Showing posts with label KASUWANCI. Show all posts
Showing posts with label KASUWANCI. Show all posts

Sunday, 19 July 2020

Shin Ko Kasan Abinda Zai Faru Da Wanda Yake Cin Bashi Amma Baya Biya?

Shin Ko Kasan Abinda Zai Faru Da Wanda Yake Cin Bashi Amma Baya Biya?

Wasu mutanen sun mayar da cinye bashin da suka karɓa na kuɗi ko makamancinsa hanyar biyan buƙatunsu na rayuwa ta yadda in hulɗar kuɗi ta haɗa ka da su sai dai ka yi haƙuri ko ka nuna babu mutumci, in suka karɓi aron kuɗi ko wani abu a madadinsa ba za su biya ba, ban da rashin tausayi ba su biya abin da ake bin su a baya ba sai su zo da sunan a ƙara musu wani bashin za su haɗa su biya, kai jama'a!

KIN BIYAN BASHI BABBAN BALA'I NE!

MarubuciAbbati Mai Shago Flg

Wasu kuwa ba sa jin tsoron cinye ƙananan kuɗaɗen da aka biyo su ta hanyar siyayyar da suka yi ko siyayyar da aka yi a wajensu, in aka biyo su wani kuɗi sai a amince musu da sunan  za su bayar saboda mutumcinsu da ake gani, ashe ba haka abin yake ba sai su yi fuska su ƙi biya. Matsalar nan ma ba ta taƙaita ga manya kaɗai ba har zuwa yara; abin ban haushi sai ka jawo yara jikinka da sunan koya musu sana'a wacce za su riƙa samun kuɗin shiga tun kafin su girma ƙarshe sai su cuce ka.

Wasu manyan cuta a kan kuɗi haka ma wasu yaran, wannan ya sa tsoro ya shiga zuciyar masu abin hannu a kan in suka ɗora wasu a kan dukiyarsu za su wulaƙanta musu ita, hakan ya sa suka ƙi ɗorawa gudun kada a banzantar musu da abin da suka sha wahala wajen tarawa. Amma shawarata ga mutane masu abin hannu su yi haƙuri su nemi nagartattun mutane su ɗora su a kan kasuwancinsu, su koya musu yadda za su dogara da kansu ko su ba su jari.

In ka zama dalilin arzikin wani ba ka san iya ladan da za ka samu ba a wajen Allah, lallai akwai mutanen kirki waɗanda babu ruwansu da abin da ba nasu ba, suna tsayawa tsayin daka wajen kulawa da duk abin da aka ɗora su a kansa, ba su san ha'inci ba, ba su san mugunta ba, ba su san cin amana ba, abinda su sani kaɗai a nan shi ne ba a yi wa mutane jam'i duk lalacewarsu domin kuwa tabbas sai an sami na kirki a cikinsu.

Ka'ida ta ƙarshe; duk wanda ya ci kuɗin da ba nashi ba sai ya biya a ranar da ba shi da abin biya sai kyakkyawan aikinsa, zai kuma riƙa gamuwa da bala'i kala daban-daban a cikin kabarinsa tun kafin a tashe shi ranar biya, wannan ƙa'idar ce za ta tabbatar maka da cewa   cin dukiyar mutane ba abin yi ba ne ga musulmi na ƙwarai!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Thursday, 2 July 2020

Karanta Nasihohin Da Zasu Amfane Ka A Harkokin Ka Na Kasuwanci

Karanta Nasihohin Da Zasu Amfane Ka A Harkokin Ka Na Kasuwanci

1. Ku sauƙaƙa farashin kayanku, idan ku ka siyo kaya da sauƙi ku siyar da shi da sauƙi, kada ku tsanantawa bayin Allah ta hanyar tsauwala farashin kayanku.

Nasihohi Ga 'Yan Kasuwa

MarubuciAbbati Mai Shago Flg

2. Ku taimakawa mabuƙata gwargwadon ikonku, kada ku wulaƙanta abokan hulɗarku ta hanyar faɗa musu zantuka marasa daɗin ji, idan aka taya kayanku ta hanyar wulaƙanci kada ku yi fushi.

