Monday 26 August 2019

Karanta Abubuwan Mamakin da Suka Faru a Ranar Hausa Ta Duniya

Tura Wannan Zuwa
A duk ranar 26 ga watan Agusta, rana ce da akaware saboda Hausa a Duniya. 

Farin Ciki da Ranar Hausa a Duniya

Saboda farin ciki da wannan rana a yau, yasa Muryar Husa24 ta kawo muku wasu daga cikin sharhin mabiyan mu akan wannan rana domin nuna farin cikin su da zagayowar wannan rana mai albarka.

Sharhin Bukar Mada

Wasu kalmomin Hausa masu ma'ana fiye da ɗaya.

1. RAMA

Rahamu ta taƙarƙare da cin ganyen RAMA kullum wai don ta yi maganin yunwar da ke sa RAMA, don ta ji an ce ramamme ba ya RAMA bugu.

2. KARA

Kallamu ya kora karsanarsa zuwa KARA domin ya sayar, a kan hanya ta ture wa Ali rumfar KARA da yakan kasa KARAn rake, da yake Ali mutum ne mai haƙuri da KARA sai ya yafe wa Kallamu.

3. KARE

Musa ya suri sandarsa da yake KARE da ita idan suna wasan karabkiya shi da Ja'e, ya nufi 'yan dangullan da yake kiwo a guje domin ya KARE su daga wani baƙin KARE da ya hango yana dafafen su yana yaƙe haƙora.

4. ZUBA

Kande takan so ta ZUBA wa Habu miya da tantakwashi, idan miyar ta kai masa karo, ya fara ZUBA mata labarin da babu waƙafi balle aya, tamkar bishiyar da ganyenta ke ZUBA lokacin hunturu, takan dube shi ta bushe da dariya.

5. TAFI

Lokacin da Inde ya TAFI gidan Sarkin Noma domin ya roƙoTAFI  uku na irin dawa sai ya jiyo matan gidan na daka suna TAFI da carabke.

6. RUGA

Audu ya RUGA da gudu yana dariyar ƙeta lokacin da ya wawushe sauran ɗanwaken da suke ci shi da Rabe ya RUGA shi duka a cikin baki, Rabe ya bi shi, suka yi ta guje-guje a cikin RUGA suka firgita zabi da kaji waɗanda suka haye saman damfami suna ta kwakwazo.

7. TUƘA

Kabiru ya TUƘA a-kori-kurarsa ya nufi siton Alhaji Audu Dankwangila domin ya ɗauko hatsin da za a TUƘA wa 'yan makaranta tuwo, a kan hanya ya wuce Garba a cikin rumfarsa yana TUƘA (tubka) igiyar da zai ɗaure ragonsa da ya ci ya ƙoshi yana ta faman TUƘA abin da ya ci.

8. KURA

Wata KURA da ta kubce babu takunkumi a cikin ƙauyen Magangari ta sa wani mutum ya yi watsi da ruwan da ya turo a KURA, garin gudu ya ture wani yaro da ke janye da KURA (mayen ƙarfe) yana kama ƙananan ƙarafunan da ke turbuɗe a cikin ƙasa.

9. CAJI

Sule ya kai batirin wayarsa wajen mai CAJI, lokacin da ya CAJI aljihunsa domin biyan kuɗin sai ya ji babu ko ƙarfanfana, nan take ya juya da sauri domin ya CAJI Ɗari da laifin lalube masa aljihu lokacin da suke kallon ƙwallo.

10. TURMI

Mani ya saɓi TURMI guda na atamfa daga cikin shagonsa, ya nufi ƙauye domin ya kai wa Inna ziyara, lokacin da ya isa sai ya tarar da ita tana daka magani a TURMI wanda Buba zai shafa a mummuƙe saboda haƙoransa, TURMI, da ya yi kogo yana masa ciwo.

DUBA WADANNAN:

Karanta Takaitaccen Tarihi akan Tushen Harshen Hausa da Al'ummar Hausawa

Ko Ka San Harufan Hausa Guda Nawa Ne?

Karanta Takaitaccen Tarihin Yaren Harshen Hausa

Ga kuma ƙarin wasu kalmomin, ko za a iya jaraba sanya kowace a cikin jimla tare da kawo dukkan ma'anoninta kamar yadda muka bayar da misali a sama? Kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Bisimillah!

Rago

Gara

Dama

Zage

Mari

Waya

Gari

Sara

Gado

Fara

Fito

Guga

Gora

Baiwa

Kwaɗo

Rina

Sa'a

Dawa

Duma

Taki

Dare

Baƙi

Kuɗi

Wuri

Wari

Taro

 Sharhin Shu'aibu Alkali


KANANCI–SAKKWATANCI

Eh–Awo wallah

Wannan–Wanga

Kuli-Kuli–Bakuru

Gyad'a–Gujjiya

Dankali–Kudaku

Bacci–Kwana

'Kofa–Garka

Gumi–Zuhwa

Ina kwana?–Kwal lahiya?

Miyar Kuka–Miyar 'Bakko/Kad'i

Zogala–TaMakka

Miyar Taushe–Miyar Sure

Me kace?–Mi kacce?

