Thursday 12 April 2018

Karanta Kaji: Dalilin Dayasa Ba Na Fitowa A Fim Amma Har Yanzu Ina Shiryawa –Safna Aliyu

Tura Wannan Zuwa

A baya ba a cika samun jaruman fim musmaman ma mata su na yin wasu harkoki na kasuwanci ko na sana’a ba, sai dai kawai mace ta ce ita ’yar fim ce. To, amma a yanzu yanayi ya canja, ta yadda za ka ga da damansu a yanzu kowacce ta na yin harkokin kasuwancinta.

SAPNA ALIYU MARU ta na daya daga cikin jaruman fim mata da a yanzu su ke sahun manyan ’yan kasuwa, da ta ke shige da fice a cikin kasashe domin saye da sayarwa. Baya da kantin da ta bude a Dantsoho Plaza da ke titin Abdullahi Bayero a Kano.

WAKILIN LEADERSHIP A YAU ya tattauna da jarumar a game da yadda take gudana da kaswancinta a matsayinta na jarumar finafinan Hausa. Shin ta daina aktin ne ko kuma tudu biyu take ci? Don haka sai ku biyu mu ku ji yadda hirar ta kasnace.

Sapna, sunanki ba boyayye ba ne a masana’antar finafinai ta Kannywood, amma dai za a iya cewa sama da shekara daya kenan an rabu da ganin ki. Wannan ya sa a ke ganin kamar kin bar harkar fim ne.

Eh, haka ne, amma dai ni abin da zan fada Sapna dai ba ta daina yin fim ba, don fim sana’ata ce, babu yadda za a yi na daina, sai dai idan na yi aure kuma ko da na yi aure zan ci gaba da yin furodusin kamar yadda na ke yi. Illa iyaka dai a yanzu akwai wasu abubuwa da na ke yi da su ka shaf harkar kasuwanci wanda a yanzu su na saka a gaba. Kuma a yanzu ma fim na daina fitowa a ciki ban daina furodusin ba, kawai dai ba na fitowa ne a ciki.

Kamar wanne irin kasuwanci ki ke yi?

To, kasuwanci ne yanzu ka ga a kantina ka zo ka same ina sayar da kayayyaki irin su atamfofi, leshi, takalma, agogo da ‘yan kunnaye da jakankuna. To kuma wannan harkar ta sa ina da karancin lokcin da zan rinka zuwa lokeshin, saboda shi fim yana bukatar cikakken lokaci/ to ni kuma a yanzu ba ni da shi. Don haka idan na karbi aikin mutane ban san yadda zan yi a shi ba. Saboda kula da kanti da kuma zuwa na kawo kaya. Amma dai nan gaba kadan idan na gama saita harkokina masoyana za su ci gaba da ganina a fim.

A yanzu kin kai tsawon wanne lokaci ba ki fito a fim ba?

To, ina ganin dai a yanzu na fi shekara don tun fim dina mai suna Watarana, da muka yi fim din da Adamu a Kaduna, ina ganin tun daga ban kara fitowa ba.

A matsayinki na jaruma, furoodusa, ko ya ya kike kallon harkar fim a wannan lokacin?

To, gaskiya ana smaun ci gaba sosai don na ga ana fita aikin fim a kodaysuhe don haka ci gaba ake smau da koia baya aka samu ba za a samu haka ba, don haka an samu ci gaba ta kasuwa da kuma kayan aiki, ni dai a yadda nake gani kenan.

Me ya sa a yanzu ba a samun jarumai masu awa ake yayin dai kamar da sai ki ga mata da yawa ana yayinsu a yanzu sai dai daya ko biyu?

To, abin da ya ya sa yanzu idan ka duba a ba cika tsayawa ba fim kadai kusan kowacce jaruma tana da harkokinta na kasuwanci da take yi don haka yanzu an daina tsayawa ana jiran a yi fim sai ake hadawa da kasuwanci. To irin wannan sai ka ga wata ma idan ana neman ta ta fito a fim sai ka ga ba ta a lokaci kamar a baya don haka za ka ga duk an ragu wasu kuma sun yi aure ba a samu wadanda suka maye gurbin su ba

Amma ba kya ganin a matsayinki na ‘yar kasuwa nan gaba idan kika dawo za ki yi fim sai a ga kudin da za a ba ki sai furodusa ya shirya don kada ki raina?

Ai ba haka ba ne shi dan fim duk wata alfarma da ya samu a duniya ta hanyar fim ce, don haka duk ina ya je ya dawo fim ne gatansa, don haka ko nawa za a bai wa mutum ba zai raina ba. Don tun kadin ya zama wani abu ya san haka ake biyan a don haka ba wani abu ne daban ba.

To, ya ya kike iya gudanar da kasuwancinki a matsayinki na jaruma da kowa ya san fuskarki?

Ina jin dadi sosai don ka ga su ‘yan fim suna da alfarma. Sau da yawa idan na je waje ko da ana hana mutane shiga sai ka ga an bar ni na shiga. Aga an ga ni ‘yar fim ce. Do haka ina jin dadin sosai kuma wasu ma saboda sun san kai dan fim ne suna zuwa sayan kaya wajena. Dn su zo su gan ni kuma duk fim ne ya ja min wannan ce alfarma.

To ya ya mu;malar ki take a yanzu da ‘yan fim?

Mu’amala ta tana nan kamar dai muna tare da su kamar tare uke yi kuma na fada maka ina furodusin don haka koyaushe muna tare sai dai idan na tafi wajen kasuwancina.
Daga karshe wace shawara kike da ita musamman ga mata ‘yan fim?
To, shawarata a garesu ita ce, lokaci ya yi da za su gane harkar fim kadai ba za ta rike su ba. Domin kuwa suna cikin fim din za su yi aure.

Kuma idan sun yi aure ba za su ci gaba da fim ba, don haka su raba kafa su rinka hadawa da kasuwanci ta yadda ko da sun yi aure za su ci gaba da yin kasuwancinsu.

To, madalla mun gode.

Ni ma na gode.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Leadership A Yau and Film Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: