Wednesday 21 August 2019

KARANTA YADDA YADUWAR HANYOYIN ALFASHA A YANAR GIZO SUKE HALLAKAR DA SAMARI DA MAGIDANTA

Tura Wannan Zuwa Ga
Tabbas alfasha tana kara mummunan yaɗuwa a tsakanin al'umma musamman ta kafofin sada zumunta.


Yaduwar Hanyoyin Alfasha


Allah Ya haramta wa bayinSa masu mishi biyayya kusantar alfasha wacce ta bayyana da wacce ta ɓoyu.

Allah ya haramta kusantar zina ta kowace fuska.

Mu sani cewa Allah Ya lissafa gani ( Ido) daga cikin ni'imomin daya mana, kuma Ya ce tabbas Zai tambayemu akansa da dukkan sauran ni'imomi baki ɗaya.

Kallon tsiraicin da ya haramta gareka ko gareki yana daga cikin mafi haɗarin al'amari a rayuwar ka da rayuwarki.

Kayi nazari tsakaninka da Allah;

Me zaka ƙaru
dashi wajen kallon alfasha da kallon tsiraicin ƴar wani ko matar wani?

Kayi nazari tsakaninka da Allah;

Wace amsa zaka bayar idan Allah Ya tambayeka game da ni'imar gani daya maka kuma ka saɓa mishi da wannan ni'imar?

Wallahi ba abinda kallace kallacen batsa da alfasha zai ƙareka dashi sai daɗa nisantaka da Allah da kuma ja maka fushin Allah.

Kayi nazari tsakaninka da Allah za ka so ace lalacewar tarbiyyar ƴarka ko matarka yakai ta dinga ɗaukar hoton tsiraicinta tana tura wa wani?

Kallon alfasha yana kashe zuciyar bawa da shafe mishi basira.

Abinda yake wajibi a kammu shine mu tuba daga wadannan munanan halayen kafin muyi farkar jaji. 

DUBA WADANNAN:
Allah Ka yafe mana laifuffukanmu, Ka taimakemu akan ayyukan alkhairi da barin munanan aiki. Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user