Gafiya–Burgu

'Bera–Kusu

Kyanwa–Mussa


Kana Bahaushe kana raina Hausa da Hausawa, har ma kana ganin cin darasin Hausa a makaranta ba wani abun a zo a gani ba ne. Bayan Mama da Baba da suka sa ka makarantar har ka yi wayewar da ta rude ka kake ganin Hausa da Hausawan ba abakin komai ba, babu Yaren da suka iya suke alfahari da shi sama da Hausar, ba su kuma da dangin da suka wuce Hausawan.
Alaji, sunanka Shagiri-girbau, sako-tumaki-ballo-jakkai.


RANAR HAUSA.

Gaskiya ce babu wasa, 
    Ta shige sak'o da  sassa,
              Ko'ina ta yad'a rassa,
                Duniya in dai ka dosa,
                    Za ka sam yare na Hausa.

Alfahar da zama Bahaushe,
   Hausa nan aka samu Baushe,
            Goro ko a kirashi Daushe,
              A miyar Hausa da Taushe,
                Wanda za'a hada da tuwo a kwasa.

Bahaushe ke da Hausa,
  Yai karin magana da Hausa,
        Yayyi zaurance da Hausa,
           Ko yama zambo da Hausa,
              Sai kwararre zai san ina ya dosa.

Hausa ne ke da kalamai,
    A rubuce kamar alamai,
      Sai a furtawa su zan mai,
         Masu banbanci kula mai,
            Ne d'ai zai san me suka k'unsa.

K'waro aka cewa Fara,
   Mai marar fata kwa Fara,
       Haka wani k'waro fa Gara,
          Wanda ke wawanci fa Gara,
                    Ka ji yare namu Hausa.

Sumar kai ce fa Gashi,
   In ka mik'a kuma Gashi,
     Tsuntsuwa kuma ke ta Tashi,
                Za ka mik'e kuma Tashi,
                    Kun fahimci ina na dosa.

To akwai bishiya ta Dashi,
    Masu tara kudi kwa Dashi,
           K'wace aka cewa Fashi,
             K'in zuwa makaranta Fashi,
                        Ba'a tsere mana gasa.

Kun sani da yawa irinsa,
       Na sani ko da a gasa,
         Ba'a tsere mana wasa,
           Matukar mun san irinsa,
              Ko da Jinn sai mun wucesa.


SABODA RANAR HAUSA.

Fadi sunan wadannan abubuwan da HAUSA;

1- Kwalba
2- Kwana
3- Duniya
4- Bokiti
5- Keke
6- Rashawa
7- Mota
8- Inji
9- Injin nika
10- Aljannah

Fadi ma'anar wadannan abubuwan;

1- Gafaka
2- Korami
3- Dumfama
4- Sakali
5- Kura tandu
6- Abawa
7- Laulawa
8- Nade da mai
9- Komaiya
10- Da6e

SHARHIN JAAFAR JAAFAR

Sunayen Igbo da Yarabawa da Turawa da sauran kabilu wandanda Hausawa suka canjawa launi.

1) Tope = Takwai
2) Kingsley = Kirsili
3) Gbenga = Biyanga
4) Ifreke = Cikurege
5) Ngozi = Ingozi
6) Nwankwo = Nawanko
7) Gbagyi = Gwari
8) Luggard = Lugga
9) Bordeaux = Bod'o
10) Awolowo = Awwalaho
11) Nnamdi = Namandi
12) Balat Hughes = Balatus
13) Taylor Woodrow = Tal'udu

Fita ta Biyu

Conductor = Kwandasta
Scrutiniser = Sakwaneza
Brake = Birki
Gear Box = Giyabos
Bumper = Bamba
Radiator = Lagireto
Carburator = Kafireto
Distributor = Disfuto
Coil = Kwayil
Valve = Bawul
Bearings = Boris
Rigs = Ringi
Plug = Fulogi
Crank Shaft = Karanshaf
Grand Overhaul = Garanbawul

Fita ta Uku

Ibadan = Badun
South West Nigeria = Kurmi
Port Harcourt = Fatakwal
Onitsha = Anacha
Africa = Afirka
America = Amurka
Turkey = Turkiyya
Istanbul = Santabul
Parsia = Fasha
Russia = Rasha
Germany = Jamus
Britain =  Birtaniya
Sierra Leone = Salo
Chad = Chadi
Cotonou = Kwatano
Port Lame = Fallomi
Yemen = Yamal
Israel = Isira'ila
China = Sin
Niamey = Yamai

Fita ta Hudu

Ford = Hodi
Bedford = Bilhodi
Mercedes = Marsandi
Peugeot = Fijo
Volkswagen = Besuwaja
Volkswagen Beetle = Ladi ba du wu
Fiat = Fet
Austin = Ostan-Ostan
Bus = Kiya-kiya (borrowed from Yoruba)
Station wagon = Dafa-duka
1973 Mercedes-Benz W114/W115 = Bagobira
1982 Toyota Corolla = Bana ba harka
Hatchback/coupe = ‘Yar kumbula
Long bus = Safa
Ten-wheel = Tangul
Mercedes 911 truck = Roka
Mercedes 1413-1414 truck = Bargazal
Mercedes 1312 (and similar sizes) truck = 'Yar Fakas
Max Diesel = 'Yar Rasha (Kirar Kurma)
Man Diesel (12-Wheeler) = Kwamanda
Truck with wooden body = Shorido
Hearse = Motar gawa
Towing van = Janwe
Tractor = Tantan
Trailer = Titiri
Pick-up van = A kori kura
Bulldozer = Katafila

DUBA WADANNAN:

Karanta Takaitaccen Tarihi akan Tushen Harshen Hausa da Al'ummar Hausawa

Ko Ka San Harufan Hausa Guda Nawa Ne?

Karanta Takaitaccen Tarihin Yaren Harshen Hausa


Bari na sauke wasu Karin Magana guda 35 da suke da Ma'anoni daban-daban, wadanda suke dauke da darussa, duk dai a cikin Yaren mu na Hausa wanda muke alfahari dashi, tunda yau ranar sa ce.

Kowa ya dauki wanda ya sani sannan ya fassara mana shi zuwa ainihin Ma'anar shi.

1. A rina, an saci zanen mahaukaciya.

2. A yi sha'ani, ɗanbirni ya cuci na ƙauye.

3. Abun dariya, kunkuru ya yi wa bushiya ƙafa.

4. Allah wadaran naka ya lalace, raƙumin dawa ya ga na gida.

5. Allah ya kawo baƙon da zai ci da ɗan gari.

6. An ce da ido wa ka raina? Ya ce wanda na ke gani yau da kullum.

7. Ana bikin duniya, ake na kiyama.
8. Ba cas, ba as.

9. Babban goro, sai magogin ƙarfe.

10. Bakin da Allah ya tsaga, ba zai hana shi abinci ba.

11. Ban ci nanin ba, nanin ba za ta ci ni ba.

12. Ban ga ta zama ba, an saci ɗan ɓarawo.

13. Ban sa a ka ba, in ji ɓarawon tagiya.

14. Baya ganin zalau, sai ya leƙa.

15. Cikina kwarkwaro, cikina tashiya.

16. Cil-da-cil, ganin annabin tsohuwa.

17. Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.

18. Da mai kama, ake ƙota.

19. Da sauran rina, a kaba.

20. Da wuya ta kashe ka, gwara/gwanda daɗi ya kashe.

21. Duk wanda ya samu rana, sai ya yi shanya.

22. Duniya rawar 'yanmata na gaba ya koma baya.

23. Fankam-fankam, bata kilishi.

24. Faɗan da ya fi ƙarfinka, mai da shi wasa.

25. Ga bikin zuwa, babu zanin daurawa.

26. Ga fili, ga mai doki.

27. Gaba kura, baya siyaki.

28. Gaba ta kai ni, gobarar titi.

29. Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah.

30. Garaje, ga dami.

31. Guntun goro, ya fi babban dutse.

32. Gurin da ba ƙasa, nan ake gardamar kokawa.

33. Haka ma arziƙi ne, ka yi baƙo ya kashe ka.

34. Idan ba a yi sharar masallaci ba, a yi ta kasuwa.

35. Idan gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta, shafawa naka ruwa.

Ranar Hausa ta Duniya



Yau 26 ga wata itace ranar Hausa ta duniya.
"Ina fatan matasa kada kuyi koyi da masu zuciya kamar Kunkuniya, domin suna nan a kowace kwarkwad'a da surkuki suna nufi kowa ya zam samma kal dasu, fatan mu shine qardajiya tayi ajalin su".

Wasu matasan a yau basu jin Hausa ko na sanqiyar bacci, koda yake dama a yau Hausa dodar sai Wanda yaci, ya sha, ya qoshi kuma yayi gyatsa da Hausa ne zai yi ta, acigaba da Koyon Hausa matasa a hankali a hankali wata ran Matankadi zai shiga Buta".

Ina masu yawan rubutu a Media? toh ga sako gare ku, daga Abdulhadi Isah Ibrahim.
Tunda ance yau ranar Hausa ce, ina so nayi mana gyara musamman mu masu yawan rubutu a Media, kura-kuran da ake yawan yi a rubutun Hausa a social media, na zabo guda 4 nayi magana akai.....

1. Duk inda zaka rubuta sunan gari, ko sunan mutum, dabba ko wuri ko mukami, ba'a rubuta farkon sa da small later, misali sai kaga mutum ya rubuta (abuja, kano, nigeria) kuskure ne hakan, duk wanda ya gani zai ce har yanzu da sauran ka, kuma mutane baza su rinka damuwa da posting din ka ba in kayi.

Sannan abu na biyu, majority din masu rubutu a social media suna da 'karancin sanin yanda ake rubutu da Hausa a tsarin da kowa zai gane, ta yanda suke hade kalmomin da ba'a hada su, misali sai kaga mutum ya rubuta (kasarmu) madadin ya bayar da space (Kasar mu), ko kuma kaga mutum ya rubuta (iyayensa) madadin (iyayen sa) da space.

Saboda kalmar (iyaye) kalma ce mai cin gashin kan ta, haka kalmar (sa) ko (shi) kalma ce ta daban, dan haka ba'a hada su, kamar a Turanci ne ka rubuta (myname is Abdullahi) is wrong, dole ka rabe (My name...) kar kazo rubutu ka rubuta (garinmu) sai dai (garin mu), sai mu gyara, haka kuma kuskure ne ka rubuta (rubutunsa) dole ka sanya space (rubutun sa) saboda kalmomi ne guda biyu, kwararrun masana Hausa basa hade su.

3. Sannan a rubutun Hausa akwai kalmomin da biyu ne amma ya halatta ka hade su a rubutun ka, misali (kazo) ko kuma (mune) babu laifi, saboda wani lokacin idan ka rabe zai bada wata ma'ana ta daban, misali (kayi?) ko da Turanci "You do?" kaga a Hausa kalmar (Ka) daban ce, kalmar (yi) daban ce, amma duk da haka masana rubutun Hausa sun ce ya halatta ka hade su, amma a Turanci kuskure ne ka rubuta (youdo?).

Akwai kalmomin da biyu ne amma ana iya hada su, a Hausa da Turanci, misali (tazo) "She came", kaga kalmar (ta) kalma ce ta daban, (zo) kalma ce ta daban, amma zaka iya hade su, ko kuma a turanci (myself) kaga kalmomi biyu ne (My) da (self) amma sai aka ce ya halatta hade su ka rubuta (myself), abu na 'karshe.

4. Sannan duk wurin da numfashi yake tsayawa a magana to ana saka masa Comma idan a rubutu ne, haka kuma duk wurin da zance ya cika ana sanya comma, kuskure ne ka rubuta (Hajiya ta dawo jiya har tazo da tsaraba) akwai comma (Hajiya ta dawo jiya, har tazo da tsaraba).

Wannan wasu ne daga cikin abubuwan da ya dace duk wanda zai rubutu da Hausa ya lura dasu kuma yayi aiki dasu, nagode.

Ranar Hausa, Hausa ba dabo ba dabara.

Tsinstiya, tsageranci, tsiya, tsagewa, tsaki, tsaga, tsakiya, tsiwa, tsunkunu, tsokaci, tsurku, tsaka, tsafta, tsamiya, tsada, tsaada, tsiri, tsira, tsirara, tsaigaitawa, tsawaitawa, tsanani, tsantseni, tsamewa, tsammani, tsohuwa, tsoho, tsotsa, tsanantawa, tsatstsafi, tsaro, tsaba, tsibi, tsabarage, tsimi, tsumuwa, tsire, Tsula,tsari,Tsiya,tsumi, Tsutsa, tsula, tsanya, tsando, tsinuwa, tsiya, Tsire, tsatso, tsimaya, Tsani, tsatsuba, tsimi, tsagwaro, Tsibiri, tsunke, tsuma, tsarguwa, tsangaya, Tsada, Tsafi, tsanewa.

Wasu daga cikin sunayen Hausawa na asali.
Garba, Mati, Lado, Tanko, jatau, Nomau, Shagari, Babangida, Asabe, Mudi, kande, kuluwa, Biba, Fatu, Audu, Dan tani, Larai, Talatu, Laraba, iya, Marka, Shatu, A'ille, Iro, Ubale, Uwani, Dan Asabe, Tukur, Ilu, Habulle, Tine, Assibi, Gambo, Jummai, Talle, Datti, Tani.


Ranar Hausa ta Duniya a shekarar da ta Gaba ta a dauki hotan.


DUBA WADANNAN:

Karanta Takaitaccen Tarihi akan Tushen Harshen Hausa da Al'ummar Hausawa

Ko Ka San Harufan Hausa Guda Nawa Ne?

Karanta Takaitaccen Tarihin Yaren Harshen Hausa


YAU CE RANAR HAUSA TA DUNIYA... KAWO MANA KARIN MAGANA GUDA DAYA DA HAUSA.

In ka ji mutum yana tsoro dare ba a ‘daure shi ya kwance ba.

Albasa ba ta halin ‘kasa, da ba ta yi yaji ba.
Maraya ba ya shakkar mutuwar uwar wani.

Ba’kon munafuki ba na mutum ‘daya ba ne
An san biri yana da wuya a kan ‘daure shi a gindi.

Ma’kiyinka ba shi yabonka ko da ka kama damisa ka ba shi.

Gudu da waiwaya shi ya kawo mugun zato.
Wanda za a kashe don an karairaya shi ba kome

An ce da akuya Sarkin Fawa ya mutu, ta ce, “Oho, ya mutu da wu’kar yanka ne ?”

Barawon da ba a gani ba sunansa mamman.

Abin da wancan ya ce shi na ce, kirarin mai tsoro.

Barawon kakaki, ba shi da ikon ya busa shi.
Wai an ce da jaki falke zai shiga aljanna, ya ce “Im ba ni nan kusa ba ?

Ina zan zauna, matsegunci ya je kasuwa.

Izza na Kano, sarauta na Sakkwato, ya’ki na Zariya, karin magana na Bauchi

Kowa ya hana ka ‘dakin kwana, da safe sai ya ganka.

Gurgu yana gani a kan sari sanda a buge shi.

KOWA YA KAWO NASA GUDA DAYA... 

DOMIN JIN DADIJ RANAR HAUSAWA TA DUNIYA.

SHARHIN RABI'U BIYORA

Kishingide nake a shigifa bisa karauni, ina nazarin wannan sarari da muke rayuwa cikinsa, tsam na mike na fito na haye laulawa jikina sanye da riga Kwakwata da wando tsala, na saka kafafuna cikin takalmi fade, unguwar gangare na nufa gidan , Malam Alto wamzami don ya sassabe mun sumar dana tara, bayan nayi sallama Alto Wanzami ya fito ratyae da Zabira a kafadarsa.

