Saturday 21 September 2019

KARANTA MUHIMMIYAR SANARWA DAGA RUNDINAR SOJIN NIGERIA

Tura Wannan Zuwa Ga
Rundinar sojin Nigeria Operation Lafiya Dole tana sanar da al'umma cewa wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba (NGOs) da suke aiki a yankin arewa masu gabashin Nigeria suna cin amanar yakin da ake da 'yan ta'addan Boko Haram.

Operation Lafiya Dole


Marubuci: Datti Assalafy

Rundinar sojin tace akwai wata kungiyar NGO da take aiki a jihar Borno mai suna Action Against Hunger (AAH) tana taimakawa 'yan ta'addan Boko Haram da abinci da magunguna duk da gargadin da kwamandan rundinar Operation Lafiya Dole yayi mata na ta dakata da tallafawa Boko Haram amma sunki.

A takaice dai wannan ya sanarwan ya fito ne jiya Alhamis 19-9-2019 daga Kanar Ado Isah mataimakin baban jami'in hulda da jama'a na rundinar Operation Lafiya Dole.

Kwana hudu ko uku da suka gabata wani mummunan al'amari ya faru a garin Gajiram, duk da an boye labarin, maciya amana sun jibe magunguna a garin da kayan abinci, kawai sai 'yan ta'adda suka shiga garin, har ma suka kwana, sun kwashe maganin da abinci suka tafi jeji abinsu, ai an san wadanda suka jibge maganin, wani mataki aka dauka a kansu?

Yafi shekara 3 muna bayyana girman cin amanar tsaron Nigeria da wadannan kungiyoyin sharri suke yi a jihar Borno, shekaran da akaci amanata 2017 na rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Maigirma shugaban kasa, gwamnonin Arewa, Mai alfarma Sarkin Musulmai da Manyan Sarakunan Musulunci, Manyan Malamai, 'yan majalisar Dattawa da na Dattijai, kungiyoyin Dattawa da na Matasan Arewa.

A cikin waskiyar na wallafa dogon rubutu nayi cikakken bayani akan yadda kungiyoyin sharrin suke taimakon 'yan ta'addan Boko Haram, nace ma wadanda na rubuta wasikar su umarci amintattunsu masana tsaro su gudanar da binciken sirri akan ayyukan NGOs din, a daidai lokacin da na wallafa rubutun hankalin wakilan NGOs yayi mummunan tashi, wani wakilinsu tsinannen Malami Ustazun karya maciyin amanar musulunci da Musulmai daga jihar Kano wanda nake zargin 'dan Luwadi ne, yazo ya kalubalanceni, aka hada baki dashi aka batar dani daga doron duniya a daidai wannan lokacin.

Na rantse da girman Allah babu abinda yake haifar da mummunan cikas a yaki da Boko Haram sama da wadannan kungiyoyin sharri saboda kawai neman kudi, amma wani mataki aka dauka akansu?

Watannin baya rundinar sojin Nigeria ta gano kungiyar UNICEF tana taimakon Boko Haram aka dakatar da su, amma a tsakanin awanni 24 manyan wakilansu na duniya suka zafafa kira ga mahukuntan Nigeria aka tilasta rundinar sojin Nigeria ta janye dakatarwan, suka cigaba da aikinsu na cin amana.

Duniya taji labarin a lokacin da tsohon Ministan Tsaron Nigeria Malam Mansur Dan Ali yayi magana a BBC Hausa yana fadawa duniya cewa kungiyoyin NGOs da suka mamaye jihar Borno suna taimakon Boko Haram saboda basa so a kawo karshen ta'addancin saboda sun mayar dashi babbar hanyar neman kudi da kasuwanci.

DUBA WADANNAN:

KARANTA BAYANI AKAN AIKIN MAMBILA HYDROPOWER PLANT DAKE JIHAR TARABA

KARANTA DALILIN DA YASA GWAMNATIN NIGERIA TA HANA SHIGO DA SHINKAFA TA KAN IYAKOKIN KASAR

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa??

Wace kasa ne a duniya zata yarda da irin cin amanar da ake yiwa tsaron Nigeria?

Matakin da muke tunanin ya kamata rundinar sojin Nigeria ta dauka shine dakatar da duk wata kungiyar NGO da aka kama tana taimakon kungiyar Boko Haram ta kowace fuska.

Yaa Allah Ka mana maganin abinda yafi karfin mu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode









TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user