Thursday 29 August 2019

KALLI YADDA ZA'A IYA MAGANIN KIDNAPPING DA SATAR MUTANE DAGA WAYOYIN HANNUN MU (SMARTPHONES)

Tura Wannan Zuwa Ga
Da yawan mutane suna siyan wayoyin hannu ne ba don abunda wayoyin suka kunsa ba (facilities) sai don ado ko burgewa.


Wayoyin komai da ruwan ka


Marubuci: Mahmud Labaran Galadanchi

Wani har ya jima da wayar tasa baya iya sanin wata bukata ta musamman da wayar zata iya yi masa a al'amuran sa na yau da gobe.

Waya ta shafi dukkan wani bangare na rayuwar dan Adam har da tsaron rayuka da gujewa fadawa hadari kamar kidnapping.

Da yawan mutane suna amfani da applications na wayoyin su amma basu gama kewayewa da abubuwan da wannan applications zasu amfane su ba.

Wani zai iya tambayar kan sa ta yaya zan iya maganin kidnapping ko satar mutum ta hanyar amfani da wayar hannu? Wannan abu ne mai sauki kuma mai saukin ganewa. A yanzu mafi yawan masu amfani da wayoyi suna yin watsapp. Ta hanyar amfani da watsapp zaka iya maganin kidnapping ko da anyi kidnapping naka za'a iya gane a inda kake cikin sauki. Yadda zaka yi hakan shine:

1. Ka kunna "location" na wayar ka.

2. Ka shiga watsapp application ka zabi wanda kake so ka yiwa sharing location din.

3. A kasa, inda kake sharing hotuna zaka ga option na "location" sai ka shiga zaka ga yana detecting current location din kake a wannan lokacin. Bayan ya gama zai nuna maka unguwar da kake a map.

Daga nan kana da zabi guda biyu. Zaka iya sending current location din da kake ko kuma kayi sharing live location. Banbancin na farko da na biyun shine:

Sending current location: shine ka turawa wani inda kake a wannan Lokaci. Wannan zai taimaka idan aka kama mutum baa san inda yake ba. Idan ya turawa wani location din za'a gane wajen da yake ba tare da shan wahala ba.

Sharing live location: in ka zabi wannan kuma, duk wanda ka turawa wannan lokaction din zai rika ganin duk inda kake a map din. Misali ka taho daga Kano, sai ka yiwa wani sharing live location din ka a kaduna, duk inda kake yana gani a nasa map din kuma yana tracing din ka. Wannan zai taimaka shima wajen gane inda mutum yake. Zai fi taimakawa jami'an tsaro wajen sanin matakin da zasu dauka. Amma kai zaka fara taimakawa kan ka duk sanda zaka yi tafiya mai tsayi kayi sharing live location din ka da wani a wani garin don gudun faruwar wani abu mai kama da kidnapping.

DUBA WADANNAN:

Karanta Hanyoyi Mafi Sauki da Zaku Kare Facebook Account din Ku daga 'Yan Dandatsa (Hackers)

KARANTA SABON TSARIN DUNIYA KASHI NA FARKO (1) NEW WORLD ORDER

KARANTA YADDA YADUWAR HANYOYIN ALFASHA A YANAR GIZO SUKE HALLAKAR DA SAMARI DA MAGIDANTA


Ina fatan mutanen mu zasu fara amfani da wannan dabara.

Shi Watsapp ba wai iya chatting kawai ake ba harda irin wadannan muhimman al'amura wadanda suke taimakawa tsaron rayuwa da dukiyoyin al'umma.

Please a turawa yan uwa wanna sakon don kowa ya samu wanna idea din.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user