Saturday 24 March 2018

Karanta Wannan Kaji: Na taba yin aure amma yanzu Banda aure Sai dai Niyya - Aina'u Ade Laila

Tura Wannan Zuwa

Sau da yawa wasu kan yi mamakin yadda wasu yaruka daban ke shiga cikin duniyar fina-finan Hausa su yi ta fantamawa suna rawar gaban hantsi.

Wannan ya sa a wannan karon Taurarin Nishadi ya tattauna da wata Bayarabiya da ta ga jiya kuma take ganin yau a duniyar fina-finan domin warware wa mutanen da ke wancan mamakin yadda lamarin yake. Wakiliyarmu, JUMMAI IBRAHIM ta tattauna da jarumar.

A sha karatu lafiya: Ya cikakken sunan jarumar?

Sunana Ainau Ade, ni Bayarabiya ce, amma a nan Kano aka haife ni.

Ya cikakken sunan jarumar?

Sunana Ainau Ade, ni Bayarabiya ce, amma a nan Kano aka haife ni.

Muna so mu ji cikaken tarihin ki da abun da ya jawo ra’ayinki kika shiga harkar fim din Hausa, da wane fim kika fara kuma a wace shekara kika fara?

Ni ai tsohuwar ‘yar fim ce, bai ma kamata ki tambaye ni ra’ayina na shiga fim ba. Wanan tambayar sai dai ki mika ta ga sabbin zuwa. Ta yaya kike hada harkokinki da kula da iyali

A yanzu dai ba ni da aure gaskiya amma lokacin da aka daina ganina a fim ina gidan mijina ne lokacin, don na yi aure ina da yara guda biyu, kuma ai harkar fim ba zai hana ni ‘business’ dina ba, ina da shago kuma ina ba da kaya ga masu siyan daya-daya ko sari.

Wane fim ne cikin finafinanki ya fi burge ki?

Ni fa Yanzu daga na ji an ce ‘action’ sai kawai na ga na fara zaro bayyanai, ban sani ba, ko don abin ya riga ya zame min jiki ne, oho, kuma gaskiya ba ni da wani fim din da ya ban wahala, kuma duk fim din da ba zai burge ni ba ba zan ma karbe shi ba, don haka duk fim din da na yi suna burge ni. Bayan haka za ki ga an ciri wani ‘scene’ ana yawo da shi a waya tsabar ya burge mutane.

Wane ne kuma kika sha wuya wajen daukarsa
Ni duk wani fim da zan yi ba ya ba ni wahala kawai dai in ba a biya ni hakkina ba ne nake jin ba dadi

Shin Ko kema kina da sha’awar ‘directing’ ko ‘producing’ fim na kanki?

Ba ni da sha’awar ‘directing’ fim, don wannan aikin maza ne, amma ina da finafinai da yawa nawa da na yi ‘producing’ a karkashin kamfanina, don ko wannan mai dan waken da ake ta yawo da shi a waya ni na yi ‘producing’ dinsa da kaina

Yanzu yaushe kike da niyyara kara wani auren?

Shi aure abu ne na Allah, duk lokacin da Allah ya kawo shi ko ka yi niyya ko ba ka yi niyya ba za ka yi shi ne, amma yandu ban da tsayaye gaskiya

Ko za ki fada mana finafinai nawa kika yi ‘producing’ a karkashin kamfaninki?

A halin yandu na yi ‘producing’ finafinai shida a karkashin kamfanina

matsayinki ta tsohuwar jaruma, ta yaya kike kallon yanayin aikin da ake yi yanzu a ‘industry’?

Aiki kam ai ko dan da ka haifa ma dole za ka ga yana girma, to haka ‘industry’ ma yanzu gaskiya ya girma Abubuwa sun canza. Yanzu ana yin ayyuka masu kyau daidai da zamani.

Wace shawara za ki ba wa masu son shigowa fim a yanzu da kuma wadanda ba su dade da shigowa ba.

Shawarar da zan ba masu tasowa na yanzu shi ne su bi na gaba da su, su girmama su, duk da dai wasunsu ba su dauki abun sana’a ba kamar yadda muka dauka, su dai sun dau abin kamar a yi wasa ne a zama ‘famous’, kuma in har mutum ya samu ‘fame’ a fim ai sai a dauki abun da mahimmanci.

Rokona na karshe dan Allah mu natsu mu rike sana’armu bisa gaskiya da amana da kamun kai.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Fim Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: