Friday 17 August 2018

Karanta Masifar Da Ta Kunno Kai A Cikin Al’ummar Hausawa

Tura Wannan Zuwa
Ba wani abu bane wannan face yawaitawar samuwar mata ‘yan madigo. Dole a kira wannan abin da masifa domin yana daga cikin abubuwan da ke haifar mana masifun da muke fuskanta a yandu cikin al’umma. 


Hakika wannan wata jarabawa ce da mata suka dorawa kansu, shin kina mace wacce za a kiraki da uwa ta yaya zaki fara aikata wannan mummunar abu haka? Shin wacce tarbiyya muke tunanin zamu dora yaranmu masu tasowa a kai nan gaba? Shin mun taba zama munyi tunanin wacce irin kalubalen rayuwa zamu fuskanta ta dalilin wannan aika aikar?

Tabbas duk wacce ta samu kanta cikin irin wannan rayuwa ta hadu da jarabawa matuka. Haka ana cutar da iyayen yara ta jefa yaransu cikin wannan dabi’a ba tare da saninsu ba bayan sun riga sun basu ingantacciyar tarbiyya daga gida.wasu yaran kan jefa kansu da kansu ba tare da wani ya tilasta musu ba. Mu sa ni a duk lokacin da muka kauce fadin Allah dole mu hadu da dana sa ni.

Mu sa ni wannan dabi’a tana iya haifar mana da matsaloli kala kala kama daga ta gangar jiki har zuwa kwakwalwa, me yasa ba zamu bi hanyar da ta dace ba don samun biyan bukatar mu? Ko yarinya budurwa aka samu da wannan dabi’a bai dace da ita ba kasancewar ta mace da zaa kira ta da uwa watarana, balle macen da ke da igiyar aure a kanta. Ya salam! Wallahi mata muji tsoron Allah, saboda mune kashin bayan gyara al’umma. Shin bama tuna makomar mu ne? Wace hujja muke da itada zamu bayar bayan mutuwar mu muna aikata wannan mummunar dabi’a ta madigo? Wallahi haramcinta mai girmane.

Saboda haka iyaye mata mu kula da mutanen da yaranmu ke muamala dasu ko a gida ko makaranta, mu zama masu matukar sa ido ga yaranmu wajen tafiyar da rayuwarsu na yau da kullum, haka iyaye maza su taimaka wurin ganin tarbiyyar yaransu bata gurbace ba ta dalilin wasu bata gari. A k’arshe mu sa ni cewar dauwama a cikin wannan dabi’a ta madigo yana haifar da cuta a mahaifa, gaban mace wanda baya jin magani, sannan yana haifar da cutar mantuwa da tabuwar kwakwalwa, yana haifar mutuwar wulakanci ga duk me yinta. Ina kira ga iyaye maza da mata akan kulawa da tarbiyyar yaran da Allah ya basu amanarsu zai kuma tambayesu ranar gobe kiyama.

MU JI TSORON ALLAH..

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Leadership A Yau

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user