Sunday 19 July 2020

Shin Ko Kasan Abinda Zai Faru Da Wanda Yake Cin Bashi Amma Baya Biya?

Tura Wannan Zuwa Ga
Wasu mutanen sun mayar da cinye bashin da suka karɓa na kuɗi ko makamancinsa hanyar biyan buƙatunsu na rayuwa ta yadda in hulɗar kuɗi ta haɗa ka da su sai dai ka yi haƙuri ko ka nuna babu mutumci, in suka karɓi aron kuɗi ko wani abu a madadinsa ba za su biya ba, ban da rashin tausayi ba su biya abin da ake bin su a baya ba sai su zo da sunan a ƙara musu wani bashin za su haɗa su biya, kai jama'a!

KIN BIYAN BASHI BABBAN BALA'I NE!

MarubuciAbbati Mai Shago Flg

Wasu kuwa ba sa jin tsoron cinye ƙananan kuɗaɗen da aka biyo su ta hanyar siyayyar da suka yi ko siyayyar da aka yi a wajensu, in aka biyo su wani kuɗi sai a amince musu da sunan  za su bayar saboda mutumcinsu da ake gani, ashe ba haka abin yake ba sai su yi fuska su ƙi biya. Matsalar nan ma ba ta taƙaita ga manya kaɗai ba har zuwa yara; abin ban haushi sai ka jawo yara jikinka da sunan koya musu sana'a wacce za su riƙa samun kuɗin shiga tun kafin su girma ƙarshe sai su cuce ka.

Wasu manyan cuta a kan kuɗi haka ma wasu yaran, wannan ya sa tsoro ya shiga zuciyar masu abin hannu a kan in suka ɗora wasu a kan dukiyarsu za su wulaƙanta musu ita, hakan ya sa suka ƙi ