Wednesday 20 May 2020

LOCKDOWN: KALLI YADDA KASUWANCI YA KOMA A JIHAR KANO

Tura Wannan Zuwa Ga
Ranaku biyu gwamnatin Kano ta sassauta a lockdown ɗin da ake ciki, wato Litinin da Alhamis don yin siyayya, a tsakanin ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

YADDA KASUWANCI YA KOMA A JIHAR KANO 

Marubuci:- Kabiru Yusuf Fagge

Amma a zahiri mutane na fitowa ne tun da asubar fari, wato tun ƙarfe 5 ko 6, kuma har zuwa ƙarfe 8 ko fiye na dare al'umma suna harkokinsu.

Kasuwannin 'Yankaba (na kayan miya) da 'Yanlemo (kayan marmari) kaɗai gwamnatin Kano ta amincewa su buɗe, sai kawai manyan kantunan siyar da kayan masarufi.

Amma gwamnati ta ƙi amincewa a buɗe manyan kasuwannin da ke Kanon kamar kasuwar Sabongari da ta haɗa duk irin kayayyakin da ake buƙata, da kasuwar Kantin Kwari ta shaddodi da atamfofi, da Kasuwar Wambai da Kasuwar Rimi da Kasuwar Singa ta kayan masarufi da sauransu.

Sai dai 'yan kasuwannin nan sun koma cin kasuwar tsaye da tsaye inda suke cika unguwannin da ke gefen ire-iren waɗannan kasuwanni musamman unguwar Fagge. Inda ake cika layuka ake kasa kayayyaki, kuma aka yi cunkus fiye da kasuwannin ma.

Hukumomin tsaro sun yi ƙoƙarin hana cin irin waɗannan kasuwannin, amma abin ya gagara.

An samu cunkuson ababen hawa fiye da yadda ake zato a duk manyan da ƙananan titunan da ke Kano, don wasu wuraren da za a iya zuwa a mintuna goma sai a yi awa ɗaya a hanya ana tafiya.

An yi bonono, wato rufe ƙofa da ɓarawo,domin tarin baki daga jihohin Nijeriya suna shigowa Kano a duk lokacin da aka ce an buɗe ɗin nan (ranakun Litinin da Alhamis) su yi siyayya, su fita.

Kayayyakin da ake buƙata sun yi matukar tsada. Waɗanda ba a buƙata kuwa masu su, suna karyarwa su siyar don su samu abin da za su siyi abinci.

Ta dalilin rufe kasuwanni, kayan wasu 'yan kasuwa za su lalace, musamman irin maya-mayai da sauransu, saboda zafi.

Al'umma ba sa yin amfani da takunkumin rufe hanci, ba a damu da tazarar tsakani ba (social distancing), ba a yawaita wanke hannu da sauransu.

Tabbas kasuwanci a Kano yana cikin wani hali, fatanmu Allah ya farfaɗo da shi, bayan an yarda za a rayu cikin wannan annoba, Allah Ya magance mana ita, Amin.

Hoto Daga: Hafiz Amin Fagge

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user