Tuesday 24 January 2023

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (49) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

8. CANJA ABOKAI


Maganar gaskiya sauya abokai wurin mai neman nasara ba mafita ba ne, sai dai maganar da ake yi ita ce "Ƙarin abokai" su wa ka ƙara? Don me ka ƙara su? Abokanka da ka taso tare da su a kan 'yan uwantaka da taimakekeniya har yanzu suna nan da wannan matsayin a wurinka ba ragi ba ƙari, waɗanda kuma sana'a ko son ci-gaba a rayuwa suka kawo maka su ma tanan za ku haɗu, shin waɗanda ka samu daga bayan nan sun zo ne su ƙara maka ci-gaba a kan hanyarka ta zama mai sukuni ko sun zo ne a dalilin sanayya a baya? Idan dai arziki suka zo ci to su biyo bayan abokanka na yaranta, su daina shige maka.


Maganar Gaskiya
Hoto: Quantum Workplace


MarubuciBaban Manar Alkasim


Idan kuwa abokan sana'a ne to ya matsayinsu? Waɗanda za ka ƙaru da su ne ta fuskar aiki ko ƙara maka sanin makama za su yi? Duk wanda zai taimaka wurin haɓakar arzikinka shi ne yake sahun farko a rayuwarka ta fuskar kasuwanci da sana'a, wanda zai taimaka maka ta fuskar rayuwa kuwa to ya biyo ta wurin abokanka na kusa waɗanda ka yarda da abokantakansu, ba su da baƙin ciki da kowa, kuma ba mahandama ba ne, idan ka sami wannan ginshiƙi ba shakka ka ajiye ɗan-ba na gina kanka a rayuwa, wani mutumin abokansa ke wargaza shi, su suke ɓata sunansa a wurin jama'a, musamman abokan da aka same su daga baya. Kar ka yarda wasu mutane 'yan ƙalilan su shiga tsakaninka da sauran jama'a. 


Ka sami wanda ka amince da shi wanda za ka riƙa tuntuɓarsa ta fuskar zumuntarka, wani ta ɓangaren abokanka, wani ta fuskar addini musamman halas da haram, wani kuma ta sashin dokokin ƙasa, don kar tsantsi ya kwashi ƙafarka ka wuce wani wurin, idan dai za ka samu ƙumbar susa to abokai kala-kala za ka gani. Kai dai kar ka yarda ka watsar da waɗanda suka so ka, suke tare da kai tun ba ka da ko sisi, irin waɗannan tserewa za su yi su barka, don gujewa da mutuncinsu. Kar ka ba su wannan damar, kamo su don su ci gaba da taimaka maka zuwa ga nasara, 'yan bambaɗanci da gulmace-gulmace kuwa ja musu layi, matso da na ƙwarai waɗanda za su riƙa shiryar da kai.


9. ME KAKE BUƘATA?


Yi tunani sosai cikin tsanaki, me kake buƙata: Nasara, dukiya, jajircewa... Wannan aikin ya fi ƙarfinka kai kaɗai, yanzu wa ya taɓa shiga inda kake ƙoƙarin shiga kuma ya ci nasara? Yaushe ya fara? Wasu hanyoyi ya bi? Yi ƙoƙari ka san irin ƙalubalen da ya samu a tsakiyar tafiyar da kuma hanyoyin da ya bi wurin warware su, saka a zuciyarka cewa kai ma fa zuwa nan da wasu 'yan lokuta kaɗan za ka kamo shi. Kar ka damu da manyan matsalolin da za ka hango, ita faɗuwa ba matsala ba ce matuƙar za a iya tashi a ƙara zage himma, ko ba komai an sami wani sabon ilimin da zai hana faɗuwa nan gaba, babbar matsala ita ce idan an faɗi a shantake, a yi tsammanin komai ya ƙare kenan.


