Friday 17 August 2018

BAYANI AKAN ALJANNAH - KARANTA YADDA ALLAH (SWT) YA TSARA ALJANNAH FIDDAUSI DA NI'IMOMI MASU TARIN YAWA

Tura Wannan Zuwa Ga
An gina Aljannah ne da tubali (blocks) na Zinare da Azurfa
tatacciya. Simintin cikinta anyi shine da Almiski mai mutukar
Qamshi.

Ɗakin Ka'aba

An cike tsakanin tubalanta da kayan ado ba Zubarjadi da
Yaaqootu.

An halicci Qasar cikinta ne daga Za'afaran.

Tana da Qofofi guda takwas kamar haka:

1. Jannatul Ma'awa.
2. Daarul Maqaam.
3. Daarus Salaam.
4. Daarul Khuld.
5. Jannatul 'Adni.
6. Jannatun Na'eem.
7. Jannatul Khaseef.
8. Jannatul Firdaus.

•JANNATUL MA'AWA ita ce daga Qasa,

•JANNATUL ADNI kuma ita ce matsakaiciya

•JANNATUL FIRDAUSI kuma ita ce Qololuwa.

Acikin Aljannah akwai Gonaki da lambuna wanda tsawon
kowacce gona da fadinta ya kai tsawon tafiyar shekara 100
ko fiye da haka.

Akwai bishiyoyi masu inuwa masu Ni'ima da tsirrai marassa
Qaya.

An Halicci bishiyoyim cikinta ne daga madaukakin Zinare da
tatacciyar Azurfa.

Suna da manyan ganye kamar girman kunnen giwa, kuma
'ya'yan itacen bassu Qarewa. Suna nan nau'i-nau'i.

Wadanda suke Qaunar juna domin Allah zasu samu shiga
Aljannah kuma acikinta za'a basu wasu Al'amudai na Yaqootu.

Akan Al'amudan akwai Dakuna (rooms) guda dubu saba'in
(70,000) masu haske.

Kuma hasken Wadannan dakunan ne zai haske 'Yan Aljannah
kamar yadda hasken rana yake haske mutanen duniya.

Akwai dakunan cin abinci yalwatattu ta yadda acikin dakin
cin abinci guda za'a samu shimfidu (dining sheet) guda dubu
saba'in (70,00).

Akwai Qananan yara masu hidima, suna zagayawa ko ina cikin
gidan Aljannah. Sunci ado da kaya iri-iri. Kuma Su kansu
suna haske kamar Lu'u.

Bishiyoyin dabinai da inabi wadanda 'ya'yansu ko yaushe
nunannu suke. Kuma suna daf da Qasa. Girman kowanne
nonon dabono yakai kamar Zira'i 12. Kuma kowanne kwayan
dabino guda ya kai girman Tulu, Kuma fari ne tas kamar
madara, Kuma babu Kwallo acikinsa. Zakinsa kuma wane
Zuma!!

Kuma girman kowanne Inabi guda daya yakai girman tulu.

Sai wani Sahabi yace "Ya Rasulallahi guda daya zai isheni
dani da iyalaina?"

Sai ANNABI (S.A.W) yace masa "AI GUDA DAYA ZAI ISHEKA
DAKAI DA KABILARKA MA BAKI DAYA"

TUFAFIN 'YAN ALJANNAH:

Kowanne Dan Aljannah za'a sanya masa riguna guda 70 na
haske. Masu taushi, masu kyalli, Kuma marassa nauyi ko
kadan.

Wadannan rigunan kowacce kalarta daban, nau'inta daban.
Kuma ba irin tufafin duniya bane, domin kuwa babu wacce
take rufe 'yar uwarta.

Saboda tsananin haskensu da kyawunsu, ana iya ganin Siffar
jikin mutum har Zuciyarsa da irin Qarfin soyayyar da take
dauke dashi.

Wadannan Tufafin bassu tsufa ko datti, kuma bassu yagewa.

QORAMUN ALJANNAH

Acikin Aljannah akwai Qoramu (Kogi) guda bakwai:

1. Kogin ruwa.
2. Kogin Madara.
3. Kogin ruwan Zuma .
4. Kogin ruwan giya (Sharabun Tahoorun).
5. Kogin Kafoor.
6. Kogin Zanjabeel.
7. Kogin Tasneem.

Ya Allah muna tawassuli da fiyayyen bayinka wato ANNABI
(S.A.W) domin alfarmarsa ka gafarta mana kasa muna cikin
'Yan Sahun gaba wajen shiga Aljannah Albarkan ANNABI
S.A.W Amin.



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user