za su yi gagarumar asara. Wannan yana bada tsoro har ana tunanin cewa akwai wasu a ɓoye masu ci da gumin sauran mutane! Tsarin hawa da saukar Bitcoin ya wuce tsarin yadda aka san cinikayyar canji a kasuwar duniya ta yadda hawa da saukar ba wani mai yawa ba ne, amma ba ya ninninka ba. Misali Bitcoin ya taɓa ninkawa har sau ɗari uku a 2017 sannan kuma ya ruguzo! Wannan yana nuna Bitcoin ba kuɗi ba ne da za a dogara da shi. Wasu daga cikin masana tattalin arziki suna cewa, ‘hauhawar Bitcoin kamar tashin kumfa take’ (bubble), nan da nan za ta sauka a dawo ƙasa!


Imamu Ibnu Kayyim ya fayyace wasu ƙa’idoji da za a fahimci yadda tsarin kuɗi yake a Musulunci. Ya ce, “Dirhami da Dinare kuɗaɗe ne na kadarori da kayan sayarwa. Abin da ake nufi da kuɗi shi ne ya zamo ma’auni, wanda za a riƙa kimanta kimar sauran dukiya da shi. Don haka ne dole ya zamo mai iyaka, a san gwargwadon yadda zai kai ya kawo, ba ya tashi sama sosai, ko ya faɗi ƙasa warwas! Domin idan kuɗi yana tashi , yana sauka kamar wata kadara, ba zai zamo nan kuɗi da za a riƙa la’akari da shi wajen kimar kayan sayarwa ba. Sai duk su zamo kadara ne, tare da cewa buƙatar mutane zuwa ga tsuran kuɗi wanda za su riƙa la’akari da shi dangane da kayan sayarwa, wannan buƙata ce ta larura, da ta shafi kowa. Shi kuwa tabbatar da wannan sai da wani farashi da za a san kimar abubuwa da shi. Shi ma wannan sai da wani tsarin kuɗi da za a riƙa yi wa abubuwa kima ta kima da shi, wanda zai zarce a kan hali ɗaya, ba wai shi ya zamo ana yi masa kima da wani abin ba, saboda ya zamo kadara da zai tashi ya sauka. Yin haka kuwa zai ɓata tsarin mu’amalar mutane, saɓani ya shiga tsakaninsu, cutuwa ta tsananta a cikinsu” -(I’lamul Muwakki’in An Rabbil Alamin na Ibnul Kayyim:2/157).


قال الإمام ابن القيم-رحمه الله-"فإن الدراهم والدنانير أثمان المبيعات. والثمن هو المعيار الذي به يعرف تقويم الأموال، فيجب أن يكون محدودا مضبوطا لا يرتفع ولا ينخفض. إذ لو كان الثمن يرتفع وينخفض كالسلع لم يكن لنا ثمن نعتبر به المبيعات، بل الجميع سلع. وحاجة الناس إلى ثمن يعتبرون به المبيعات حاجة ضرورية عامة. وذلك لا يمكن إلا بسعر تعرف به القيمة. وذلك لا يكون إلا بثمن تُقوّم به الأشياء، ويستمر على حالة واحدة. ولا يُقوّم هو بغيره، إذ يصير سلعة يرتفع، وينخفض، فتفسد معاملات الناس، ويقع الخلف، ويشتد الضرر".

Wannan bayani ne mai matukar ƙarfi, tare da cewa Ibnul Kayyim ya yi shi ne bisa duba da la’akari da tsarin kuɗi tuntuni. Sai dai a zahiri bayani ne kamar yau aka yi shi da ya shafi irin gararin da Bitcoin yake son jefa mutane a ciki. Domin a halin yanzu mu’amalar da ake yi da Bitcoin ɗin tare da cewa ana yi masa kirarin cewa kuɗi ne, amma mu’amalar irin wadda Ibnul Kayyim ya faɗa tana so ta mayar da shi kamar kadara/haja ba kuɗi ba !!


iv- Garari: Akwai garari a ciki saboda idan an tura kuɗaɗe ba za a iya shan kansu ba a dawo da su ba, idan misalin an fasa cinikin. Sai dai in wancan ɓangaren wanda ba a san kowaye ba, ya tausaya ya dawo da su. Sannan wanda aka yi ciniki da shi zai iya cinyewa mutane kuɗaɗensu ba tare da an kai shi wurin hukuma ta hukunta shi ba. Don haka wanda yake wannan mu’amala ya shirya karɓar mummunar asara da abokan mu’amalar ba za su san mai yake ciki ba ma ballantana su yi tunanin tausaya masa ba!


v- Jahala: A cikin hulɗar Bitcoin akwai rashin sanin yadda wasu abubuwan suke gudana da yawa. Domin ba komai ne a fayyace ba. Hatta wanda mutum yake hulɗar da su, mutum bai gama fahimtar su waye ba, ta yaya suka tara kuɗaɗensu, shin yana taimakawa marasa gaskiya ko kuwa?


Da dai sauran irin waɗannan tambayoyi masu wahalar amsuwa. Muhimmi dai ana so a gina ciki ba jahiltar abin da cikin ya ƙunsa. Imamu Ibnul Arabi Al-maliki yana cewa, “Malaman wannan al’umma sun haɗu a kan cewa cinikayya ba ta ƙulluwa sai ga abin da aka sani, daga wanda aka sani, da abin da aka sani, ta kowace irin fuska wadda za a iya samun sanayyar”-(Al-Kabas Shurhul Muwadda na Ibnul Arabi Al-Maliki:2/786-803).


قال الإمام ابن العربي المالكي-رحمه الله-"وقد اتفقت الأمة على أنه لا يجوز إلا بيع معلوم من معلوم بمعلوم- بأي طرق العلم وقع".  

