Thursday 21 May 2020

KARANTA LOKACIN DA AKA WAJABTA YIN ZAKKA

Tura Wannan Zuwa Ga
Malamai sun yi saɓani game da lokacin da aka wajabta Zakka, waɗansu sun ce an wajabta ta ne a Makka, saboda ayoyin Makka waɗanda suka yi magana a kanta, wasu kuma suka ce an wajabta ta ne a Madina, saboda ayoyin Madina sun fi bayyana wajabcin ta.

Bayar da Taimakon Ka Ga Mai Neman Taimako...

Masu magana ta biyu sun fi kawo hujja mai ƙarfi, Inda suka ce musulmi a Makka daidaiwa ne, basu da tsari zartacce, ba su da hukuma, Ita kanta Zakkar ma ba ta da tsari wannan lokacin, watau ba ta da nisabi, ba a kuma ayyana waɗanda za a bai wa ba, don haka maganar da ta fi rinjaye ita ce, an wajabta Zakka ne a Madina, a shekara ta biyu bayan Hijira.

(Duba fiKhuz Zakkat na Dr. Yusuful Kardawi, Juz’I na 1 sh:52-62.)

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user