Friday 10 March 2023

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (50) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa

12. Jarraba ka gani: Duk abin da ba ka taɓa gwadawa ba ba za ka san cewa yana da riba ko bai da shi ba, idan kana da abubuwa da yawa da kake son zama ko kake son yi zaɓi mai sauƙin cikinsu wanda kake ganin za a iya samun abin da ake so a cikinsa, kafin ka fara, dubi waɗanda suka yi nisa a cikinsa ka ɗan tambaye su, idan kuma bayani ba zai yi ba to zauna kusa da su ka koya kafin ka shiga. Wannan idan kana son cin nasara kenan, amma kawai ka dubi abu da ido ka ce ba za ka iya ba matakin farko kenan na karya kai, da wahala ka zama abin da kake so.


Mutane kala-kala ne
Hoto: Forbes


MarubuciBaban Manar Alkasim


13. Me ka fara?: Mu ba mu da wannan lissafin, ba kamar Turawa ba ne da idan mutum ya so yin abu ya gaza sai ya fara binciken kansa me ya hana shi kaiwa? Idan ya samu sai ya yi maganinsa kawai, kai ma idan ka gano shi sai ka yi ƙoƙarin gyara shi ba wai ka ce tsarin ya rushe gaba ɗaya sai dai wani ba. Idan ka taɓa yin shago a jikin gidanka, wanda 'yan uwanka suka karya ka da bashi, kar ka ce ka kulle shagon shikenan, bar shi kowa ya ga lalacewarsa, sai ka riƙa gaya musu dalilin karyewarka, ɗan ba su sarari na ɗan wani lokaci, sai ka dawo da ƙarfi, a wannan lokacin ba bashi, don ba za a sake karyaka ba, idan ka yi haka za ka iya tsayuwa da ƙafafunka.


Wanda ya so shiga sana'ar kanikanci, ga shi ya iya, har ya buɗe nasa amma mutane ba sa zuwa, zai yi wahala a ce abin hawansu ne ya daina lalacewa, ya binciki ɗayan abubuwa guda uku: Anya lokacin da yake koyon aiki ya gwanance kuwa? Don dole waɗanda suka saba da shi su biyo shi; Anya ya sami wuri mai kyau kuwa? Anya mu'amalarsa da mutane tana da kyau kuwa? Kar ya ce ba a samun komai zai canja wata, wasu na samu ai, shi ma ƙila abin da ya gani kenan, sai ya binciki abubuwan nan 3 kawai ya gyara.


14. Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka: Shakka babu wannan maganar gaskiya ce, mutane da dama an haifo su talakawa ne ba su mutu ba sai da suka yi arziki, wasu an haifo su a gidan kuɗi ne, kuma mahaifin ya mutu ya bar su da gado mai tarin yawa, sai dai kuma Allah bai yi musu arziki ba sun koma sahun masu ƙwatar rayukansu da ƙyar, haka rayuwa take a kowane lokaci. Yanzu dai tunda ka san inda kake son zuwa sauko da kanka ƙasa, kai me nema ne ba ka san inda za a dace ba, yi ƙoƙari ka shiga fannin da kake so, fara tafiyar tare da su, duk da cewa arziki ake nema yanzu ba lokacin tara shi ba ne, matakin farko na sanayya ne, akan yi ƙoƙarin a saba da mai iyo ne tun rani.


Manyan mutane ba sa son ka fito musu da maitarka ta son kuɗinsu ko nuna cewa kai fa kanka ya waye ɓaro-ɓaro, yanzu sai su yi ƙoƙarin rabuwa da kai, babban abin da za ka yi shi ne ƙanƙan da kai, babu matsala idan ka yi barci amma da ido ɗaya, koyi duk abin da kake buƙata, saba da irin mutanen da suka amfana, banda ƙarya banda ha'inci, banda nuna kwaɗayi a fili, da sannu za ka ga kai ake turawa wasu harkokin, kar ka damu da cewa ba ka samun komai tunda manufarka kai ma ta ka tura wasu ne anan gaba, ba wai a yi ta tura ka ana biyan ka ba, koyi aikin sosai.


15. Mutane kala-kala ne: Wani za ka taras a rayuwarsa ba abin da ya ƙi jini irin ya ga ma'aikacinsa ba ya neman nasa na kansa, yakan yi iya ƙoƙarin sa ya ga duk ma'aikatansa suna cikin wadata, shi yake tambayarsu abubuwan da suke yi, idan ba su yi masa ba ya ɗora su a kan hanya, wani kuwa ba ruwansa da kowa, abin da ya sani aikinsa kawai, mutum shi yasan yadda zai fidda kansa, wani bai son ka nuna kana son abin hannunsa, wani kuma ba abin da yake so kamar ka nuna masa kana da buƙatar wani abu daga gare shi, kowanne akwai, lura da wanda kake tare da shi.


Na zauna da wanda bai iya ba ma'aikacinsa abin hannunsa, amma bai damu da abin da za ka samu ta ma'aikatarsa ba, ko nawa ne ma kuwa, shi da kansa zai gaya maka cewa ka yi aiki idan kana son kuɗi, bai da bakin ciki kokaɗan. Irin waɗannan idan ka same su sai ka zage dantse ka yi aiki tuƙuru don tara abin da kake so, idan kuwa ka zauna da mutanen da ba su son ci-gaban kowa to ka ɓoye wayonka ka yi karatunka ka ƙara gaba, ba matsala ba ne ka zauna da wanda kake ƙaruwa da shi ta fuskar gina kai, don dama abin da ya kawo ka kenan.


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (51) Cikin Sauki


Sai dai duk halin mutum ka sani cewa ba za ka iya kaɗa fuka-fukanka ka tashi sama ba sai ka bar ƙarƙashinsa ka sami gashin kanka, mutumin da ya yi ƙoƙarin tashi bayan yana ƙarƙashin wani ya san cewa ƙume kansa zai yi ya dawo ya durƙushe, ga zafin ƙume kai ga na faɗuwa, abubuwan da ke tattare da yunƙurin tashi a ƙasan wani sun haɗa da:-


1. Ƙoƙarin shiga gaban maigida.


2. Zargin sace kuɗinsa don gina kai.


3. Ƙwashe masa abokan hulɗa.


4. Ja da shi a al'amuran rayuwa.


5. Rashin aminci ta kowace fuska, da sauransu.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user