10. Banda koke-koke: Wani al'adarsa kenan, ko rowa yake son yi maka sai ya yi ta zargin sana'arsa yana kushewa tare da faɗin munanan kalamai don dai ka san cewa ba ya samun komai, banda zargin sana'a ko zargin abokan sana'a, wani idan bai sami abin da yake so ba to a kan sana'ar zai ƙare, ko ya abka wa abokan sana'arsa ko ya ce wane ya yi min kaza, ba don shi ba da yanzu na sami kaza, ko wallahi ina son yin abu kaza amma su wane nake tunani, bayan abin da zai samu nasa ne shi kaɗai, kawai idan ya gaza ya yi ƙoƙarin gano abin da ya hana shi sannan ya fuskanci matsalolinsa zuwa ƙarshe, me ya sa ya gaza? Ya zai yi maganin hakan anan gaba?


11. Banda gaggawa: Galibin waɗanda suka ci nasara a rayuwarsu ba su yi gaggawa ba, bi a sannu, yi ƙoƙari ka san mutane a fannin da za ka shiga, babban kuskure shi ne ka nemi su ba ka kuɗi, dage kawai ka san hanyar da suka tara kai ma ka bi, idan ka ce kai yanzu-yanzu kake son abu za ka sha wahala, na zauna da kala-kalan mutane da dama, wasu ina tare da su ne ba su ma yarda ina cikinsu ba, sun nuna ta fuskoki daban-daban, amma ni na san me nake ƙaruwa da su don haka na nuna ban san me suke yi ba, da haka na gama sakandare na yi dufuloma har na iso matsayin da nake ciki, ban karɓar kaye a cikin sauƙi, kuma da wahala ka ga ban kai inda nake so ba, ba abin da ya fi kyakkyawar niyya, naciya da haƙuri amfani, malam Jafar Allah ya jiƙansa ya nuna cewa nasara ba ta samuwa idan ba haƙuri.


12. Banda ɗaukar zugi: Da yawa wasu abin da yake raba su da ma'aikatansu kenan, kullum ka riƙa zaton wane zai cutar da kai, ka riƙa sakawa ana jiyo maka me yake cewa? Na zauna da wanda har waya ake yin recording ake kai masa, wai ga abin da wani ke faɗi a kansa, kai har taro yakan haɗa ya sa a ɗauka a waya a kai masa don dai ya ji me ma'aikatansa ke faɗi a kansa, sai ya zamo bai da natsuwa da duk wanda yake tare da shi, bai yarda da kowa ba, ga kamfaninsa babban kamfani, a ƙarshe dai ɗan ƙaramin abu ma sai dai ya yi da kansa. 


Wannan ya hana kamfanin bunƙasa, kullum yau a jiya, dole mutum ya yi maganin irin wannan cutar dake harɗe shi ta hana shi zama babban mai sukuni, wani sa'in waiwayen ƙaramin abu zai sa a wuce babba ba tare da an ganshi ba.


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (50) Cikin Sauki


Saki jiki, sami ma'aikatan da ka yarda da su, riƙa bincikawa idan suna yin aikinsu kamar yadda ya dace, kar ka yi sakaci da kuskure komai kasawarsa sanya a gyara ba tare da masifa ba, a ja wa mai kuskure kunne don ya kiyaye gaba, rage wa kanka aiki ta wurin samun waɗanda ya dace su tsaya a kan wasu ayyukan, maida hankali kan ƙololuwar sana'ar, yi ƙoƙari shugabannin kowani sashe su riƙa ganinka a kullum ko a lokutan da suka dace don jin inda aka tsaya da inda za a tashi, duk wata matsala na da yadda ake warware ta, don haka ba ka da matsala da kowa a kan abin da za a iya gyarawa, wanda ya ɓaci gaba ɗaya musamman wanda yake da alaƙa da yarda ko aminci to bi a hankali har ka rabu da shi, musamman idan ya zamo wanda ba zai gyaru ba.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user