Monday 14 October 2019

SHIN SHIGOWAR JARUMA MARYAM YAHAYA KANNYWOOD CE SILAR KWARAROWAR KANANAN JARUMAI A KANNYWOOD?

Tura Wannan Zuwa Ga
Kusan za a iya cewa babu wani lokaci da aka samu bunkasar kwararowar kananan yara a cikin harkar fim kamar a yanzu, inda abin ya zamo wani kalubale ga masana’antar shirya finafinan Hausa, Kannywood.


Jaruma Amal Umar, Bilkisu Shema, Maryam Yahaya


Shekaru uku da suke shude, bayyanar fitacciyar jaruma Maryam Yahaya mai karancin shekaru, ba kamar yadda ake ganin sabbin jarumai suna shigowa ba, wadanda da daman su idan aka yi hira da su za ka ji sun ce sun taba yin aure wasu ma har da 'ya'ya.

Nasarar da Maryam Yahaya ta samu lokacin da aka saka ta a cikin fim din Mansoor, shi ne kashin bayan fitowa daruruwan kananan ‘yan mata domin su yi fim.

Tasirin ta ya kara dagawa a lokacin da ta fito a ciki fim din Mijin yarinya, wanda hakan ya yi wa yara mata da dama tasiri tare da ba su karfin gwiwar shigowa harkar fim, tsananin matsin rayuwa da ake ciki ya sa wasu iyaye suka rika kwaso 'ya'yansu suna kawowa a saka su a fim saboda ga karamar yarinya Maryam Yahaya ta zo lokaci guda ta daukaka, ta yi suna kuma tana hawa mota mai tsada, ga kuma manyan wayoyi tana rikewa.

Babu wani dogon nazari a kan shin da gaske fim ne yake ba ta wannan kudin ko kuma wani kasuwanci take yi? Ko Kuma akwai wata hanya ta karkashin kasa da take kawo mata kudin. Sai dai mutane sun fi karkata kan alherai ne take samu daga masoyanta da ke sassa daban-daban na duniya.

Sai dai a daidai lokacin da aka rika kawo yaran nan babu kan gado, to sai ya zama harkar fim din tana kara samun koma baya ta fuskar kasuwanci, saboda haka bayan Maryam Yahaha, ba a kara samun wata matashiyar jaruma sa’arta da ta samu daukaka ba.

Da yake harkar tana da wani sirri na idan aka shigo ba kasafai ake iya fita ba, sai ya zama yaran da suka shigo babu aikin yi sai su yi ta watangaririya a gari, ba nan, ba can. Amma idan jama’a dole ana yi mata kallon ‘yar fim. Har ila yau, tasirin kafafen sadarwar zamani na kara taimakawa wajen fitowar ‘yan mata.

Babban abun lura shi ne, cikin irin wadanan yaran akwai wadanda ba su taba fitowa a fim ba sai wannan wakokin da suka yi suka yi ta turawa a online, amma sun mallaki manyan motoci da wayoyi masu tsada, kuma duk inda suka je da sunan harkar fim suke nuna kan su.

Da yake abin ya shafi bangaren jarumai ne, wakilinmu ya tuntubi shugaban kungiyar jarumai ta kasa Alhassan Kwalle, dangane da barin yara da suke yi shigowa harkar fim kuma suna gani ana saka su ba tare da sun dauki wani matakin hanawa ba.

Alhassan Kwalle, “Gaskiya muna yin iyakar kokarin mu sai dai muna samun matsala ne daga su masu shirya fim din wato Daraktoci da kuma Furodusoshi, domin suna fakewa ne da cewar ai labarin ya zo da yara ne shi ya sa suke saka su, amma duk da haka muna iyakar kokarin mu don ganin an magance wannan matsalar.”

A doka ta Hukumar Tace Finafinan ta jihar Kano ba a yarda ga duk yarinyar da ba ta kai shekara sha takwas ba ta shigo harkar fim, wanda ko a lokacin Abubakar Rabo an dakatar da Maryam Booth saboda shekarun ta ba su kai ba, hakan ya ba ta damar ta tafi ta ci gaba da karatu kuma a sherarar da ta gabata ta gama digirin ta.

MUKALOLI MASU ALAKA:

Tsohuwar Jarumar Kannywood Mansura Isah ta Yiwa Jaruma Sadiya Haruna Nasiha Mai Zafi

Kalli Kayatattun Hotunan Jaruma Maryam Yahaya Hotunan Sun Dauki Hankulan Duniya Sosai

Zargin Luwadi a Kannywood 'Yan sanda Sun Kama Sadiya Haruna

Sai mun ji ta bakin Shugaban Hukumar Tace Finafinai Isma’ila Na’Abba Afakallu, kan shin dokar ta daina aiki ne? saboda haka ya ce, “Har yanzu dokar tana nan, don haka ne ma muka samar da tsarin yin rajista ga 'yan fim din kuma ka jira ka gane nan da dan lokaci kadan duk yarinyar da ba ta kai shekarar da take ta ka'ida ba, ba za a ba ta lasisin yin fim ba.”

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Source: Northflix
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user