Sunday 19 May 2019

Ko Ka San: Harufan Hausa Guda Nawa Ne?

Tura Wannan Zuwa Ga
Harafi suna ne da ya haɗe baƙaƙe da
wasula. Wato kenan kowanne baƙi harafi ne, haka kuma kowanne wasali harafi ne.







Ga harufan Hausa kamar haka:


     Tilon Harufa:


Aa Bb Cc Dd Ee Ff (Pp) Gg Hh Ii Jj Kk Ll Mm Nn Oo Rr Ss Tt Uu Ww Yy Zz.


     Tilon Harufa Masu Lanƙwasa:


1. Ɓ ɓ
2. Ɗ ɗ
3. Q ƙ


     Tagwan Harufa:


1. AI ai
2. AU au
3. FY fy
4. GW gw
5. GY gy
6. KW kw
7. KY ky
8. QW ƙw
9. QY ƙy
10. SH sh
11. TS ts
12. UI ui
13. ‘Y ‘y


     Waɗannan harufa su ne kaɗai ake
amfani da su wajen rubuta duk wata
kalma ta Hausa.


     Wasulan Hausa:

a, e, i, o, u, ai, au, ui.

LURA:


Harafin (Pp) a Hausa, ana amfani da shi ne kawai yayin rubuta zanannen suna, irin su Panshekara, ko Mustapha, ko Sipikin da sauransu.

A cikin wannan rubutu mun yi amfani da salon rubutu na RABIAT (wato wasula masu lanƙwasa). Za ka iya ganin harufan sun zo da sigar wasu harufan Ingilishi, idan na'urarka ba ta iya karanta harufan na Hausa, wato ɓ da ɗ da ƙ. Sannan kuma akwai buƙatar mu fahimci cewa, harufan Vv da Xx da Qq harufan harshen Ingilishi ne ba na Hausa ba, ba mu da waɗannan a cikin harufan daidaitacciyar Hausa.


MURYAR HAUSA24


Shafin Komai da Ruwanka. 

Muryarhausa24.com.ng muna yin aiki tukuru don jin dadinku.

Isar da bayanai a kan lokaci ba tare da son zuciya ba, shi ne muradinmu.

Burin shafin Muryarhausa24 shi ne, ta fito da kyawawan manufofi, tsari, nagartar masu jin harshen Hausa a dukkan fadin Nijeriya da kasashen da suke makwabtaka da ita, kuma ta hada kan masu jin harshen Hausa waje ɗaya a ko ina suke a fadin duniya.

Domin samun Labarai, da Nishaɗi, da Kalaman Soyayyar Hausa, da Bincike mai zurfi, da Tarihi, da Fadakarwa, da Tunatarwa, da Addu'o'in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, da Kimiya da Fasaha, da Hotuna, da Hausa Kwamedi, da Sababbi da Tsofaffin Wakokin Hausa na-ji da bidiyoyi, da Labarin Fina-finan Hausa Na Kannywood, da Labaran Bollywood, da Labarin Wasanni, da Garabasar Kira da Hawa Yanar gizo-gizo, da Ilmantarwa Tare da sharhi mai gamsarwa, da Tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su, ku cigaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda ku ka kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya, na bada labarai da suka hada da harkokin yau da kullum, da zummar samar da zaman lafiya da kuma daukaka kima da martabar al’adun Hausa.

Za ku iya aiko mana da labari ko shawarwari, ko ra'ayoyinku ko kuma nuna gamsuwarku a kan yadda muke tafiyar da wannan shafi mai albarka.

Aika saƙon ka/ki a kan adireshinmu na yanar gizo-gizo muryarhausa24@gmail.com  Za mu yi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mun gode.

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

Sunana Abba Muhammad Sagir wanda aka fi sani da Abba Danhausa. Ina son harshen Hausa sosai, kuma ina da sha'awar yin rubuce-rubuce a cikinsa. Burina a ko da yaushe kawo wa harshen Hausa ci gaba ta fannoni daban-daban na rayuwa, tare da ganin ya bunkasa, ya wuce inda yake a yau. Wannan shafin na bude shi ne domin kare martabar harshen Hausa, da ciyar da al'ummar Hausawa gaba da sauran masu ji da magana da harshen Hausa ta hanyar yin la'akari da harshe da adabi da al'adun Hausawa. 07038838301.