Tuesday 30 July 2019

KARANTA LABARIN MALAM DUDU MAI-GANI-HAR-HANJI

Tura Wannan Zuwa Ga
An yi wani mutum a wani gari wanda ake kira Dudu, mai-gani-har-hanji. Ba komai ya sa ake kiransa da wannan suna ba sai don dabi'arsa ta nazarin taurari.

MALAM DUDU MAI-GANI-HAR-HANJI


MarubuciBukar Mada

+2348021218337

Kullum ba shi da wata al'ada sai idan yamma ta yi, ya tada kai sama ya yi ta duban taurari yana fada wa mutane abin da zai faru shekaru masu zuwa.

Wata rana da yamma, ya fito daga gidansa za shi tafi wani wuri, sai ya daga kansa sama yana nazarin taurari yana tafiya. A cikin nazarin nasa wai har ya gano ranar da duniya za ta tashi. Yana cikin tafiya, kansa a sama, yana kidayar taurari da hannu, ba zato ba tsammani sai ya fada cikin wani katon rami mai cike da kwatami. Ya yi ta bundum-bundum cikin kwata yana kokarin fitowa, amma ya kasa.

Da mutane suka ji kururuwa daga cikin rami sai suka sheko da gudu, suna zuwa sai suka ga ashe Malam Dudu ne ke iyo cikin kwata. Suka kama masa ya fito, duk ya yi tsamo-tsamo da kwata, mutane sai toshe hancinsu suke yi saboda doyin da ya cika wurin, kamar ana yasar tsohuwar salga.

Wani dattijo daga cikinsu ya dubi Malam Dudu ya ce, "Yanzu ina amfanin dubanka? Kai da kake duba abin da zai faru shekaru da yawa masu zuwa, amma ka kasa duba abin da zai faru gare ka cikin wannan lokaci?"

Darasin da labarin yake koyarwa.

FARA DUBA MATSALOLIN DA KE KEWAYE DA KAI, KAFIN KA HANGO MATSALOLIN DA KE NESA.

LABARAI MASU ALAKA:


DARIYA DOLE LABARIN WANI YARO DA MAHAIFINSA AKAN JARABAWAR JAMB

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user