Thursday 5 January 2023

Hukunci Tare Da Muhimmancin Yin Aure Ga Musulmai A Addinin Musulunci

Tura Wannan Zuwa Ga

Yin aure, abu ne da ya dace da  shari'a da lafiyayyan hankali da al'ada mai kyau. Akwai hikimomi da fa'idoji masu tarin yawa wajan yin aure, ga maza da mata, Allah ta'ala ya ce: (fassara) "Su matanku tufafi ne a gareku kuma tufafi ne a gare su.". Suratul Baƙara. 


Muhimmancin Yin Aure Ga Musulmai
Hoto: About Islam


MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


AURE A INUWAR MUSULUNCI DAGA LITTAFIN KIMIYYAR AURE


Wannan  aya ta nuna aure ado ne kwalliya ne, sutura ne rufin asiri ne mutuncin ne da daraja, saboda yadda aka kamanta rayuwar ma'aurata da tufafi, yadda tufafi suke ga Ɗan Adam, suna da amfani da yawa don haka aka kamanta rayuwar aure da tufafi, daga ciki amfanin tufafi akwai rufe tsiraici da yin kwalliya, da sutura, kuma duk wanda zai ɗinka tufafi yana buƙatar yasan kalar yadin da zai saya, na auduga ko na kattani ko na roba, mai kauri ko mai shara-shara,  mai tsada ko mai arha ko tsaka-tsaki,  fari ko baƙi ko wata kala daban, sannan wajan ɗunki mai yalwa ko mai matsi, ko kadaran kadahan, to haka rayuwar aure take wajan zaɓin abokin zama.


HUKUNCIN YIN AURE


Kasancewar mutane sun bambanta a halitta da halaye da yanayi, yasa malamai suka kalli ayoyi da hadisai da suka yi kira akan yin aure suka ba su fassara kashi uku:


Wasu malamai suna ganin yin aure sunna ne, abin da suke nufi, idan ka yi aure za ka sami lada, amma idan ba ka yi aure ba, kuma ba ka yi fasiƙanci ba, ba ka da alhaki. Wannan shi ne ra’ayin mafi yawan malamai, Badayatul mujtahid na Ibn Rushed 2/23. Addasuƙiy 2/214. Almugniy 6/446.


Na biyu sun ce yin aure sau ɗaya a rayuwa wajibi ne ga mutum, idan ya zauna bai yi aure ba ya yi laifi, domin wajibi shi ne abin da shari'a ta nemi ayi shi dole, idan mutum ya yi yadda aka umarce shi zai sami lada, idan kuma yaƙi ya zama abin zargi, kuma ana iya yi masa uƙuba akan haka. Saboda ko ba komai aure yana cika kamalar mutum mace ko namiji. Kuma abubuwan da suke cikin aure suna da yawa na buƙatu tsakanin namiji da mace, don haka idan aka yi aure kowa zai amfana. Wata ruwaya daga Alimam Ahmad, da wasu manyan Malamai daga cikin magabata, Almuhallah na ibn Hazamin, 9/440. Fathul Bariy 9/110. Dauda azzahiriy, Ibn Hazamin.


Na uku suka ce shi aure ya kasu gwargwadon yadda mutane suka karkasu;


Na ɗaya wanda aure ya zama wajibi a kansa. (shine wanda yake da ƙarfin sha'awa kuma yana da halin da zai iya riƙe auran ko sana'a, kuma idan bai yi auran ba zai yi lalata.).


Na biyu wanda aure ya zama sunna akansa. Wanda zai iya ɗaukar nauyin iyalin kuma yana yin wata sana'a ko neman ilmi, ba shi da sha'awa mai ƙarfi).


Na uku wanda aure ya zama haramun akansa. (Wanda ba zai iya ɗaukar nauyin matar ba, kuma ba shi da buƙatar auran, ko idan ya yi zai dinga cutar matar, wajan hana ta haƙƙoƙinta, ko ba shi da lafiya wajan biyan buƙatar iyali).


Na huɗu wanda aure ya zama makruhi akan sa. (ba a so ya yi aure saboda ya shagala da wani abu mai muhimmanci, ko ibada ko wani ilimi, ko wani bincike wanda ya hana shi samun lokaci, ko kuma ba shi da sha'awa, kuma babu tsoran yin lalata tare da shi.).


Na biyar wanda aure ya zama halal a gare shi (idan ya yi babu matsala, idan bai yi ba babu matsala).


Wannan shi ne magana Malikiyya, kuma akwai irin wannan ya shahara a fatawar daga wasu cikin shafi'awa da Hanbaliya. Fathul Bariy 9/110. Alƙawaninul Fiƙhiyya Ibn Juzay. 193.

 

Wannan shi ne fassara da malamai suka bayar ga dukkan ayoyi da hadisai masu kira da yin aure.

 

Amma ba kowa ya kamata ya yi aure ba saboda wasu ba su da sha'awa wasu ba su da lafiya wasu ba su da hali wasu ba su da lokaci, wasu kuma sun shagala da wani abu da ya fi yin auran muhimmanci a wajan su a wannan lokacin, kamar yadda Shaikh Abu Gudda ya kawo tarihin wasu malamai maza da mata waɗanda har suka gama rayuwar su ba su yi aure ba, yawan ya haura talatin, a cikin littafinsa mai suna Al'ulama'ul Uzzab.


Haka kuma ba kowa zai ƙi yin aure ba, domin wasu suna da buƙatar yin auran, domin samun zuriya, wasu domin samun abokin rayuwa wasu domin kare kai da gujewa lalata, kamar zina, maɗigo da luwaɗi, wasu domin ƙara mutunci da kamala.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user