Bayan ya zauna sai ya fito da kayayyakin aikin nasa, Koshiya ya fara daukowa, sai yar tsaga da Aska, Mawashi da isga sai kuma kaho, daganan ya sassabemun suma kamar yadda na bukata....

TAMBAYA GAMU HAUSAWA DA MASU AMFANI DA YAREN HAUSA....

A wannan rana da ake bukin Harshen Hausa a Duniya, ya kamata musan asalin sunayen wadannan abubuwan....

Mota
Jirgin Sama
Babur
Keke
Bokiti
Television
Radio
Fanka/fans
Titin Mota
Telephone

Zaka iya karawa da sunayen wasu abubuwan daka sani nasu na asalin Hausa....

Tattaunawa cikin shakatawa don taya juna murnar ranar Hausa ta Duniya......

Ranar Hausa ta Duniya



SHI BA BAHAUSHE BA KUMA SHI BA BATURE BA, HAKA KAWAI KA ARI ABIN DA BA NAKA BA KACE DOLE NE SAI YA ZAMA NAKA? SUMA FA MASU WANNAN YAREN (ENGLISH) SUN MAYAR DA HANKALI AKAN GINA YAREN NASU WANDA A YAU HAR YAKAI MATSAYIN DA YAKE KAI.

ME NE NE YASA KAI MA BAZAKA BAYAR DA GUDUNMAWAR KA WAJEN CI GABAN HARSHEN KA BA?

AKWAI HANYOYI DA YAWA DA ZAKA IYA BAYAR DA GUDUNMAWAR KA, IDAN KANA DA SHA'AWAR HARKAR RUBUCE-RUBUCE KAYI AMFANI DA DANDALIN SADA ZUMUNCI DA MUSAYAN RA'AYI (FACEBOOK) KO KUMA (TWITTER, WHATSAPP, YOUTUBE, INSTAGRAM DA SAURAN SU) IDAN KANA DA DAMA ZAKA IYA TAIMAKAWA WAJEN BUDE WEBSITE/BLOG DOMIN BAYAR DA TAKA GUDUNMAWAR.

SUMA FA YAREN NAN (ENGLISH) DA KAKE GANIN KOMAI AKE NEMA A NET ZAKA SAMU MATUKAR DA ENGLISH KA BINCIKA BASU NEMI TAIMAKON KOWA BA WAJEN GINA SHI A NET.

ME YASA KAI MA BAZAKA YI AMFANI DA ILIMI DA BASIRAR D ALLAH (SWT) YA BAKA WAJEN GANIN YAREN NAMU YAKAI WANI MATAKI ANAN GABA BA? 

KOWANNEN MU YANA DA IRIN BAIWAR DA ALLAH YAYI MASA TA WANI BATAYI KAMA DA TA WANI BA, HAKA ZALIKA ABIN DA WANI ZAI YI WANI KO TIRILIYAN AKA BASHI ACE YAYI BAZAI IYA BA (KAMAR MISALIN MACE MAI CIKI CE) NAMIJI BAZAI IYA HAIHUWA BA, SABODA ALLAH BAIYI MASA MAHAIFAR DA ZAI IYA HAIHUWA BA.

TO HAKA MISALIN BAIWA TAKE KOWA DA KALAR TASHI BAIWAR.

DAN UWA NA, AKWAI HANYOYI DA YAWA DA ZAKA IYA TAIMAKAWA WAJEN GANIN AN GINA YAREN HAUSA A WANNAN KAFA TA ZAMANI WANDA A HALIN YANZU KUSAN ZAMU IYA CEWA , ANFI MAYAR DA HANKALI WAJEN BINCIKE DA KARANCE-KARANCE A WANNAN KAFA (YANAR GIZO) FIYE DA YADDA AKE BINCIKE A LITTATTAFAI KO KUMA DAKIN KARATU.

INA DA BURI DA FATA NA GANIN HARSHEN HAUSA YA WANZU A DUK SASSAN DUNIYA BA YANKIN AFRICA KAWAI BA , DUNIYA GABA DAYA NAKE DA BURIN GANIN HARSHEN YA SAMU SHIGA KOWANNE LUNGU DA SAKO INSHA ALLAH.

DAFATAN ZA'AYI MIN UZIRI NA RASHIN AIKO DA SAKO DA KUMA FARIN CIKI NA ZAGAYOWAR RANAR HAUSA TA DUNIYA, HAKAN YA FARU NE SABODA WANI DALILI.

ALLAH YA SA MU DA CE AMIN.


Rayuwa!

‘Salamu alaikum ko mutan gidan na ciki?’

Sallama ce daga waje.

‘Wa’alaikumus salam,’ yaro ne dan shekara 8 ya amsa mata.

Ta shigo cikin falon, ta yi tsaye da ta ga yaro ba ko riga yana kallon ta.

‘A’aaaha, ba kowa ne a cikin gidan, sai kai?’

‘Akwai kowa mana, ko ni ba kowa ba ne halan?’ Ya fada cikin yarinta.

‘Yi hakuri, ni ba baka na ce ka fada mini ba, daga tambaya!