3. Ku riƙa yin haƙuri a kan ƙananan abubuwa, ku zama masu tausayawa talakawa da tallafa musu a kan buƙatunsu na yau da kullum, abin da kuka bayar shi ne naku, wanda kuka ci a cikkunanku ya tafi, ba za ku same shi a Lahira ba, in ku ka bayar za ku sami abin da ku ka bayar ɗin har ma ku yi burin ina ma kun bayar da fiye da abin da ku ka bayar a lokacin da kuke raye!

4. Idan ku ka sayo kaya dayawa ko kaɗan zuwa wani lokaci ku ka sami labarin tashin kayan a kasuwa, ku ji tsoron ku siyarwa da mutane a farashin da ku ka kasance kuna siyarwa tun kafin ya tashi, ku bari sai kun siyo sabon kaya sai ku ƙara masa kuɗi.

5. Ku kula da waɗanda za ku bawa bashi, lallai wasu mutanen babu komai a tare da su in ban da son cutar da wanda ya yarda da su ko wanda yake taimaka musu, wannan ne ma ya sa za su zauna da kai kamar mutanen kirki a ƙarshe su cuce ka.

6. Ba na ce ku dena bayar da bashi ba ne, sai dai ku san wanda za ku bawa, haƙiƙa akwai nagartattun mutane waɗanda suke dawo da bashin da aka ba su ba tare da sun tauye shi ba.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng

Friday, 12 June 2020

Karanta Manyan Abubuwa 6 Da Zasu Faru Bayan Dakile Yaduwar Cutar Sarkewar Numfashi Ta Covid-19 A Duniya

Karanta Manyan Abubuwa 6 Da Zasu Faru Bayan Dakile Yaduwar Cutar Sarkewar Numfashi Ta Covid-19 A Duniya

Na san muna ta jira a gama Covid19 kamar yadda aka gama Ebola ko Lassa FEVER mu koma sha'anin mu kamar yadda muka saba ko? Kwarai za a kammala Covid-19 ba da daɗewa ba, kwayar cutar za ta mace a hannun magungunan da ake ta samarwa.

DUNIYA BA ZATA KOMA YADDA TAKE BA!!!

Marubuciya:- Rahma Abdulmajid

Sai dai tasirinta na iya wanzuwa nan da shekaru ɗari masu zuwa in ba wani iko na MAI duka ba.

Me ya sa ba za a koma yadda ake ba kamar yadda aka yi zamanin Ebola? Tambayar kenan ko? Amsar ita ce Ebola ƙasashen Rabbana aatina ta kassara waɗanda ko a Africa ma basu da farcen Susa, yayinda Covid19 kuwa ƙasashe ashirin masu makullan Sarrafa duniya ta maƙure wa wuya. Daga Babbar giwa China ta soma rarrafe sannan ta balaga a babbar Giwa Amurka bayan da ta saki rassa a kasashen G8 da Rasha.

Amma Wane irin tasiri za ta iya bari bayan ta mutu wanda ko Ɗan Adam ne ya mutu bai taɓa iya bari ba ballantana wata ƙwayar cutar da bata kai ƙwayar Zarra ba? Wannan ma tambaya ce, bari na lissafa amsoshin kamar haka:

1. Zai yiwu an kawo ƙarshen zama a Ofis a manyan ƙasashen duniya, Kamfanin Facebook da Goggle tuni suka bai wa ma'aikatansu hutun zuwa ofis har zuwa shekara ta 2021, wannan alama ce ta cewa kamfanoni da manyan ma'aikatu akan hanyarsu ta zuwa hutu sun fahimci cewa za a iya aiki daga gida, kenan babu buƙatar tara manyan gine gine da biyan kuɗin wuta, kayan kyale-kyale da kwamfutoci da ɗumbin haraji da ofis ke ƙallafa musu tunda ma'aikata za su iya aiki daga gida. Su ma ma'aikatan za su sami karin kuɗin kashewa idan aka cire musu kuɗin mota na zuwa ofis daga nauyin da suke ɗauka.

