Thursday 29 December 2022

Ingantattun Shawarwari 10 Ga Masu Son Yin Nasara A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

1. KAR KU TAƁA MIƘA WUYA A KOWANE HALI: Idan kuka yarda da kanku, to sauran jama’a ma za su yarda da ku. Idan kuka ƙi miƙa wuya a yaƙin zaman duniya, to sauran jama’a ma ba za su taɓa daina bin ku ba. Mutum ɗaya ba zai taɓa yin abubuwan da mutane da yawa za su iya ba, saboda haka ku haɗa kai da sauran jama’a, ku ba su dama su ma su kwatanta yin abin arziki a duniya. 


Shawarwari 10 da za su inganta rayuwarku 
Hoto: The Down Reh


MarubuciBello Galadanchi


2. KAR KU YI AMFANI DA TSOFAFFIN AƘIDU DA RA’AYOYI: Kuna da ‘yanci da damar laƙantar sababbin ra’ayoyi da aƙidu. Babu wanda ya isa ya saka ku dole ku bi ra’ayin da ba ku amince da shi ba. Ko maciji na canza fata, saboda haka kuma matasa nauyi ya hau kawunanku wajen canza aƙidun siyasa, shugabanci, ilimi da sauran ɓangarorin rayuwa. Kar ku zama tumaki, waɗanda ke bin kowa da komai ido rufe. 


3. KAR KU JIRA SAI AN BA KU – KU NEMA, KU TAMBAYA: Ku nemi abin da kuke buƙata komai ƙanƙantar shi. Ina so ku sani cewa duniyar nan ba wajen kiwon sarakuna ba ne. Idan kuna son wani abu, ku tambaya, kuma ku ba da hujjoji masu ƙwari da suka sa kuko so. Idan ba ku samu ba, kar ku yi fushi, kar ku miƙa wuya. Ku ƙara tambaya. 


4. KU TAIMAKI MASU ƘARAMIN ƘARFI DA MARASA GALIHU: Kowa na da baiwa. Baiwa mafi amfani a duniyar nan shi ne wanda ya taimaki jama’a wajen kawo ci-gaba. Wacce baiwa kuke da shi, kuma ta yaya za ku yi amfani da ita wajen taimaka wa jama’a? Kar ku zama ‘yan jari hujja. Ba komai ba ne ya cancanci riba, amma duk wani aikin alkhairi na da sakamako mai kyau ta hanyoyi iri-iri, ko yau, ko gobe. 


Tausayi na da matuƙar muhimmanci a rayuwar bil adama. 


5. FARIN CIKINKU DA KWANCIYAR HANKALI NA KAN KAFAƊUNKU: Kar ku bari wasu su ɓata muku rai. Kuna da alhakin yanke shawara idan za ku bari abu ya ɓata muku rai, ko kuma za ku nutsu ne domin fahimtar daliliai da neman mafita. 


Ku tuna cewa duk wanda ya yi nasarar fusatar da ku ya yi nasara, kuma ya samu iko akan ku. Faɗa, tashin hakali, cece-kuce, gardama da zafin kai ba za su warware matsala ba. Duk zafi, duk wuya, ku kwantar da hankulanku ku yi tunanin mafita. 


Yawaita ƙorafi da nuna fushi na ƙalubalantar manufofinku na rayuwa. 


6. KU KASANCE ABIN SHA’AWA A KO YAUSHE: Duk abin da za ku faɗa, duk abin da za ku yi, duk inda kuke, ko da wa kuke, ko me kuke yi, ku kasance abin marmari da misali. Ku faɗi alheri, ku saka tufafi masu kyau da tsafta, ku yi murmushi kuma ku saurari jama’a idan suna hira da ku. 


7. KU FI KOWA AIKI TUƘURU BA TARE DA NEMAN IHISANI BA: Ku sadaukar da kawunanku da lokutan ku ga ayyukan da kuke sha’awa. Kar ku yi kuskure. Kar ku bari abubuwan da suke cikin zuciyoyinku su shafi ayyukanku. Ko albashinku ɗan kaɗan ne, ku tuna cewa ƙwarewa da ilimin da za ku samu a wajen aikin ya fi kuɗi daraja. Jama’a su sanku a matsayin mutane masu zuciya, aiki tuƙuru, kuma waɗanda za’a iya dogara akan su ko yaushe. Sakamako na tafe, ko yau, ko gobe. 


8. KU GIRMAMA DUK WANDA KUKA HAƊU DA SHI: Ku watsar da nuna banbancin al’ada, addini, aƙida, yanki da arziki. Idan kuka yi tunani, za ku fahimci cewa mafi yawancin jama’a ba su zaɓi halin da suke ciki ba. Saboda haka ku yi murmushi, ku girmama su, sannan ku kasance masu sauƙin kai da kirki. Ba za ku taɓa sanin ko da wa za ku haɗu ba. 


9. KU RIGA KOWA FARKAWA DAGA BACCI: Ku riga rana tashi daga bacci. Masu yin haka sun fi kowa cimma burinsu na rayuwa, kuma wannan lokaci ya fi kowanne daraja da albarka. Idan karatu ne ba ku gane ba, to wannan lokacin shi ne ya fi cancanta wajen ƙarin ilimi.  


10. KU CANZA KASASHEN KU: Idan kasashen ku na fuskantar ƙalubale, kar ku zauna ku yi ta ƙorafi. Ku samu fanni ɗaya da kuke gani za ku iya gyarawa, ku fara. ‘Ya’yan ku, jikokinku da tattaɓa kunnen ku ba su da wajen zuwa. Dole su zauna a wannan ƙasa, komai zafi, komai wuya. Saboda haka idan kuka fara gyarawa, to kun kafa tushen ci-gaba da warware matsalolin da za su saka ‘ya’yanku da jikokinsu su yi matuƙar farin ciki nan gaba. 


Ku tuna cewa duk wani abu mai kyau yana da wahalar samu. Idan kuwa ba ku yi komai, to kune za ku yi da-na-sani.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user