‘Ai, akwai magana fara ne da kike batun baka? Abar dai zancen, duk sun fita, sun bar ni tsaron gida ne.’

‘Don Allah rufe man baki da yawan surutu, ta yaya kamar ka zai tsare gida in ba hauka ba.’

‘Hauka? Ta yaya yaro kamana zai yi hauka, cewa nake yi sai manya ko  ma’aikatan gwamnati ke yin hauka?’

Cikin mamaki ta ce da shi, ‘yaya kake ce da ma’akaitan gwamnati mahaukata?’

‘Haka na ji Baba na fada. Yana cewa ai mai aikin gwamnati shi ne mahaukaci yau a Nijeriya. Domin kuwa ba yadda za a yi idan ba hauka ba, mutum ya amshi albashin dubu talatin a wata, alhali shi yana bukatar dubu sittin ya ciyar da iyalinsa, ya yi mirsisi ya ce Allah ya kyauta,’ in ji Baba.

‘Ban gane ba, me Babanka ke nufi?’

‘Bari na yi maki Gwari-Gwari. Cewa yake yi hauka ne ka amshi albashin da ka san ba zai ci da iyalinka ba, a kuma zauna lafiya!’

‘Ta yaya mutum zai zama mai hankali idan da kai ne za ka yi bayanin da kyau,’ ta fada, ta kuma nemi wuri ta rashe.

‘Ai da in zama mahaukaci, gara in zama barawo!’ Ya ce da ita.

‘Haba kai ko, ta yaya za ka ce haka, barawo ai ba mutum ba ne.’

‘Shi ko mahaukaci fa, mutum ne? Ya tambaye ta.

‘Mutum ne mana, me kake nufi?’

‘Wallahi ni dai ban amsar abin da na san bai ciyar da iyalina domin in bauta wa gwamnati.’

‘Kai kuwa dana ai ba bauta ba ce, ba ka ganin cewa abin da ya dace a biya ka ke nan?’

‘Rabin hakkina a wata shi ne biya na? To ko ke ma kin soma irin nasu haukan ne?’

‘Ashe ba ka da kunya, ni kake ce wa mahaukaciya?’ Ta fada cikin kakkausar murya.

‘Allah ya huci zuciyarki, ba haka nake nufi ba. Amma don Allah ki fada mani gaskiya ke ma ma’aikaciyar gwamnati ce ko?’

‘Ehhh, ita ce, sai me?’ Ta fada a fusace.

‘A’a, ba komi’, ya fada cikin guna-guni.

‘Don Allah ka bayyana mini man, ba zan sake yin fushi da kai ba.’

‘To shi ke nan. Na san dai kin zo wurin Mama ne ki roki sauran garin kwaki, to mu ma Baba ya jefa tiyar garin da ta rage cikin wata bakar leda, ya sa kirtani ya daure, ya dauki bakar ledar ya sa cikin wani kwanon sha, ya rufe, ya sa bisa silin din dakinsa ya boye!’

‘Saboda me?’ Ta ce da shi cikin mamaki.

‘Ai haka Baba yake yi duk tsakiyar wata, yana cewa ba a kara shan gari sai wata ya kusa karewa’.

‘Haba sai ka ce mahaukaci?’

‘Mahaukaci!’ Ya ce da ita.

‘Me ka ce?’

‘Na ce mahaukaci!’

‘Baban naka kake ce da shi mahaukaci?’

‘Yo ba ke kika ce in ce ba!’

‘To mu manta da wannan batun, ni ba garin kwaki na zo bida ba, dama ina son ku ‘yan mani ruwa ne, ba mu da ko tarfi a gidan, tun jiya da dare.’

‘Ai abin da nake gaya maki ke nan tun dazu. Ba kowa gidan, yayyena sun tafi bakin kasuwa inda famfon ya fashe, su gani ko za su kwakulo mana jarka guda, tun dazu ba su dawo ba.’

‘Ku ma naku famfon ya lalace ne?’ Ta ce da shi.

‘Ko alama, Mama cewa take a kullum, famfon namu gara babu da shi, domin kuwa rabon da ruwa ya digo daga jikin famfon tun kafin a yi yayen ‘Yar lele, yau kusan wata shida ke nan.’

‘Ita Babar taku ina ta tafi?’

‘Ta leka wajen masu nikan masara ne ta ga me ya faru. Domin tun da safe ta aiki wana Kabir kai nika har yanzu ba su dawo ba?’

‘Ko ka san abin da ya hana Kabir dawowa da nikan?’

‘Na sani mana. Na gaya wa Mama kada ma ta damu kan ta, ba zai sami nikan ba sai da magariba, ta ki saurare na, ni kuma na kyale ta.’

‘Amma kai ko, ai dole ta bi shi saboda a sami garin da za a yi muku tuwon dare.’

‘Lallai haka ne. Amma ai abin da ba ta sani ba shi ne NEPA ba za ta kawo wuta ba sai da kusan magariba, a lokacin kuma Mushirikat ta tafi coci, ba kuma za su daina wake-waken da raye – rayen ba sai wajen takwas na dare. To ina amfanin bin yaya da ta yi?’

‘Ka sani ko tana son su kai nikan wajen injin ruwa ne!’