2. Manyan Birane za su dena samin cinkoso, kai zama su dena yi wa ƙauyuka tinkaho. Eh mana! Dama ofisoshin da suke da su ne ke janyo mutane su narka kuɗi don kama wani ƙaramin ɗaki da zaman mota don kawai a je ofis. Kenan mutum da ya baro ƙauye ya zo birni saboda aiki zai iya komawa ƙauyensa batare da ya rasa aikinsa ba tunda zai yi a ƙaton gidan da kuɗin ɗakin birni zai iya samar masa. Wannan zai sanya ƙauyuka su fara samin ababen more rayuwa muddin ƴaƴansu da suka ɗanɗana birmi za su dawo su nemi haƙƙinsu na rayuwa da walwala. Kenan za rasa cinkoso a irin Biranen New Delhi, New York, Beijin, da Moscow kamar yadda za a iya rasawa a Abuja da Lagos ko Qahira da Iskandariya, ko Cape town da Johannesburg a nan Africa.

3. Makarantu na iya komawa yanar gizo. Tun da aka fara Covid19 makarantu da dama sun ƙarye bayan da aka rufe su iyaye ba za su biya kuɗin 3rd term ba. Sannan a dole sun ƙirƙiri ɗakunan karatu na yanar gizo don iya tsira da ɗalibansu ko ba ko sisi. Garin haka iyayen sun fahimci za su iya sanya ƴaƴansu a makarantu masu tsadar gaske a zahiri tunda yanar gizo zata rage farashin kuɗin makaranta, sannan su ma makarantun sun fahimci za su iya rage nauyin malamai da ɗakunan karatu tunda idan aji na ɗaukar yara 20 da malamai biyu to a yanar gizo aji na iya ɗaukar ɗalibai dubu 20 da malami daya!.

4. Hijira zata tsaya cak! Eh mana, muddin ina da ƙwaƙwalwa da zan iya aiki daga ɗakina me zai sanya sai na yi hijira daga Moriki zuwa Abuja, ko da ga Malawi zuwa Amurka? Saboda Dala? To ai za a biya ni da Dala a ko ina.

5. Kuɗin takarda zai ƙarasa mutuwa. Kwarai a zaman sama da sati biyar da ƙasashen duniya suka yi a kulle an sami ƙaruwar kasuwancin yanar gizo inda maimakon samar da cinkoso a manyan shaguna sai aka riƙa aikin Delivery inda zaka buƙaci abu shagon ya aiko maka. Ko a ƙasar nan da ba mu da jan wuya an yi cinikin kayan salla ta social media. Sannan ƙananan shaguna ma ko a nan Africa sun fi gane su rataye lambar Acc a gaban shago ka yi musu Transfer in ka sayi abu, saboda tsoron yaɗa cutar ta hanyar kuɗin takarda. Hakan ya ƙara sanyawa burbushin Takarda da ake ta rajin ɓatarwa nan da 2030 na iya tafiya kafin 2021.

6. Fiye da kashi 70 na gidajen karuwai na duniya na iya zama kufai. Kwarai ina nufin karuwanci zai yi mugun raguwa muddin mazaje suka dena hijirar neman aiki nesa da iyalansu wanda hakan ke sanya su zama kayan karau a hannun karuwai, sannan matan za su ƙara ƙaimi wajen sake mallakar zukatan mazansu da suka rasa a baya wanda hakan ya kashe musu gwiwa ta hanyar sallamawa. Su ma karuwan zasu nemi wasu sana'o'in muddin kuɗin shiga ya ragu.

Me ake buƙata ne don tarbar wannan sauyi hannu bibbiyu? Na san wasu za su ce 5G ake buƙata kamar yadda labarai ke cewa dama shi ake son ƙaddamarwa ko? Ni dai ban sani ba, amma na san tabbas babu abinda ake buƙata na karɓan wannan sauyi hannu bibbiyu sai Bisimillah da Karɓan ƙwaƙƙwaran WIFI.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng

Wednesday, 20 May 2020

LOCKDOWN: KALLI YADDA KASUWANCI YA KOMA A JIHAR KANO

LOCKDOWN: KALLI YADDA KASUWANCI YA KOMA A JIHAR KANO

Ranaku biyu gwamnatin Kano ta sassauta a lockdown ɗin da ake ciki, wato Litinin da Alhamis don yin siyayya, a tsakanin ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

YADDA KASUWANCI YA KOMA A JIHAR KANO 

Marubuci:- Kabiru Yusuf Fagge

Amma a zahiri mutane na fitowa ne tun da asubar fari, wato tun ƙarfe 5 ko 6, kuma har zuwa ƙarfe 8 ko fiye na dare al'umma suna harkokinsu.

