Saturday 1 June 2024

Hirar Soyayya A Tsakanin Saurayin Zamani Da Ustaziya

Tura Wannan Zuwa Ga
Saurayi: Masoyiya wallahi son da nake miki ba ya misaltuwa, na kai hatta idan ina Sallah ke kawai nake gani, wani lokacin har sunan ki nake faɗa a maimakon tasbihi, ki tausaya min ki soni.

Hirar Saurayi Da Ustaziya
Hoto: Islam4U


Marubuci: Hafiz Sufyan


Ustaziya: Gaskiya ni kuwa ai ba zan so ka a haka kana fifita so na da sallah ba wacce ita ce ginshiƙin addini, ai sai ka hallaka, a'a gaskiya ni irin kalar wannan son ba na son shi.


Saurayi: Masoyiya ai idan na mallake ki duk wannan zan daina tunda na dai samu muradina a tare da ni, da ma rashin ki ne ke sanya haka.


Ta yi wuf ta ce to da ma ashe son na ƙarya ne, idan ka mallake ni dainawa za kai, ai wallahi ku maza duk halin ku ɗaya. Idan kuna son mutum komai gani zai yi, amma da kun samu abin da ku ke so sai ku zama kamar mara lafiyar da ya warke.

NI: Ai ku ɗin ne sai da haka.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user