‘Uhum, ai injin ruwa daya ne kurum a unguwar. Kuma tun jiya na ji Iya Tawakaltu tana ce da Tawa, ta gaya wa mahaifinsu in ya dawo daga gareji ta tafi dauko injin din da ta kai gyara can kara, ba kuma za ta dawo ba sai gobe da safe.’

‘Kai ko wai yaya aka yi ka yi wayo haka?’

‘Ba wayo ba ne, rayuwa ce!’

‘Ban gane ba, wata makaranta ce kake zuwa ta rayuwa?’

Ya yi murmushi, ‘ai ko makarantar ma ban shiga ba!’

‘Me ya hana?’

‘Baba ya hana!’

‘Don Allah ka daina yi wa iyayenka karya, me zai hana su sa ka makaranta kai kuwa?’

‘Da wane kudin za su sa ni? Imam, babban wana na jami’a. Maijidda, mai bi masa na kwaleji. Isa da ke biye da ita, na firamare.

A kowane zangon karatu Baba na bukatar sama da Naira dubu 90 ya biya musu kudin makaranta. Saboda haka ya ce ni in dan huta kafin wani lokaci. Shekara biyu ke nan ina hutawa.’

‘Haba yaro ya za a yi a kasa biya maka kudin makaranta saboda ‘yan uwanka na karatu?’

‘Hala dai ba ki yi makaranta ba ne?’

‘Me ya sa ka ce haka?’

‘Idan aka tara dubu 30 sau uku, nawa ke nan?’

‘Dubu 90!’ Ta ce da shi.

‘A kowane zangon karatu wata nawa ne, in ce uku?’ Bai jira ta amsa ba, ya ci gaba, ‘kin manta cewa albashin Baba dubu 30 ne kowane wata?’

‘To shi Baban naka bai iya yin komi ya samu kudin da zai cikasa ya sa ka makaranta?’

‘Yana iyawa!’

‘To me ya hana shi?’

‘Ban sani ba!’

‘Haba, yaro mai wayo kamar ka zai ce bai sani?

Don Allah gaya man hanyar da zai bi ya taimake ku.’

‘Hanya daya ce,’ ya fada da ajiyar zuciya.
‘Wace ce?’

‘Ya yi sata.’

Ta yi zambur ta mike tsaye. ‘Sata, haba dana, sata fa ka ce!’

Yana mamaki, ya ce da ita, ‘to laifi ne yin satar?’

‘Laifi ne mana!’

‘In laifi ne shi ne na yi ta gani a talbijin an nuno buhunan Gana-Mus-Go a majalisar Dattijai da ta Wakilai ana cewa daga ofishin Shugaban kasa ne, wai an aiko musu da cin hanci?’

Ta yi shiru.

‘Me ya same ki, na ji kin yi shiru?’

Ba ta amsa ba!

‘Kukan me kike, cinnaka ne ya cije ki, na ga kina zubar da hawaye?’

Ta sa hannu ta share hawaye da habar zanenta, ta ce ‘ba komi, kana ba ni tausayi ne kurum.’

‘In don ni ne kada ma ki damu kan ki, ba abin da zai same ni, domin Babana ya ce mu yara ba abin da zai same mu daga mahaukaciyar gwamnatin kasar nan.’

‘Wai wa ke koya maka irin wadannan miyagun kalamai haka?’

‘Babana!’

‘Shi ke koya maka zagi da bakaken maganganu irin wadannan?’

‘Ehh mana. Na ce maki ni ba na ko zuwa makaranta balle ki ce can na koyo. Rayuwa ce kurum! Idan ma kika ji yadda Baba ke bayani, ai ni ba komi nake cewa ba. Jiya na ji yana cewa ai shi bai ki duniyar ta watse ba. Yana cewa in ma an ga dama a yi tashin kiyama, yau ko gobe. Haka kuma na ji yana ta fadar bai taba ganin shegun shugabanni irin namu ba. Yana karawa da cewa bai taba ganin mugaye, macuta, mamugunta, azzalumai ba irin masu kudinmu. Da na ce da shi Baba ta yaya kake neman a yi tashin kiyama a halin yanzu, me ya yi zafi….’

Nan take ta katse masa hanzari ta ce da shi, ‘kai amma ana cikin matsalaloli a kasar nan.’

‘A’a, ba a cikin matsaloli, mu tamu matsala daya ce kurum!’ Ya ce da ita!

‘Wace ce?’

‘Yunwa!’

‘Shi ke nan?’

‘To kila talauci!’

‘Talauci?’ Ta tambaye shi.

‘Rashin boza mana, ko ba ki san wannan ba? Fatara. Rashin naira!

Ni ban san wannan ba!’

‘Karya kike yi wallahi?’

‘Kai dan abin uwar nan…. ni kake karyatawa!’

‘Ni ban karyata ki ba. Ba kuma ni na fada ba, Baba ne ya ce duk wanda ya ce bai san talauci a kasar nan ba, to mahaukaci ne ko kuma makaryaci?’

‘Me ya sa Babanka ke bayyana maka wadannan abubuwa marasa dadin ji da kuma ban takaici?’

‘Cewa yake saboda idan na girma ba zan hadu da matsaloli a rayuwa ba.’

‘Me zai faru gare ka in ka girma? Me yake hange?’

‘Matsaloli!’

‘To ai yana nan raye zai iya taimakon ka ko!