9- Kasancewar duk ma’anoni guda uku da suke ruguza ciniki wato, riba, garari da algush, sun haɗu a wannan mu’amala ta Bitcoin, ya wajaba ga wanda yake yin hada-hada da Bitcoin da ya dakata, ya daina. Ya sayar da abin da ya tara a lalitarsa sannan ya kwashe uwar kuɗinsa, ragowar kuma ya bada su sadaka ko ya sa su a wani aikin alheri da al’umma za ta amfana da su bakiɗaya. Wannan saboda Allah Maɗaukakin Sarki ya ce, “In kun tuba, to sai ku riƙe uwar kuɗinku, ba ku zalinci kowa ba, kuma ba a zalinceku ba”-(Bakara2:279)

 
"وَإِنْ تُبْتُمْ فَلَكُمْ رُءُوسُ أَمْوَالِكُمْ لَا تَظْلِمُونَ وَلَا تُظْلَمُونَ"-(البقرة:279) 

10- Mu’amalar Bitcoin tana da ɗan rikitarwa. Abubuwa da yawa ba su bayyana ba a cikinta sai daga baya. Wannan ya sa malamai sun yi ɗan saɓani wajen fitar mata da hukunci, musamman a shekara ta 2017, a lokacin da lamarin Bitcoin ya bunƙasa, mutane suka faɗaka da irin yadda za ta kawo musu kuɗi suna kwance, ba wata wahala.


Malamai a ɗaiɗaikunsu da kuma Majalisu sun zauna a lokuta daba-daban don su tabbatar da hukuncin wannan mu’amala.


Daga cikin waɗanda suka tattauna mas’alar, suka kuma tabbatar da cewa ta saɓawa Shari’ar Musulunci akwai Majalisar Malamai ta Ƙasar Turkiyya (Darul Ift’it Trukiyyah, 29/11/2017: https//goo/gl/KVqoyr), da Misra (Darul Ifta’il Misriyyah, 28/12/2017: https//goo/gl/WTMpdu); da Falasdinu (Majlisul Ifta’ Al-Filisdiniyya: https//goo/gl/TEMmlu).


Haka nan, akwai taron ƙarawa-juna-ilimi da aka yi a Doha ta ƙasar Qatar (4th Doha Islamic Finance Conference) a January, 2017 M. sun tattauna irin kuɗaɗen da ake hulɗa da su ta hanyar intanet kawai. Masu taron, waɗanda suka haɗa da Dr. Abdussattar Abu Ghudda-Allah ya yi asa rahama- da Dr. Aliyu Kardagi da sauran masana a fagen tsarin tattalin arziki na Musulunci, sun tabbatar da cewa irin waɗannan sababbin cinikayya suna da rikitarwa da haɗarin gaske, musamman da yake ba wani nassi da ya zo a kansu. Amma fitar da hukunci ga irin waɗannan mas’aloli ba zai gagari masana Fikihu ba a cikin malaman Musulunci.


Bayan haka manyan malamai sun daɗa zama a ƙarƙashin Majma’ul Fikihil Islami Addauli (International Islamic Fiqh Academy) a farkon shekara 1441 H./2019, a inda suka tattauna sosai a kan ɗabi’ar wannan mu’amala.

 
11- Akwai wasu abubuwa waɗanda idan Bitcoin da sauran hulɗoɗi masu kama da shi suka cika su za a iya la’akari da su a janye haramcin da yake kansu a yanzu kamar yadda Sheikh Aliyu Kardagi ya bada shawara. Waɗannan abubuwa sun haɗa da:


i- Gwamnati ta ɗauki Bitcoin a matsayin kuɗi. Don haka sai a samu wata ƙasa ta yarda da tsarin Bitcoin da makamantanta, ta yadda Babban Bankin ƙasar zai amince da hulɗa da ita. Sai a sawa manhajar ƙa’idoji. Yawancin ƙasashen da ake cewa a yanzu sun karɓi tsarin, sun karɓa ne a dunƙule, amma ba su sa dokokin da za su maida Manhajar ta zamo ƙarƙashin Babban Bankin waɗannan ƙasashe ba. Don haka kada wani ya ruɗu da zancen ai Akwai ƙasashen da suka yarda da tsarin.


ii- A ɗauki Bitcon a matsayin ‘kadara/haja’. Wannan kuma sai an sami kamfanonin da za su riƙa juya Bicoin ɗin a matsayin “share”, ta yadda kowace ‘share’ za ta zamo a na ganinta cikin jumlar tsarin waɗannan kamfanonin. A halin yanzu Bitcoin ba shi da wannan tsarin ta kowace fuska. 

 
iii- Ya zamo kamar tsarin su Visa Card, Credit Card, da sauransu. Ta yadda za a sami wasu kamfanoni da za su ɗauki gabaran gudanar da tsare-tsarensa da hadahadarsa da shige-da-fitarsa kamar yadda ake yiwa waɗancan katika.


Yin ɗaya daga cikin wannan zai ba wa Bitcoin wata sabuwar kima ta halacci a idon Musulmi.  

 
A ƙarshe, hadahadar Cryptocurrency a karan kanta ba za a iya cewa haram ba ce, ba laifi Musulmin duniya su fara tunanin yadda za su ci moriyar hakan ta hanyar da ta halatta wadda aka nuna a nan sama kaɗan. Saboda da alamu nan gaba kaɗan duk duniya za a raja’a a kan Digital Money. Amma dai a halin yanzu idan aka yi la’akari za a ga cewa wannan mu’amala ta Bitcoin ta faɗa ɓangarori da yawa na haramci a Shari’ah, ba wai wani ɓangare ɗaya ne kurum ba.

 

A ƙarshe muna yiwa Allah godiya, da  fatan ya sa mun dace.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user