Kasuwannin 'Yankaba (na kayan miya) da 'Yanlemo (kayan marmari) kaɗai gwamnatin Kano ta amincewa su buɗe, sai kawai manyan kantunan siyar da kayan masarufi.

Amma gwamnati ta ƙi amincewa a buɗe manyan kasuwannin da ke Kanon kamar kasuwar Sabongari da ta haɗa duk irin kayayyakin da ake buƙata, da kasuwar Kantin Kwari ta shaddodi da atamfofi, da Kasuwar Wambai da Kasuwar Rimi da Kasuwar Singa ta kayan masarufi da sauransu.

Sai dai 'yan kasuwannin nan sun koma cin kasuwar tsaye da tsaye inda suke cika unguwannin da ke gefen ire-iren waɗannan kasuwanni musamman unguwar Fagge. Inda ake cika layuka ake kasa kayayyaki, kuma aka yi cunkus fiye da kasuwannin ma.

Hukumomin tsaro sun yi ƙoƙarin hana cin irin waɗannan kasuwannin, amma abin ya gagara.

An samu cunkuson ababen hawa fiye da yadda ake zato a duk manyan da ƙananan titunan da ke Kano, don wasu wuraren da za a iya zuwa a mintuna goma sai a yi awa ɗaya a hanya ana tafiya.

An yi bonono, wato rufe ƙofa da ɓarawo,domin tarin baki daga jihohin Nijeriya suna shigowa Kano a duk lokacin da aka ce an buɗe ɗin nan (ranakun Litinin da Alhamis) su yi siyayya, su fita.

Kayayyakin da ake buƙata sun yi matukar tsada. Waɗanda ba a buƙata kuwa masu su, suna karyarwa su siyar don su samu abin da za su siyi abinci.

Ta dalilin rufe kasuwanni, kayan wasu 'yan kasuwa za su lalace, musamman irin maya-mayai da sauransu, saboda zafi.

Al'umma ba sa yin amfani da takunkumin rufe hanci, ba a damu da tazarar tsakani ba (social distancing), ba a yawaita wanke hannu da sauransu.

Tabbas kasuwanci a Kano yana cikin wani hali, fatanmu Allah ya farfaɗo da shi, bayan an yarda za a rayu cikin wannan annoba, Allah Ya magance mana ita, Amin.

Hoto Daga: Hafiz Amin Fagge

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tuesday, 12 May 2020

Hanyar Da Kowa Yake Bi Yayi Arziki

Hanyar Da Kowa Yake Bi Yayi Arziki

Arziki nufin Allah ne, babu wani Mahaluki da yake azurtawa ko talautawa, babu wata nau'in sana'a ko kasuwa bayyananniya da aka ce a iya ita ake arziki, ba kasuwar da wani baiyi arziki ta silar ta ba, ba kuma kasuwar da wasu basu karye a cikin ta ba. Kai dai ka roƙi Allah ka kuma yi riƙo da sila ɗin.

Arziki Nufin Allah Ne

Marubuci:- Anas Darazo

Na tuna lokacin da Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba dabbobi (Akuya) ga mata suyi kiwo mutane sukai ta dariyar abun suna ganin hakan a matsayin renawa talaka hankali ko rashin sanin makamar aiki.

Yanzu sai naga wani bidiyo da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa tayi hira da wata mata da ta ci moriyar waɗancan dabbobi da gwamnatin jihar ta raba, matar tayi iƙirarin tafi ƙananan ma'aikatan gwamnati abun hannu, tunda har bashi suke zuwa karɓa a wurin ta su ce "sai ƙarshen wata" tace yanzu ma kenan nan gaba kam (idan suka ƙara haihuwa sukai yawa) tace manyan ma'aikatan ma zasu buga da su, ta bada labarin yadda Awakin guda uku da aka bata suka yaɗu daga haihuwar ɗaya zuwa uku har sukai yawan da take sayarwa take samun alheri tana ci tana sha ƴaƴan ta suna karatu.

Wannan shima misali ne ta yanda Allah Ya ke azurta bayin shi a wasu harkokin da mutane ke musu kallon ƙaskanci ko abun dariya, kada ka damu da wane irin kallo mutane suke yiwa kasuwancin ka, kai dai kayi kasuwancin da gaske ka nemi dacewa a wurin Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.