Tuesday 17 September 2019

KARANTA BAYANI AKAN AIKIN MAMBILA HYDROPOWER PLANT DAKE JIHAR TARABA

Tura Wannan Zuwa
Ka Daure ka karanta gaba daya, ta hakan ne zaka samu dukkan bayanan da kake so.

Da yawan mutane suna bayyana ra'ayin su akan aikin Mambila ba tare da cikakkiyar masaniya akai ba, wasu kuma na amfani da hakan wajen yada farfagandan siyasa, amma a zahirin gaskiya babu karya ko kadan akan aikin, sai dai akwai tarin matsalolin da aikin ke fuskanta masu alaka da fara gudanar da aikin.

Bayani akan Aikin Mambila

Marubuci: Rabi'u Biyora

Ina da cikakkiyar masaniya akan aikin Mambila da alaka da fara aikin tun shekara daya data wuce, inji mai wannan bayanin da zan fassara zuwa Hausa.

Aikin Mambila tsoho ne da aka fara bayar da Kwangila akansa tun zamanin mulkin Obasanjo, Yar'adua da kuma Jonathan, kowanne daga cikin wadannan shugabannin ya bayar da Kwangila ne ga wasu kamfanonin daban-daban, wanda hakan yasa dukkansu ke ikirarin mallakar kwangilar.

Kaso tamanin da biyar na kudaden aikin Mambila 5.7 billion Dollars bashi ne da Bankin Exim na kasar China zai bayar, ita kuma Gwamnatin Nigeria ta bayar da kaso Goma sha biyar, amma hakan bazai samu ba, har sai an samu ikon dakatar da dukkan sauran kwangilolin da aka bayar a baya, wanda hakan kuma Gwamnatin Shugaba Buhari tayi har ya dauketa dogon lokaci kafin samun nasara.

Bayan dogon turanci da tattaunawa Shugaba Buhari ya sanu nasarar akan su 'yan Kwangilar da aka bawa aikin a gwamnatocin baya, har aka amince za'a basu wani bangare na aikin suma suyi, bayan an sasanta tare da janye dukkan shari'oin da suka shigar, sannan Nigeria ta samu damar saka hannun sabuwar Kwangila da Kamfanin CGCC, CGGOC da kuma SINOHYDRO dukkansu na kasar China, an saka hannu a tsakanin Nigerian Ministry Of Finance da Bankin Exim na kasar China.

Kafin Kamfanonin Kasar China su fara aiki a wajen da aka tsara za'ayi aikin, ita Gwamnatin Nigeria ta yi aikin Kwashe dubunnan mutanen dake garuruwan da aikin zai shafa, tare da sauya musu wani sabon wajen da zasu koma, da kuma biyan diyya duk gaba daya, Gwamnatin sai ta samar da sabbin Hanyoyin da kayan aiki zai bi takai, sai ta samar da matsugunin Jami'an tsaron da zasu bayar da kariya gasu ma'aikatan kasar China da zasuyi aiki a wajen, a shekara biyun da akayi bayan sanya Hannu a fara aikin, har zuwa yanzu Gwamnatin Nigeria bata samu damar yin abubuwan da suka shafi kwashe mutane tare da hanyoyin ba, hakan kuma ya faru ne daga Gwamnatin Jihar Taraba tunda sune masu mallakin kasar da za'a mayar da mutanen.

Manyan Matsaloli biyu ne suka haifar da jinkirin fara wannan aiki da aka sanya hannu akansa.

1. Gwamnatin Jihar Taraba taki ta bayar da sabon filin da Gwamnati ta nema inda za'a mayar da wadanda aikin zai shafi gidajen su.

2. Ita Gwamnatin Tarayya taki saka Kaso sha biyar na aikin da aka tsara zatayi tun a farko.

Wadannan abubuwan guda biyu sun temaka sosai wajen jinkirin da aka samu na fara aikin Hasken lantarki na Mambila.

Tabbas aikin samar da Hasken lantarki na Mambila gaskiya ne, bawai cuwa-cuwa akayi akansa ba, ba kuma karya bane kamar yadda wasu suke cewa, sai dai aikin ya hadu da tarin Matsalolin da sai yanzu aka samu ikon magance su.

Aikin Mambila an tsara shi akan za'a kammala a tsawon Wata Saba'in da Biyu wanda ke nufin zaa kwashe shekara shida cur ana aiki, tare da hasashen zaa iya kaiwa har shekara Goma kafin a kammala gaba daya, wanda hakan ke nuna burin Shugaba Buhari na samar da aikin duk da sanin da yayi cewa ba za'a kammala aikin a lokacin da yake kan mulki ba.

Abun da nake son Al'umma su fahimta, a Nigeria babbar matsalar dake damun mu ita ce rarraba Hasken lantarki ba samar dashi ba, idan baku manta ba ai Gwamnati ta Gina Kainji, Shiroro, Jebba tare da wasu Hydropower plant, wadanda duk an siyar dasu ga Kamfanonin kasuwancin rarraba hasken lantarki a Nigeria, kuma hakan bai kawar da wahalar da ake sha akan harkar Lantarki ba, shi kansa Mambila idan aka gama siyar dashi za'ayi ga masu kasuwancin lantarkin indai ba'a sauya wannan tsarin da kasar ke tafiya akai ba, wanda Gwamnatocin baya sukayi akan hasken lantarki.

Gwamnatin Shugaba Buhari da gaske take wajen samar da karin 3050 Megawatts na hasken lantarki daga Mambila, wancan matsalar da aka samu na samun filin da za'a mayar da mutanen da abun zai shafa ya temaka wajen kawo jinkirin fara aikin, amma kamar yadda akaji Minista Engr Saleh Mamman ya fada a hirar sa da BBC Hausa yace an shawo kan wannan matsalar sakamakon shima dan jihar Taraba ne.

Dollars Biliyan bakwai da doriya ba kananun kudade bane, musammam da yake bashi aka ci wajen tafiyar da aikin Mambila, shiyasa nake ganin babban abun da Gwamnati ya kamata ta mayar da hankali akai shine gyara yadda ake rarraba hasken lantarki a kasar, kamfanonin dake kasuwancin hasken lantarki akwai bukatar a sake duba yadda suke aiki, ko kuma a shigo da Attajirai irinsu Aliko Dangote su shiga harkar kasuwancin Gina Hydropower plant tare da kasuwancin sa a Nigeria, tunda dama ita Gwamnatin ta cire hannunta mai yawa daga cikin sabgar.

A karshe nake tabbatarwa da Al'ummar Nigeria cewa aikin Mambila Hydropower Plant ba karya bane, gaske ne kuma ba'a yaudari kowa ba, sai dai tabbas an hadu da matsalolin da sai a yanzu aka samu damar kawar dasu, fara aikin a yanzu ba zaisa a kammala a lokacin mulkin Shugaba Buhari ba, za'a dauki a takaice shekara Shida ko Goma kafin a kammala, don haka ya kamata al'umma su mayar da hankali wajen kiran Gwamnatin akan yadda ake kasuwancin hasken lantarki tare da rarraba shi a Nigeria.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KALLI YADDA 'YAN NIGERIA SUKAI ABIN KUNYAR DA BA A TABA YI BA A TARIHIN DUNIYA

Karanta Sharhin Manyan Masifu Da Bala'in Dake Kunshe Cikin Rayuwar Gidan Yari

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa??

Ahmed Musa Husaini shine ya rubuta cikin yaren Turanci, Ni Rabi'u Biyora na fasaara wasu sashe zuwa Hausa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user