Sunday 15 September 2019

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa??

Tura Wannan Zuwa
SHARHIN DANLADI HARUNA AKAN VAT.

ILLOLIN KARIN HARAJIN VAT

Gwamnatin Tarayya na ikirarin cewa dan abin da take samu daga haraji yayi kadan kwarai. Kuma ta kara da cewar duk a fadin Afirka Nijeriya ce ke da harajin mafi karanci. A wata fadar kuma gwamnatin na cewar da ƙarin harajin zai iya samar wa jihohin kasar nan karin kudin shiga na kimanin biliyan 400 wanda zai samar musu da kudaden ayyukan yau da kullum.

Karin Haraji


Shi dai harajin VAT an kirkiro shi karkashin dokar soja ta 102 a shekarar 1993. An soma aiki da dokar a ranar 1 ga Janairu 1994. Dokar dai ta share tsohuwar dokar harajin saye da sayarwa ta 1986. A yanzu dai, ana aiki da dokar harajin VAT ta 2004 wadda aka yi wa gyara a 2007.

Tun a watan May na 2007, tsohon shugaba Obasanjo ya yi kokarin karin harajin VAT zuwa 10% amma kuma Shugaba 'Yar adua ya rushe dokar bayan kungiyar Kodago ta yi masa korafi.

Ana lissafin harajin VAT ne ta hanyar auna farashin kayan da ake kira input and output. Misali, duk lokacin da ka sayi abu a kanti, za ka gane harajin VAT ta hanyar raba 5 da 105 abin da ya ba ka sai ka ninka shi da farashin kayan da ka saya. Wannan shi ne harajin VAT da ya zama wajibi kowanne dan kasuwa ko kamfani ya aikawa hukumar FIRS duk 21 ga kowanne wata na cinikin watan da ya gabata.

Idan ka sayi abu akan ₦1000, lissafin VAT zai zama 5/105 x 1000 = ₦47.62

Amma yanzu da aka yi karin kenan zai zamana kudin harajin VAT zai zama 7.2/107.2 x 1000 = ₦67.16

Na tabbata kuwa sai sun yi karin kudin abin zuwa ₦1100.

Gwamnatin Shugaban kasa Buhari na dudduba yiwuwar hanyoyin samun karin kudaden shiga, don haka suka ga dacewar karin kudin harajin VAT. Wannan gurguwar shawara ce, domin kuwa za ta haifar da matsaloli da dama kamar haka;

a. Farashin kayan masarufi za su karu, mutane za su fake da guzuma su harbi karsana wajen karin kudin farashin kaya. Wannan zai sa abubuwa su sake dagulewa.

b. Sumogal zai karu. Za a rika shigo da kayayyaki ta barauniyar hanya koda kuwa kayan na cikin wadanda aka amince a shigo da su ne. Hakan zai sake mai da kasar nan baya wajen hada hadar kasashen waje. (Balance of Payment)

c. Za a samu ƙaruwar masu kaucewa biyan haraji ta hanyar ƙiri da muzu (Tax Aversion) da kuma hanyar wayon waniƙiƙi (Tax Avoidance). Wannan kuwa ba zai sa a samu wani kari daga harajin da ake samu a yanzu ba.

d. Gwamnati za ta kara wa kanta ayyuka marasa kan gado, domin kuwa za a samu ƙaruwar wadancan abubuwan da salon kin biyan haraji. Hakan zai sa kudaden gudanarwa zai karu ta yadda ba za a samu wani fifiko da abin da ke kasa a yanzu ba.

e. Gwamnatin tarayya na ikirarin cewar jihohi ne za su fi samun moriyar wannan karin harajin. Babu wani abu da zai faru ga haka sai karawa gwamnonin hanyoyin samun wadaƙa da dukiyar da ke hannunsu. Da aka ba su kudin bailout ma me suka tsinana?

A halin yanzu fa akwai haraji iri - iri da kamfanoni da daidaikun mutane ke biya sama da guda ashirin. Kenan karin farashi akan VAT tamkar ƙarin wahalhalu ne ga yan Nijeriya.

Idan gwamnati za ta ji shawara ta sai na ce da ita:

a. A janye aniyar karin harajin VAT ba shi da fa'ida.

b. A ɓullo da sabbin hanyoyi wajen inganta karbar haraji da toshe kofar zurarewar kudaden da ake tarawa.

c. A sassauta hanyoyin tara harajin da kuma wadanda ke sa wa wasu ke nokewa wajen sauke nauyin da ke wuyansu.

d. A cigaba da wayar da kan jama'a wajen muhimmancin biyan haraji.

Dadin ta ma dai wannan ƙarin harajin ba zai yi tasiri ba har sai majalisar tarayya ta amince da shi. Ina sa rai ƙungiyoyin ƙwadago da na 'yan kasuwa za su taka rawa wajen hana aiwatuwar wannan ƙari mara kan gado.

