Wednesday 21 August 2019

Karanta Hanyoyi Mafi Sauki da Zaku Kare Facebook Account din Ku daga 'Yan Dandatsa (Hackers)

Tura Wannan Zuwa Ga
Mukanji ba dadi a duk lokacin da wani ya kira ya sanar damu cewa an kwace masa account dinsa na Facebook, mun tabbata rashin daukar matakan daya kamata wajen bawa account din kariya ke sanyawa a dinga saurin kwace account.


Kafin bude shafin Facebook


Marubuci: Rabi'u Biyora

Da farko ya kamata ku dena amfani da lambar waya a matsayin Password, ku nemi wasu kalmomi masu tsauri wadanda ko na kusa dakai ba zai taba tunanin dasu kake amfani ba, idan a karamar hukuma kake da zama sai ka nemi sunan wani abu dake birni kayi amfani dashi.

Misali SHAWARMA76¥8 da sauran sunaye na abubuwan da yan birni ne ke amfani dasu, idan a birni kake sai kayi amfani da DADDAWA12@2 da sauran sunayen kayan karkara, hakan zai baka kariya daga tunanin yadda abokanka na birni masu son kwace maka account zasu san abun daka saka.

Na Biyu ku dena bude link da ake turamuku a inbox a nemi ku bude don kallon abun mamakin dake ciki, ko waye ya turamaka da link a inbox kada kayi saurin budewa koda kuwa cewa zaayi kana budewa zaka samu Ten Thousand Dollars.

Kuyi activating din Code a Facebook account dinku ta yadda babu wanda ya isa ya shiga account din har sai yana da code din da zaa turo zuwa layinka na waya da zakayi activating dashi, kenan koda wasu sun samu nasarar sanin Password dinka ba zasu iya shiga ba tunda basu da code din.

Ku tabbata kun hade Facebook Account dinku da Email dinku Na Gmail ko Yahoo ta yadda idan ma an samu akasi zaa iya tuntubar Kamfanin Facebook akan matsalar.

Babu dadi mutum yayi sakaci da account dinsa kuma ya nemi mu gyara masa yaga bamuyi ba, domin muma muna kula muke da namu yadda ya kamata, kaima idan ka dauki mataki sosai ba wanda zai kwace maka account cikin sauki, in kaga ka dena amfani da account din ka sai dai in laifi kayiwa Kamfanin Facebook suka dakatar dakai.

DUBA WADANNAN:




Wanda shima idan ka saka email dinka, sukan iya dawo dakai bayan tattaunawa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user