‘Ya ce kafin ya mutu zan san hanyoyin magance matsalolin rayuwa.’

‘Me zai sa ya mutu?’

‘Matsalolin rayuwa mana!’ Fashi da makami. Sace-sacen mutane. Karuwanci da zina da madigo. Kashe mutane da yankar kai da kuma hadama da babakere. Kai ga su nan bilahaddin…. 

Ta yi ajiyar zuciya, sa’annan ya ji tana cewa,‘ Allah ya isa, Allah ya tsine. Allah wadarai. Allah ka fatattaka wadannan musu bata mana rayuwa da ta yara irin wannan. Allah ka sa su shiga cikin kunci da muke ciki, ko ma nasu ya fi haka. Allah, idan masu gyaruwa ne ka gyara su, idan ko ba masu gyaruwa ba ne, Allah ka kashe su, ka kashe su na ce!’

‘Me ya sa kike irin wadannan miyagun maganganu ke ma, ko kina zuwa makarantarmu ne?’ Ya ce da ita.

‘Wace?’

‘Ta rayuwa!’

Ba ta amsa masa ba.

‘Shegu!’ Ta fada cikin kakkausar murya.
Ya fashe dariya, ‘ke ma kin soma magana irin ta Baba.’

‘Allah ya isa! Ai ni wallahi da zan ga inda aka ajiye kahon nan, wallahi da na dauko shi na hura shi yanzu-yanzu, kowa ya huta. Takadarun azzalumai kawai!’

Ta mike za ta wuce, ta ce da shi, ‘ka gaya wa Mamanka cewa na leko, idan kuma ta rage tuwon jiya ta aiko ka da shi, domin yaran gidana tun safe rabon su da su jefa wani abu a uwar hanjinsu.

‘To za ta ji.’ Ta fice. Shi kuma ya yi zaune zugudum, yana magana a hankali, ‘ ka ji maras hankali ko. To ta aiko maki da sauran tuwo, mu kuma mu ci me?’


MALAM BAHAUSHE A JIYA DA YAU!!!

Bahaushen jiya.

Yana da  Riqo da addininsa
Yana da tsarin shugabancin sa mai kyau na sarakunan gargajiya.

Yana da matukar riqo da Harshensa da Al'adunsa na usuli.

Bahaushen jiya baiyarda da zaman banza ba da mutuwar zuciya ba shiyasa zaka magidanci yana Noma ko kasuwanci, a gidansa kuma zaka samu akwai garke na awaki ana kiwo, matansa kuma zakaga akwai aikin dasuke agida na dogaro dakansu irinsu niqa, chasa d.s
Bahaushen jiya keda matuka wajen taimakon junansa misali idan andawo daga wajen sana'a za afito da abinci daga gida ahadu guri daya aci, idan wani yaga dan wani yayi laifi to zai hukunta shi kuma axo har gida ai masa godiya.

Ranar Hausa ta Duniya

Bahushen yau.

I'm sorry to say to the extend bahaushen yanxu ya gurbace tako ina compare to asalin bahushen jiya. Hujja ta ita ce,
Bahaushen yau ya zubarda yawancin al'adaunsa kyawawa yana ganinsu a matsayin qauyenci.

Bahaushen yau bai dauki addininsa da muhimmanci ba a aikace sai a baki kawai.
Hassada, kyashi, mugunta, son kai da zunzurutun jahilci ya samu babban muhali a zukatan hausawan yau sai wadanda Allah ya tsare kawai.

Mafita ga bahaushen yau.

1. Ni bahaushe in yarda banda Yaren dayafi Hausa.

2. Yin watsi da bakin al'adu na aro da dabbaka namu na usul.

3. Bibiyar tarihin magabata da koyi da yanda sukai rayuwansu.

4. Yin cikakken ilimin Addini dakuma aiwatar da karatun a aikace.

Yau take Ranar Hausa ta duniya.


RANAR HAUSA,

Aci ba'a siyar ba kaza tafi doki

Ranar hausa

Duk daya ne akace da makafi sunyi dare

Ranar Hausa

Duk tsawonka kujerar gwamna tafi ka tsayi

Ranar hausa

Abinda kamar wuya wai raba talaka da buhari

Ranar hausa

cin moriyar jaki nisan kwana,

Ranar Hausa

Yau da gobe kesa a mari suruka

Ranar Hausa

kuturu da kudinsa alkaki saina kasan kwano

Ranar Hausa

A bari ya huce shike kawo rabon wani 

Ranar Hausa

me rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi sai ya gani

Ranar Hausa

Abin rabo ne kuturu ya kama tarwada

Ranar hausa

Alhamdulillah!!! a cikin waɗannan sharhin da MURYAR HAUSA24 ta kawo muku daga wasu mabiyan mu , sharhin waye yafi birge Ka/Ki kuma yafi daukar hankalin Ka/Ki?

Zaku iya yin sharhi a ƙasan wannan maƙala ko kuma ku turo mana da shrhin ku a akwatin aika saƙo na imel a muryarhausa24@gmail.com zamuyi farin ciki da samun saƙon Ka/Ki Mungode!

Muryar Hausa24 muna yiwa dukkan al'ummar Hausa Barka da Wannan rana dafatan za'asha shagulgulan bikin wannan rana lafiya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user