MU SAKE DUBA HARAJIN VAT.

Jiya wani maigidana ya jawo hankalina dangane da harajin VAT. Ya ce na gaza fayyace kayayyakin da ake dora musu wannan harajin da wadanda ba a dorawa.

Lallai kam  dokar harajin VAT ta kawwame wasu abubuwa guda 13 da ba a dora musu harajin VAT akansu. Sannan akwai wasu abubuwan da suna cikin lissafin amma babu komai a gare su watau zero rate.

Sai dai kuma da yake 'yan kasuwarmu ba su da takunkumi, ba lallai ne su yi la'akari da hakan ba. Na tabbata karin farashi za su yi na kan mai uwa da wabi suna fakewa da cewar an yi karin kudin harajin VAT. Shi ya sa na ce za a fake da guzuma a harbi karsana.

Abubuwan da aka yafewa kudin harajin VAT su ne:

1. Magungunan asibiti da sauransu

2. Kayan abincin yau da kullum

3. Littatafai da sauran abubuwan ilimi

4. Kayayyakin jarirai

5. Manyan injunan da aka shigo da su domin masana'antu

6. Manyan injunan da aka kera domin aikin gas da fetur

7. Manyan motoci da injunan aikin gona

8. Duk kayayyakin da za a fitar da su waje

9. Takin zamani da ake samar a cikin gida da duk magungunan dabbobi

10. Cajin da likitoci ke yi wa mara lafiya

11. Ayyukan  bankunan tsimi da tanadi (Micro Finance Banks).

12. Wasan kwaikwayo da makarantun ilimi ke gudanarwa domin koyo da koyarwa.

13. Duk wani aiki da aka yi a kasashen ketare.

Baya ga wadannan abubuwa da aka yafewa harajin VAT akwai kuma wasu da aka kebe ba a ƙara musu ko kwabo duk da cewar suna komar  VAT.

Waɗannan abubuwa sun haɗa da:

1. Duk kayan da jami'an diflomasiyya suka saya

2. Kayan da aka yi musamman domin fitarwa kasashen waje.

3. Kayan da aka saya domin ayyukan jin ƙai da taimakon al:umma.

Daga wadannan abubuwa za mu ga cewar da dama za a yi ta fakewa da su ana kin biyan harajin a gefe guda kuma 'yan kasuwa na rufe ido su yi ta zabgawa kaya farashi bisa hujjar an yi musu karin haraji.

Shi dai haraji na daga tubalan da ake kira 'Automatic Stabilizers' idan kudi sun yi yawa a hannun mutane, sai a kara haraji, idan kuma ana talauci sai a rage shi. Ya zuwa yanzu a Nijeriya talauci ake ciki ko arziki? Ya kamata gwamnati ta yi la'akari da wannan.

Duk da kasancewar wasu ƙasashen na Afrika na cajin VAT har zuwa kimanin 20% ko fiye, bai kamata Nijeriya ta rika koyon saƙa da baƙin zare ba. Ƙarin harajin nan ba zai amfani kowa ba sai tsirarun jami'an  gwamnati da kuma ɗaiɗaikun 'yan kasuwa.

Idan gwamnati ta zartar da wannan hukunci na ƙarin VAT, ta tabbata burin ta na fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci ba zai cika ba, maimakonsa miliyoyin mutane ne za su afka talaucin. Allah ya kiyaye.

Kada fa ku yi tsammanin cewar kashi 2.2% aka kara a harajin VAT.

Bal an kara kashi 44%. Lissafin a gwarance shi ne 2.2/5 x 100 = 44.

Idan kana sayen makilin akan ₦200 yanzu zai iya komawa ₦288 ko ₦300.

Allah ka tsare mu da wannan fitina ta tsofaffi

Karin Haraji

SHARHIN RABI'U BIYORA AKAN VAT.

DA FARKO ME NE NE VAT?

Shi wannan value-added tax VAT da aka kara a Nigeria daga 5% zuwa 7.2% tayaya yake aiki, shin karashi da akayi zai shafi talaka ko kuwa?

Akwai bukatar samun cikakken bayanin yadda yake da yadda yake shafar al'umma da kuma irin abun da zai iya faruwa bayan karashi da akayi.

Shin da aka kara VAT zuwa 7.2% me aka ce za'ayi da karin kudaden, sannan kafin a kara me akayi da 5% na baya da ake karba7??

Shin Malam Musa dake zuwa kasuwar Danbatta ya siyo kayan abuncin da zaici a gidansa, wannan karin VAT zai shafeshi ne ko kuwa sai masu zuwa Shoprite da manyan shaguna kawai zai shafa?

