Wednesday 21 August 2019

KALLI YADDA DUBUN SHUGABAN MASU GARKUWA DA MUTANE TA CIKA A HANNUN ABBA KYARI... LATEST VIDEO

Tura Wannan Zuwa Ga
Gawurtaccen mai garkuwa da muntane Alhaji Hamisu Bala Wadume a hannun 'yan sanda bayan an samu nasaran kamashi daren jiya a gidansa da ya gina a unguwar Layin Mai Allo Hotoro jihar Kano.

Hamisu Bala Wadume tare da jami'an tsaro


Marubuci: Datti Assalafy

Ina wadanda suka kubutar da Hamisu? an dai yi abin kunya, asiri zai tonu, babu halin boye gaskiya kuma, ku koresu daga aiki kawai, ku miko su inda ya dace don su fuskanci tuhumar cin amanar tsaron kasa da kisan gilla na kwararrun jami'an 'yan sandan Nigeria.

'Dan ta'adda Alhaji Hamisu Bala Wadume ka cutar da mu 'yan Nigeria masu kaunar zaman lafiya, ka hana idon mu bacci, a dalilinka aka cusa mana matsanancin bacin rai da bakin ciki.

Hamisu Bala Wadume 


Jama'a wannan rikakken 'dan ta'adda yana da alaka da manyan mutane 'yan siyasa da kuma jami'an tsaro, kuma rikakken matsafi ne mai tsananin wayo da dabara, babban bokansa da yake daurashi a tafarkin tsafi yana garin Maiduguri, yanzu haka matarshi tana Kasar Saudiyyah, bayan faruwar abin ya hanata ta dawo Nigeria.

Sarkin Yaki DCP Abba Kyari yana garin Ibbi a jihar Taraba inda wannan 'dan ta'adda yayi sanadin halakar yaransa guda uku, yana cigaba da tattara sahihan bayanai da shaidu da bincike, daga can ya bawa yaransa umarni suka je suka kama Hamisu bayan ya gano maboyarsa, har ya koma Abuja, ina mai tabbatar muku duk wanda yake da hannu a cikin wannan al'amari bincike sai ya zakuloshi an tona masa asiri, kuma sai ya fuskanci hukunci.

Kalli Bidiyon kai Tsaye..

Rikakken 'dan ta'adda mai garkuwa da mutane Alhaji Hamisu Bala Wadume yake bayani da bakinshi cewa shine wanda 'yan sanda suka kama a garin Ibbi, sai sojoji suka bisu suka bude musu wuta suka kashe 'yan sandan, sannan sojojin suka daukeshi suka kaishi sansaninsu suka cire masa ankwa na hannu da kafa (handcuff/legchain) suka barshi ya gudu kafin 'yan sandan suka sake kamashi a karo na biyu, Wannan abin kunya ne da takaici, wallahi anci amanar tsaron Nigeria.

Muna jiran sakamakon bincike da hukuncin da Maigirma Shugaban Kasa Baba Buhari Maigaskiya zai zartar.

DUBA WADANNAN:





Don haka mu kwantar da hankali, Insha Allahu gaskiya zatayi halinta.

Allah Ka taimaki rundinar 'yan sandan Kasarmu Nigeria, Allah Ka kare mana DCP Abba Kyari tare da yaranshi, Allah Ka kara musu taimako da nasara Amin.

Muna rokon Allah Ya cigaba da tona asirin maciya amanar tsaron Nigeria Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user