Thursday 12 April 2018

Karanta Kaji: Saudiyya za ta fara shirya bikin kade-kade da raye-raye

Tura Wannan Zuwa

A farkon shekarar da mu ke ciki, wata tawaga ta masu kade-kade da raye-raye daga kasar Lebanon suka yi wasan kwaikwaiyo na farko a Saudiyya inda suka ba da labarin wani sadauki da ya yi suna kafin isowar addinin Islama da kuma masoyiyarsa 'yar kabilar Bedouin mai suna Abla.

Wannan ya na cikin shirye-shirye masu nishandantarwa da aka bullo da su a cikin kasar mai ra'ayin mazan jiya.

Yana cikin gagarumin shirin yerima mai jiran gado Mohammed bin Salman da aka yi wa lakabi da vision 2030, na mayar da kasar daga wadda take dogaro da man fetur zuwa ta mai kazar-kazar ta fuskar tattalin arziki.

Yayin wata ziyara da ya kai Burtaniya da Amurka da kuma Faransa, Yerima Mohammed mai shekara 32 ya rika neman taimakon kasashen waje a kan yadda zai cimma wannan buri nasa.

A ranar Litinin ne kungiyar kade-kade da raye-raye na Paris ta sa hannu da Saudiyya a kan yadda za ta taimaka wa kasar kafa tata kungiyar kade-kade da raye-raye ta kasa.

An soma shirye-shiryen bude gidan kade-kade da raye-raye na farko a birnin Jeddah wanda shi ne birni mafi girma na biyu a kasar.

Ministan raya al'adun gargajiya na Saudiyya ya yi shellar wani sabon tsari bayan tattaunawar da suka yi da takwaran aikinsa na Faransa:
Gajerun fina-finan Saudiyya za su shiga cikin bikin baje kolin fina-finan Cannes a karon farko da za a yi a shekarar da mu ke ciki.

Hakan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen bude gidan sinima na farko a Riyadh a watan da mu ke ciki, ga kuma bangaren harkar fina-finai na cikin gida da ke samun karbuwa.

Sai dai yarjejeniyar raya al'adun gargajiya mafi girma da kasashen biyu suka hannu a kai, za ta bai wa Faransa damar kawo sauyi a akasarin wuraren da babu kowa, zuwa gidan ajiye kayan tarihi.

Manufar shirin ita ce a samar da wurin adana kayan kofai na kasar, ciki har da zane-zanen layin dogo na Hejaz da ya tashi daga Damascus zuwa Medina, wanda TE Lawrence ya kai wa hari lokacin da Larabawa suka yi bore.

A watan Fabrairu ne Saudiyya ta ce za ta zuba jarin fam bilyan 64 a bangaren nishadi a cikin shekaru goma masu zuwa.

Wannan dai wani sauyi ne ake gani a cikin kasar da wasu ke yi wa kallon mai tsaurin ra'ayi, inda askarawan kasar kan hana duk wasu kade- kade da raye -raye da ake yi a bainar jama'a.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: