Monday 16 January 2023

Dalilan Da Yasa Mutane Masu Basira Suka Fi Nutsuwa A Ko'ina

Tura Wannan Zuwa

Idan za ka iya warware matsalar, to mene ne dalilin tayar da hankalinka?


Idan ba za ka iya warware matsalar ba, to ina amfanin tayar da hankalinka?


Jama'a idan kuka yi nazari, za ku ga cewa tayar da hankali ba shi da amfani a kusan kowani lokaci.


Mutane Masu Basira
Hoto: Betterup

MarubuciBello Galadanchi


Ga misalai:


1. Akwai jarrabawa mai matuƙar muhimmanci dake tafe kuma ka damu. Idan ka tayar da hankalinka, ba za ka iya yin bitar karatunka ba yadda ya kamata. Sakamakon haka, sai ka gagara taɓuka abun arziki a jarrabawar. 


2. Ɗan fashi ya tare ka, kuma ka tayar da hankalinka. Hakan zai iya fusatar da shi har ta kai ga yi maka illa. Ka ga daga murhu ka faɗa rijiya. Allah Ya kiyaye. 


3. Kai ne shugaban ma'aikata a wajen aikinka, inda kuka samu kanku a cikin wata matsala, ko ƙarancin lokaci. Wannan dama ce da ya kamata ka harzuƙa mabiyan ka, ka ba su ƙarfin gwiwa, ka nuna shugabanci don ku samu ku kammala abin da Allah ya sawwaƙe. Idan ka yi hakan, akwai yiwuwar za ku ma iya warware matsalar baki ɗaya. Idan kuwa ka tayar da hankalinka, to za ka rage wa mabiyanka ƙarfin gwiwa. Sakamakon haka, ba za ku yi aikin yadda ya kamata ba. 


A ƙarshe, duk lokacin da ka tayar da hankalinka, to ƙwaƙwalwarka na samun ƙalubale wajen tunanin hanyoyin warware matsalar da neman mafita. Saboda haka mu kwantar da hankulanmu, mu yi addu’a. 


Allah yana nan a kowani hali.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user