Saturday 21 September 2019

KARANTA DALILIN DA YASA GWAMNATIN NIGERIA TA HANA SHIGO DA SHINKAFA TA KAN IYAKOKIN KASAR

Tura Wannan Zuwa
Sumogal din shinkafa da ake yi da babura ko fasakwaurinta daga kan iyakokin Nijeriya zuwa cikin gida Haramun, kamar yadda hukumar dake kula da wannan janibi ta sanar. Mutane da yawa na sukar wannan lamari, watakila bisa son rai ko kuma bisa jahilci.

fasakwaurinta daga kan iyakokin Nijeriya 


Marubuci: Yasir Ramadan Gwale

Hakikanin gaskiya yana da kyau mutane su fahimci cewar, manufofin wannan gwamnatin inganta tare da habakar harkar noma musamman na shinkafa, domin manoman shinkafa na gida su samu arziki, 'yan Najeriya su ciyar da 'yan Najeriya da shinkafar da aka noma a cikin gida.

Wannan na daga cikin manufofin Gwamnatin Buhari kan bunkasa harkokin noma a Najeriya. Wannan ya sanya hukumar kwastan ta kasa sanya dokoki da ka'idoji kan batun shigo da shinkafa zuwa Najeriya daga kasashen waje.

Hukumar kwastan, tace yin sumoga ko fasakwaurin shinkafa ta kan iyakoki haramun ne, saboda hujjojin da shugaban hukumar Hameed Ali ya bayar, domin kudin da gwamnati ya kamata ta samu na harkar futo, anyi mata asararsu, sannan an shigo da abinda ake zargi yana dauke da guba.

Na farko ita wannan shinkafa da ake shigo da ita Najeriya ta barauniyar hanya, dauke take da guba, domin kafin isowarta Najeriya, an zuba mata sinadarai iri iri wanda zasu hanata rubewa ko lalacewa, saboda warin ruwan teku da ruma da kuma kumewa, wanda binciken hukumar kwastan ya tabbatar da cewar wannan shinkafa mai dauke da wadannan sinadarai tana cutarwa ta hanyar sanyawa mutane ciwon kansa.

Ciwon kansa ko sankara, ba ciwo bane da ake dauka nan take, watakila sai bayan wasu shekaru ciwon ke bayyana a jikin masu dauke da shi. Da wannan dalili da ma wasu, hukumar kwastan tace, duk wanda zai yi kasuwancin shigo da shinkafar waje zuwa Najeriya, to, ya shigo da ita ta hanayoyin da suka dace, domin a yi mata gwaje gwaje a tabbatar da inganci da kuma lafiyarta. To meye laifin hakan?

Mu 'yan Najeriya muna da al'adar rashin girmama duk abinda muke da shi. Tayaya manomanmu zasu samu cigaba a harkar noman shinkafa alhali muna kaucewa sayan 'yar gida muna cin wadda ake shigo da ita daga waje wadda ke dauke da sinadaran da ka iya illata jiki?

Ba daidai bane, mutane su dinga wasa da rayuwarsu, akan dan abinda za a basu in sun yi sumoga din shinkafa daga kan iyakokin da aka rufe zuwa gida Najeriya. Gwamnati dole ta karewa al'umma jini da dukiya da kuma mutuncinsu.

Me yasa masu kasuwancin shinkafa suke son lallai sai dai su shigo da ita ta barauniyar hanya, ta hanyar yin sumoga ko fasakwaurinta? Alhali Kuwa akwai yadda zasu iya shigo da ita a bisa tanade tanaden hukuma, ta anyar mfania da gabar tekun ad gwamnati ta ware domin yin harkar futo.

Yana da kyau 'yan Najeriya su yiwa kansu tambayar me yasa ake sumogal din shinkafa indai sahihiya ce, kuma halastaccen kasuwanci mutane suke yi na sayar da shinkafar? Indai sun tabbatar shinkafar bata dauke da guba, me yasa ake tsoron shigo da ita ta gabar teku?

Ya danganta, ko dai ace zata yi tsada idan aka shigo da ita ta kan iyakokin Najeriya da aka tanadar wato teku, wannan kuma ba wani abin damuwa bane, domin wanda ba shi da ikon cin shinkafar da aka shigo da ita daga waje saboda tsada, yana iya sayan wadda aka noma ta a Najeriya, kuma wannan shi zai baiwa manoman shinkafa na gida damar bunkasa harkar noman shinkafar gida.

DUBA WADANNAN:

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa??

KARANTA BAYANI AKAN AIKIN MAMBILA HYDROPOWER PLANT DAKE JIHAR TARABA

KALLI YADDA DUBUN SHUGABAN MASU GARKUWA DA MUTANE TA CIKA A HANNUN ABBA KYARI... LATEST VIDEO

Babu wata gwamnati da ta san abinda take yi, zata yadda a dinga jidar dala daga Nijeriya, ana zuwa wasu kasashe ana azurta manoman shinkafar can kasashen, suna bamu shinkafar da aka cika ta da sindaran da zasu illata lafiya, alhali za a iya samar da shinkafar a gida Nijeriya mai tsafta da inganci, mara cutarwa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user