Friday 13 January 2023

Matsalolin Soyayya 12 Ga Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga
Shi dai so abu ne me daɗi wanda kowa yake so, to amma a cikinsa da akwai wahalhalu kala-kala waɗanda kowa da irin wanda ya taɓa fuskanta.

BABBAR WAHALAR DA KE CIKIN SOYAYYA
Hoto: Wallpaper House

MarubuciNura Nakowa

Wani bai taɓa shan wahalar soyayya ba, wani ya sha ɗan kaɗan, wani kuma gabaki ɗaya soyayyar sa a wahale take.

Idan aka ce wahalar da ke cikin soyayya wasu za su yi tunanin cewa rashin dace a soyayya ko ka nema ka rasa shi ne kaɗai wahalar soyayya. Ba haka ba ne. Daɗi da ɗacin da ke cikin soyayya kowannen su yana ɗauke da nasa irin nau'in wahalar.

Bari mu fara da ɓangaren daɗin:

Daɗin dake cikin soyayya shi ne Farantawa, Kyautatawa, da Kulawa.

To a yayin gabatar da waɗannan abubuwan guda uku dole sai da ujula. Kowanne daga cikin su (farantawar da kyautatawar da kulawar) a aikace ake yinsa.

Dukkanin su suna buƙatar lokaci da yanayi da kuma Ihisani. Sai ka samu lokacin da za ka dinga zuwa yin hirar da za ta farantawa masoyiyar. Haka ma ita macan. Hakanan kuma a soyayyar ku kakan yi alkhairi da yin kyauta, kamar sayawa masoyin ka abin da zai ci ko ya sha ko abin da zai saka a jikinsa domin ya yi kwalliya irin su sutura da kayan ƙyaleƙyale.

Waɗannan aikace-aikacan da zirga-zirga da baye-bayen da kakeyi, su ma wahalhalu ne a cikin soyayya amma ba a lissafa su a matsayin wahalar da ke cikin soyayya saboda su suna taimakawa ɗorewar soyayyar ne.

Da za ka tsaya ka yi lissafin lokacin da ka ɓata ba dare ba rana kana zuwa hira, da dukiyar da ka kashe a dalilin zuwa hirar, to za ka san cewa ba ƙaramin aiki ka yi ba. Kuma kai ka san cewa idan ba a dalilin so ba, babu wanda ya isa yasa ka yin wannan hidimar.

To wannan kenan;

Idan kuma za mu duba ɗayan ɓangaren na Ɗacin So a matsayin wahalar dake cikin soyayya, za ka ga cewa rashin dacewa da samun wanda zai so ka shi ne kan gaba a wannan matakin domin shi ne zai sa ka rinƙa shiga cikin ragowar matakan tsanani da ƙuncin da za ka iya tsintar kanka a ciki.

A sanadiyyar soyayya wani/wata ya shiga cikin ruɗanin da bai ma san ana sonsa ko ba a sonsa ba.

1. Wani ya san ba a sonsa amma yana sa rai da cewar wataran za a so shi. Kuma haka za a yi ta tafiya har a rabu ba tare da an so shin ba.

2. Wani ya kashe dukiya me tarin yawa amma ko sau ɗaya bai taɓa cin ribar abin da ya kashe ba saboda ba a karɓi soyayyar sa ba.

3. Wani kuma rayuwar soyayyar sa mujadala aka dinga yi saboda wadda yake so tanada manema dayawa. Ko da kuwa zai yi fintinkau a ƙarshe, shi kansa yasan babu sauƙi.

4. Wani yana ji yana gani za a bada wadda yake so ga wani amma babu yadda zai yi.

5. Wani yana so ana son shi amma kuma iyayensa ko iyayenta su ce ba za ayi auren ba. Haka zai yi ta fama amma ba za a yi auren ba. Kuma koda kuwa anyi auren, to fa babu kwanciyar hankali.

6. Wani kuma ƙarancin shekaru ko ƙarancin lokaci ko rashin ko rashin sana'a ko aikin yi ne yake jefa shi cikin shan wuya a soyayya, yayin da wani kuma an rena arzikinsa ne ko asalin sa shi yake haifar masa da wahalhalun soyayyar sa.

Da akwai kuma waɗanda wahalar tasu ta zarce na waɗannan.

7. Wani ya ci dukan tsiya akan Soyayya.

8. Wani an ɗaure shi.

9. Wani an yi masa sharri iri iri.

10. Wani an yi masa barazana da lafiyar sa da rayuwar sa.

11. Wani ma ya rasa rayuwar sa akan soyayya.

12. Kai, na ga wanda aka ɗaure shi tsawon watanni sai bayan an yi auren yarinyar da yake so sannan aka sako shi, amma a cikin ikon Allah sai da ta zama matarsa bayan ta yi auren ta fito da 'ya'ya biyu.

Alhamdu lillah.

Kaɗan kenan daga cikin abin da na za ƙulo na irin wahalhalun da ke cikin soyayya.

A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun LitininLaraba, da Juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user