Wednesday 14 August 2019

JARUMI SADIK SANI SADIK YAYI ABIN DA BABU WANI DAN FILM DA YA TABA YI A TARIHIN KANNYWOOD

Tura Wannan Zuwa Ga
Mutane sun tofa albarkacin baki bisa rubutun da nayi akan Sadik Sani Sadik, wasu sun zargeni da cewa wai kudi ya bani, saboda kawai na fadi wata dabi'a tasa mai kyau da nima aka bani labari.

Sadik Sani Sadik

Marubuci: Datti Assalafy

Ya kamata amin adalci, cewa nayi daya daga cikin limaman da suke jan sallah ta asuba a masallacin Indimi Ustaz Mustapha Muhammad  Bakomi shi ya kirani a waya ya sanar da wani abinda ya bashi mamaki game da Sadik,  mutanen Maiduguri zaku iya zuwa Masallacin Indimi ku tambayeshi.

Duk kiyayyar dake tsakanin mu da wani, sai muka ga ya aikata abin kirki ba laifi bane don an bayyana, wannan shine tarbiyyan da aka bamu, zan bada misali da Zakzaky, lokacin da ake tsakiyar kisan rayuka a jihar Zamfara, mun fitar da wani bidiyo inda Zakzaky yake bayani akan abinda ya shafi tsaron Zamfara, mukace gaskiya ne ya fadi, har ma nayi masa fatan shiriya.

Mutane suna ganin cewa muna kawo bayani akan illar 'yan hausa film, sai kuma akaga na kawo bayani akan abin kirki da daya daga cikinsu yayi, bai kamata hakan ya zama laifi har da zargi ba, wallahi babu wata alaka ko ta kusa ko nesa da ya taba hadani da Sadik Sani Sadik, ban taba ganinshi a zahiri ba.

Tabbas ya cancanci yabo duba ga abinda ya aikata, akwai masu ra'ayin wai hadiza Gabon ita tafi cancanta da samun yabon mu, domin tana taimakon marasa galihu, wannan kuskure ne, domin akwai banbanci tsakanin aikinsu.

Ita Hadiza tana saka wa a dauki hotuna ta yayata a duniya, shi kuma wannan imba don na'ibin Masallacin Indimi ya sanar ba da baza'a sani ba.

Shaiɗan shugaban matanen banza ya sami adalci ta hanyar yabon da annabi (SAW) yayi mishi akan ayatul Kursiyyu, ina kuma ga ɗan uwa musulmi?

Adalci shine idan aka fadi sharrin mutane watarana idan sunyi abin kirki a fadi alkhairinsu.

Akwai wadanda sun bi ni ta sirri suka fada min abinda suka sani na barna da Sadik Sani Sadik yake aikatawa wanda ni bai bayyana a gareni ba, idan ya tabbata gaskiya muna masa fatan shiriya.

MUKALOLI MASU ALAKA:

Kalli Sababbin Hotunan Jarumi Rabi'u Rikadawa cikin Shigar Mata a wani Sabon Film

BABBAN BURINA A DUNIYA IN AURI JARUMA HASSANA MUHAMMAD - FURODUSA ABUBAKAR MAISHADDA

NAFI KOWA FARIN CIKIN KORAR SUPER EAGLE A WASAN AFCON 2019 - DATTI ASSALAFY

Daga karshe duk wanda ya zargeni akan cewa Sadik Sani Sadik ko wani 'dan hausa film ya bani kudi shiyasa na fadi alherinshi na yafe, Allah Kuma Ya zama shaida.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user