Friday 31 May 2024

Abubuwa 5 Da Za Su Inganta Rayuwar Matasa A Yau

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan na ba ka mamaki, to ni ma ka ba ni mamaki. Ba'a fafan gora ranar tafiya. Idan ka shirya wa Litinin, to mene ne abun fargabar ta? Kasala ne? Ko ka manta kasala cuta ne, kuma rashin ta nasara ne? Batun gaskiya duk inda ake hangen nesa a kowace rana, da aiki babu ganda, da rashin son zuciya, da fahimtar juna to ina son kasancewa a ciki. Litinin kuwa ta kasance ranar da ake haɗuwa da jama'a musamman bayan hutawa a ƙarshen mako. Yanzu ga wani ɗan guzuri nan domin taimaka wa matashi wajen tsayawa akan ƙafafun sa. 


INA KAUNAR LITININ
Hoto: Begin again institute



MarubuciBello Galadanchi


Kafin na yi nisa, ina so na yi tuni; duniyar nan kullum canzawa take yi, kuma ba ta jiran kowa. Idan yau ka share sa’o’i tara kana bacci, wani shida ya yi, sannan ya yi amfani da ukun da kake bacci wajen yin wani abu da zai bunƙasa rayuwar shi ya fi ka samun ilimi, ko ya fi ka dabaru, ko ƙwarewa, ko samun kuɗi, ko fahimtar sirrin yau da gobe. Duk matashin dake so ya bunƙasa kan shi, to akwai abubuwa 5 da ya kamata ya mallaka:


1. BURI: Duk matashin dake da buri, jama’a sun fi sha’awar shi, sannan yana harzuƙa mutane tare da samun dama iri-iri daga bil adaman da yake haɗuwa da su. Idan kana da buri, to kai abokin kowa ne. 


2. DARAJA: Daraja abu ne da kowa yake so ya ƙara. Idan abokai ne da kai, ko aiki, ko sana’a, to idan har ka darajanta kanka, to za’a kusance ka, kuma za’a saka ka a inda darajar ka za ta yi amfani. Ka yi ƙoƙarin ƙware wa a wani abu, ko ka kammala karatu. Bugu da ƙari, halin ka ya zama mai kyau, duk waɗannan za su ƙara maka daraja sannan za ka gina wa kanka gimshiƙin rayuwa mai ƙarfi. 


3. IYA MAGANA: Matasa masu yawan gaske suna fama da matsalar rashin iya bayyana abin da ke cikin zuciyarsu a sauƙaƙe. Waɗannan abubuwa sun kama daga ƙwarewar su, hikimar su, irin burinsu da aikace-aikacen da suka yi a lokacin da suke neman ilimi. Nasara a rayuwa ba farilla ba ce, saboda haka idan har kana so, dole sai ka miƙe ka nema. Kuma a lokacin da kake nema, akwai miliyoyi kamar ka da suke nema kuma ba su samu ba. Sai ka zage damtse ka ƙware a magana, kuma ka faɗi gaskiya. 


4. ƘWAREWA: Duk dabbar da ba ta da dabara a cikin dawa, to kuwa sunan ta gawa. Duk mutumin da ya ƙi ƙwarewa wajen yin wani abu a rayuwa, to shi ma sunan sa gawa, saboda da shi da gawar marabar su kaɗan ce. Idan ba ka ƙware a wani abu ba, to ba ka da daraja. Idan ba ka da daraja, babu wanda zai yi sha’awar ka ko ya so ya yi mu'amala da kai. Jama’a sun fi ƙaunar gwal saboda yana da daraja. Kar ka zama dutse, ka samu wani abu ka mayar da hankali akai ka iya shi yadda ya kamata. Kar ka yi ta kame-kame a rayuwar ka.


5. NEMAN ILIMI: Wannan yana da matuƙar amfani. Ko kai Farfesa ne, to idan har kana so ka cika mutum, kuma ka cimma burin ka na rayuwa, to ka buɗe idanunka kullum wajen neman sani. Idan ka haɗu da wanda ya san wani abu da ba ka sani ba, to ka girmama shi, ka yi tambayoyi domin ya fahimtar da kai. Ka nemi littatafai ka karanta. Ka binciki duk abin da yake ba ka sha’awa. Kar ka dogara akan karatun makaranta kawai, a’a, ka hau yanar gizo ka yi bincike. Ka samu masani ya yi maka ƙarin bayani. Ka zama mayunwaci a neman ilimi har ƙarshen rayuwar ka. 


Zaman duniya ba abu ne mai sauƙi ba. Idan ka zauna zaman jira ba tare da inganta rayuwar ka ba, to a haka za ka ƙare jama’a ba su darajanta ka ba, kuma kai ma ba ka darajanta kanka ba. Allah Ya kiyaye mu, kuma Ya bamu rayuwa mai albarka.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user