Thursday 8 August 2019

HOTUNA DA CIKAKKEN TARIHIN ABUBAKAR MAI SHADDA: BABBAN BURINA A DUNIYA IN AURI JARUMA HASSANA MUHAMMAD - FURODUSA ABUBAKAR MAI SHADDA

Tura Wannan Zuwa Ga
A hirarsa da Aminiya ya bayyana dalilin da ya sa ya fara harkar fim da burinsa a harkar da dalilin da ya sa ya ci gaba da shirya fina-finai duk da kasuwar fim ta durkushe a shekarun baya.

Abubakar Maishadda da Jaruma Hassana Muhammad



Abubakar Bashir Abdulkarim wanda aka fi sani da Abubakar MaiShadda, fitaccen furodusa ne a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood. Shi ne shugaban kamfanin shirya fina-finai na Maishadda Inbestment. Maishadda ya fara shirya manyan fina-finai a shekarar 2015 kuma ya lashe gasar Best Indigenous Language Hausa AMBCA 2015 da fim din ‘Bincike.’ Ya zama Gwarzon Furodusa (Best Producer) na Gasar Best City People Award da kuma Zuma Festibal Award na shekarar 2018.


Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Abubakar Bashir Abdulkarim wanda aka fi sani da Abubakar Bashir Maishadda, an haife ni a Dala Unguwar Dandishe, na yi makarantar rainon yara a Shukra International School da ke Kurna, daga nan muka dawo Gadon Kaya, inda na karasa firamare da sakandare, sai na yi diploma a kwas Nazarin Kasashen Waje a Jami’ar North West da ke Kano, daga nan na fara harkar fim.

A ina ka samo sunan Maishadda?

Sunan Maishadda shi ne sunan da muke amfani da shi a gidanmu, saboda mahaifina yana kasuwancin shadda tun tasowarsa, sai sunan ya bi shi, bayan an haife mu sai muke amfani da sunan Maishadda. Ni ma na fara zuwa kasuwa ina sayar da shadda, daga baya ne na koma harkar fim gadan-gadan.

Abubakar Maishadda tare da Kamal S. Alkali


Me ya ja hankalinka ka fara harkar fim?

Tun ina karami sosai a unguwarmu ta Dandishe an taba zuwa an dauki wani fim mai suna ‘Boda’, a fim din akwai jaruma Fati Mohammed, a lokacin akwai wani kaura ana ce masa Buda to a layinmu yake, tun a nan na fara sha’awar harkar fim. Sannan fina-finai irin su ‘Mujadala’ da ‘Abin Sirri Ne’ da ‘Sabani’ da sauransu sun kara mini sha’awar harkar fim, har yanzu ina tuna fina-finan, don haka sha’awar fim zan iya cewa da ita na taso, har ta kai ina zuwa lokeshan na daukar fim. Na zama dan fim ta hannun Darakta Hafizu Bello, shi ne mutum na farko da ya ba ni damar shirya fim (producing), amma kafin shi akwai Abubakar A.S Maikwai da Musa Maisana’a duk lokacin da za su yi aikin fim ina zuwa wurinsu.

Bayan Hafizu Bello sai na fara harka da maigidana Abba Miko Yakasai, shi ma na zauna da shi na koyi wasu abubuwa, a haka dai har na lakanci shirya fim.

A cikin harkar fim, za ka ga wadansu sun zabi zama jarumai, wadansu daraktoci, me ya sa kai ka zabi bangaren shirya fim?

Tun a farko ba shirya fim na so in fara yi ba, na fara ne da manajan yadda ake daukar nauyin fim, inda daga baya sai na fara shirya fim. Na fara da shirya fim mai suna ‘Bincike’, inda da fim din na lashe gasar ‘Best Indigenous Language African Magic ta 2015. Dalilin da ya sa na zabi bangaren shiryawa shi ne, ba na sha’awar zama jarumi ko darakta, abin da nake sha’awa shi ne in shirya fim ko in zama manajna shiryawa (Production Manager).

zuwa yanzu ka shirya fina-finai nawa?

