Saturday 21 September 2019

DARIYA DOLE: KARANTA KAYATACCIYAR HIKAYAR SHEHU JAHA "KARKA GASKATA SHI"

Tura Wannan Zuwa
Wata rana Shehu yaje kasuwa, sai ya hadu da wani mutum shi kuma ya siyo tangaram cike da buhu.


Hikayar Shehu Jaha


Sai yace ma shehu, ka daukar man kayannan nawa ka kaiman gida, ni kuma zan sanar dakai wasu
abubuwa guda ukku da zasu amfane ka har karshen rayuwarka, shehu yace ya yarda.

Suna cikin tafiya
har sunyi kashi daya cikin ukku na tafiyarsu, sai
shehu yace ka fada min yanzu?

Sai mutumin yace, na daya duk wanda yace maka da ƙoshi gara
yunwa karka gaskatashi.

Shehu yace to na biyu
fa?

Sai yace duk wanda yace maka da tafiya kan abin hawa gara tafiya a ƙasa karka gaskatashi.

Bayan sun isa kofar gidan mutumin sai shehu yace ka
fada min gudan.

Sai yace duk wanda yace zan biyaka ladan daukar kayan nan karka gaskata shi,

LABARAI MASU ALAKA:

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WATA MARAINIYA DA DAN SARKI

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WATA MATA DA KWARTAYE BIYU

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN

Sai shehu ya daga buhun tangaram ya rabkashi da kasa.

Sai yace duk wanda yace akwai sauran
tangaram mai rai a cikin buhun nan karka gaskatashi!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user