Na tsara Tambayoyin a haka, domin mu tattauna gaba daya, na tabbata baza'a kasa samun mutanen da ko kadan basu san taya VAT ke aiki ba?

A SANI

Nayi wannan rubutun a matsayina na Dan Nigeria, ba a matsayin Mai kare yan siyasa ba, burina kowa ya samu bayani akan abun da yake son yayi magana akai.

Dan APC da PDP ko APGA kai har da masu jam'iyya mai Alade kowa wannan sabon kari ya shafe shi, ba'a ware wasu ba.

Dan Allah, mu tattauna cikin sanin ya kamata da wayewa, ba tare da amfani da kalaman rashin girmamawa ko mutumtawa ba.

SHARHIN DAUDA B. ABUBAKAR AKAN VAT.

VAT yana nufin value added tax.

Harajine da mai sayan kaya (consumer) yake biyan gwamnati duk lokacin dayi cinikaiya  acikin ƙasar ta, shi wannan haraji ana biyanshi ne cikin kuɗin kayan daka saya ne.

Misali:

Kasayi buhun simintin Ɗangote ₦2500 kaso biyar na wannan kuɗin (₦125) zai tafine cikin Asusun gwamnati.

Tambaya.

1). Ta ya ya gwamnati kesa wannan haraji?

Mai kamfani ne kesa a dadin kuɗin haraji a cikin kayansa misali Ɗangote yayi kowane  buhu na siminti a kan kuɗi ₦2475.

Gwamnati na buƙatar Ɗangote yasa haraji na kaso biyar (5%) na kuɗin siminti.

Don haka idan ɗangote yatashi sai da simintinshi zai kama 2475 + 124= ₦2599, a kasuwa.

2. Ta ya ya kuɗin ke komawa hannun gwamnati?

Duk ƙarshen wata zai cika form in da zai gayama gwamnati adadin abinda ya saida sannan yayi remitting kuɗin (5%) gwamnati zuwa FIRS.

Haka shine ke faruwa ga duk kayan da ake kira vatable goods and services.

3. Yanzu mi zai faru tunda gwamnati ta ƙara VAT yakoma 7.2%?

Abinda wannan ke nufi kowanne company zai dinga chajin 7.2% mai makon 5%.

Ma'ana: Kowanne kayan da ake biyan VAT zai ƙaru da kashi 2.2%.

Kamar misali da na bada asama maimakon ₦2599 da Ɗangote ke saida siminti yanzu zai sai dashi ₦2475 + 178= ₦2653.

Karin Haraji

SHARHIN HARUNA BELLO AKAN VAT.

Kowacce irin gwamnati na samun kudi ne akasari ta hanyoyi uku.

Biyan haraji, ciyo bashi da kuma siyar da wasu ma'adanai da kasar ke dashi.

Kamar Nigeria ma'adanai da muke dashi har yake kawo mana kudin azo a gani shine danyen fetur. Yau an wayi gari idan muka siyar da danyen mai , bai Isa ya biya bukatun kasar ba, barrantana ayi ayyuka.

Daga duk VAT da ake karba, kashi 85% na zuwa jahohi da kananan hukumomi, a haka ana maganar jahohi da kyar ke iya rike Kansu saboda kudin dake shigo musu kusan sama da kashi 65 yana tafiya a biyan ma'aikata, yanzu idan aka ce su biya sabon minimum wage, tabbas da yawan su baza su iya biya ba, a wayi gari ana bautawa ma'aikatan gwamnati kadai wanda yawan su cikin al'umma bai wuce kashi 5 ba.

Mu duba budget na 2019, dole sai da gwamnati ta ciwo bashi domin funding manyan ayyuka, wanda  a aikin titi kawai Abuja-kano- da kuma akwanga- Jos- Gombe - Bauchi ya haura 500 Billions, banda sauran manyan ayyukan tituna a arewa da kuma sauran yankunan kasar.

A social programs support kawai irin su N-power, trader moni da sauran su shima wajen 500B ne.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KALLI YADDA ZA'A IYA MAGANIN KIDNAPPING DA SATAR MUTANE DAGA WAYOYIN HANNUN MU (SMARTPHONES)

Karanta Ma'anonin Sunayen Fullanci da Hausa

Karanta Abubuwan Mamakin da Suka Faru a Ranar Hausa Ta Duniya

Wanda tax zai taba jikin sa, shine wanda ke da manyan harkoki, amma kai ko ni mai zuwa siyan naman miya, tattasai, albasa, doya babu wani chanji mai girma da mutum zai gani. Allah ka tausaya ma kasar mu ta koma kan saiti Ameen.

Idan Kai/Ke kuna da karin Sharhi akan wannan makala ko wani abu wanda bai shafi wannan ba zaku iya tura mana kai tsaye a muryarhausa24@gmail.com

Mungode!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user