Daga lokacin da na fara shirya fina-finai zuwa yanzu na shirya fina-finai akalla 20. Akwai ‘Mariya’ da ‘Mujadala’ da ‘Hafiz’ da Sarina’ da ‘Hauwa Kulu’ da ‘Wutar Kara’ da ‘Dan Gaske’ da ‘Karfen Nasara’ da ‘Ana Dara Ga Dare Ya Yi’ da ‘In Search of the King’ da ‘This is the Way’ da ‘Light and Darkness’ da ‘Kalen Dangi’ da ‘Kanwar Dubarudu’ da sauransu.

Abubakar Maishadda


A shekarun nan kasuwanci fina-finai ya ja baya, amma kai a lokacin ka rika shirya fina-finai, me ya sa ba ka noke kamar yadda sauran ’yan fim suka noke wajen shirya fina-finai ba?

Abin da nake so ka gane shi ne Allah (SWT) Shi ne Mai komai, Mai tsara komai a lokacin da Ya so, duk lokacin da aka samu tsanani akwai sauki. A gaskiya lokacin da aka samu matsala a harkar fim, to ni a lokacin ne ma nake ji a raina na fara ta, saboda na yi fina-finai ne kawai amma cikin ikon Allah komai ya tafi daidai. Mun kai fina-finan silima, kuma babu wanda aka yi asara. Akwai ‘Kalen Dangi’ kudinsa ya dawo an ma ci riba sosai, haka ‘Mariya’ da ‘Mujadala’ da ‘Hafiz’ da sauransu, kuma an samu kudi sosai. Don ka san abin ana jin dadi yanzu haka ma akwai fim dina mai suna ‘Hauwa Kulu’ da zan nuna ranar Idin Babbar Sallah.

Me fim din ‘Hauwa Kulu’ ya kunsa?

Yana magana ne a kan illar fyade a kan kananan yara, don haka nake kiran masu kallon fina-finan Hausa su zo su kalli wannan fim, fim ne da ba a taba gabatar da irinsa ba, akwai jarumai irin su Ali Nuhu da Hadiza Gabon da sauransu.

Mene ne burinka a Kannywood?

Burina in zama babban furodusa a duniya, ina nufin in zama furodusa ba kawai a fina-finan Kannywood ko na Nollywood ba, in yi fina-finan da duniya za ta gani ta yaba, ta kuma tabbatar da an shirya babban fim.

Akan ga kana dora hotonka da jaruma Hassana Muhammad, sannan ka rika yin kalaman soyayya, shin mene ne a tsakaninku?

Ba masoyiyata ba ce kadai, Hassana ita ce matar da zan aura.

A cikin jaruman da kake aiki da su, shin wadanne ka fi jin dadin aiki da su?

A gaskiya duk jarumin da ka ga ina aiki da shi, to ina jin dadin aiki da shi, saboda idan ba ni da kyakkyawar fahimta da mutum ma ba zan kai kaina wurinsa ba. Idan na duba na ga wanda na ga zai iya ba ni abin da nake so, sai in rika aiki da shi. Don haka duk jarumin da ka ga ina aiki da shi ko mace ko namiji to ina jin dadin aiki da shi.

Yanzu wane kalubale kake fuskanta?

A yanzu dai zan iya cewa babu wani kalubale da nake fuskanta, domin abubuwa suna tafiya daidai yadda nake bukata, sai dai ’yan kananan abubuwan da ba za a rasa ba.

MUKALOLI MASU ALAKA:





Mene ne kiranka a karshe?

Ina so in yi amfani da wannan dama in gayyaci masu kallon fina-finan Hausa mu kasance da su a ranar Idin Babbar Sallah don kallon fim din Hauwa Kulu a Ado Bayero Mall da ke Shoprite a Kano. Ina so masu kallo su fahimta ta hanyar zuwa su kalli fim din ne za mu samu damar ci gaba da kawo musu sababbin fina-finai masu ma’ana da kuma kayatarwa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Source: AMINIYA


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user