Tuesday 30 July 2019

KARANTA SUNNONIN AZUMI DA LADUBBAN SA

Tura Wannan Zuwa Ga
Azumi yana da sunnoni da mustahabbai, yana daga cikin su:

1. Sahur: shi mustahabbi ne a gamuwar malamai, wanda bai yi shi ba ba shi da lafi sai dai wanda ya yi sahur ya fi shi yawan lada. Domin Annabi (S.A.W) ya yi umarni da a yi shi.

عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "سَحَّرُوا فَإِنَّ فِي السُّحُورِ بَرَكَةٌ." (رواه البخارى ومسلم).

An karbo daga Anas dan Malik (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku yi sahur hakika, akwai albarka a cikin yin sahur.” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).


Kafin shan ruwa (kafin buɗa baki)


2. Gaggauta yin buda baki da jinkirta sahur.

لِقَوْلِ النِّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "لاَ يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ مَا عَجَّلُوا الْفِطْرَ وَأَخّرُوا السُّحُورَ." (رواه البخارى ومسلم)

Don fadin Annabi (S.A.W) da ya ce: “Mutane ba za su gushe suna cikin alheri ba, muddin suna gaggauta buda baki kuma suna jinkirta sahur.” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).

3. Yin buda baki da dabino:

لِقَوْلِهِ عَلَيْهِ الصَّلاَةُ وَالسَّلاَمُ: "إِذَا أَفْطَرَ أَحَدُكُمْ فَلْيَفْطِرُ عَلَى تَمْرٍ فَإِنَّهُ بَرَكَةً فَإِنْ لَمْ يَجِدْ تَمْرًا فَالْمَاءُ فَإِنَّهُ طَهُورٌ." (رواه أبو داود والترمذى)

Don fadin Manzon Allah (S.A.W) da ya ce: “Idan dayanku zai yi buda baki ya yi buda baki da dabino, idan bai samu dabino ba, ya yi da ruwa, don tsarki ne ko tsarkakakke ne.” (Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito).

4. Addu’a yayin buda baki:

عَنْ عَبْدِ اللهِ ابْنِ عُمَرُو بْنِ الْعَاص: أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "إِنَّ لِلصَّائِمِ عِنْدَ فِطْرِهِ دَعَوَةٌ مَا تُرَد." (رواه ابن ماجه).

An karbo daga Abdullahi dan Amru dan As (R.A) ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Hakika, mai Azumi in ya yi addu’a lokacin buda baki ba a mayar da addu’ar (ana amsawa).” (Dan Maja ne ya rawaito).

Annabi (S.A.W) ya kasance idan zai yi buda baki yana cewa:

"اللَّهُمَّ لَكَ صُمْنَا وَعَلَى رِزْقِكَ أَفْطَرْنَا فَتَقَبَّلْ مِنَّا إِنَّكَ أَنْتَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ" (أبو داود)

Ma’ana: “Ya Ubangiji dominKa muka yi Azumi, kuma da arzikinKa muke buda baki, ka karba daga gare mu, lallai Kai mai ji ne Masani.” (Abu Dawuda ne ya rawaito).

Da wasu addu'o'in da dama.

5. Asuwaki: Ana so ga mai Azumi ya yi asuwaki  lokacin azuminsa.

Saboda Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yin asuwaki lokacin da yake Azumi.
Hakanan yana daga ladubban Azumi a nisanci shaidar zur, karya, giba, rada, tashin hankali, da dai sauran ayyukan sabo.

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA RUKUNAN AZUMI

KARANTA RABE-RABEN AZUMI

KARANTA FALALAR AZUMIN RAMADAN

KARANTA MA'ANAR AZUMI A TAKAICE CIKIN ADDININ MUSULINCI

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user