Wednesday 21 August 2019

WATA SABUWA: DAGA YAU DOLE NE SAI MASU TARBIYA NE ZASU YI FINA-FINAN HAUSA - SHEHU HASSAN KANO

Tura Wannan Zuwa Ga
Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano karkashin jagorancin Shugabanta Isma'il Afakallahu ya rantsar da kwamitin tsoffin 'yan fim da zasu tantance duk masu ruwa da tsaki a harkar fim din Hausa.

Shehu Hassan Kano



Kwamitin da Shehu Hassan Kano ke jagoranta zai fara aikin tantancewar ne ranar Litinin mai Zuwa zai kuma dauki tsawon wata guda yana aikin tantancewar.

A tattaunawar da yayi da Jaridar SARAUNIYA Shehu Hassan Kano ya bayyana manufar kwamitin shine tsaftace harkar fim din Hausa da marasa manufa da TARBIYYA suka cika shi da badala maimakon basira da gogewa.

Ga Cikakkiyar hirar a nan ga mai bukata

Kalli Bidiyon kai Tsaye...


Ya kuma jaddada kudirinsu na cewar ana son samar da nagartattun masana ne harkar domin dawo da martabar masana'antar kamar yadda take a baya.

Bugu da kari tare da rage kwaranyowar mata 'yan kama waje-zauna da suka mamaye harkar fim ba tare da sun zo da muharramansu su ba. Kazalika kwamitin zai rika ladabtar da masu zagi gami da batanci a kafar sadarwa.

DUBA WADANNAN:





Tantancewar ta hada da Marubuta, Masu Daukar Hoto, Masu Tace Hoto, Masu Shiryawa, Masu Bayar Da Umarni, Mawaka Da Makada, Masu Daukar Nauyi, Masu Kwalliya Da Sauransu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user