Thursday 12 April 2018

SHIN KO KASAN YADDA ZAKA GYARA MEMORY CARD DINKA IDAN YA LALACE?

Tura Wannan Zuwa
Yan da ake gyara Memory Card ko Flash Dinka idan ya lalace ya yi (Currupt). Memory Card shi ne abu
na biyu mafi soyuwa da Muhimmanci a cikin waya
bayan layi (Sim Card).

Mu kan ji ba dadi yayin da Memory Card dinmu ya lalace (Currupted), misali
kana kan amfani da Memory Card dinka, kwatsam!

Sai kaga ya nuna maka "Damaged SD Card" in kayi
Format din a cikin wayar ya kiyi, in ma an sa a
computer anyi format dinsa haka zai ta nuna maka
koda kayi format din ba zai ci gaba da amfani ba.

A takaice dai Memory Card dinka ya lalace ka rasa
komai na cikinsa, ka rasa shi kansa Memory Card
din.

Abinda za'ayi magana a yau shi ne yanda zaka
gyara Memory Card dinka a sauKake ba tare da
kayi amfani da wani Software ba.

Abubuwan da ake
bukata kafin gyara Memory Card ko Flash:

1. Natsuwa: yana da kyau ka natsu sosai wajen
gyara lalataccen Memory Card ko Flash dinka.

2. Lalataccen Memory Card tare da Card Reader
waton gidan sa Memory Card din 3. Computer: Dole da ita za kayi aiki wajen gyara
Memory Card din naka.

Da farko ka bude Coputer din sai ka danna alamar
Windows din Computer, zai fito maka da shafuKan
Computer din a kasa. Akwai wajen search sai ka
rubuta "CMD" kana rubutawa zaka ga ya fito, sai ka budeshi inya bude sai ka rubuta “DISKPART” sai ka
5aba Enter Key na Computer.

Daga nan zai kai ka wani shafin, sai ka rubuta “
LIST DISK” sai ka danna Enter Key zai nuno maka
Disk wato Memory din Computer din da kuma
lalataccen.

Sai ka duba kaga wannene lalataccen a ciki, Disk 1
ne ko DisK 2 amma yawanci yafi zuwa a DisK 1, sai
ka rubuta “SELECT DISK 1” sai ka taba Enter Key
zai nuna maka DISKPART> DisK 1 is now selected
sai ka sake rubuta “CLEAN” sai ka taba Enter Key
DisKPart> Succeed Cleaning The Disk. Sai ka sake rubuta “CREATE PARTITION PRIMARY” sai ka tba
Enter Key, zai nuno maka DISKPART> Succeed
Creating In The Specified Partition
Sai ka rubuta “ACTIVE” sai ka taba Enter Key zai
nuna maka DISKPART> Marked The Current
Partition as Active sai ka rubuta “SELECT PARTITION 1”

Sai ka taba Enter Key zai nuna maka, Partition 1 is now
The Selected Partition sai ka sake rubuta “FORMAT
FS=FAT32” sai ka taba Enter Key daga nan zai fara
Format zaka ga ya sama 0% to Complete. A haka a
hankali har sai ya kai 100%.
Ka tabbatar kayi shi kamar yanda yake.


Source by ©Hausa Class
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user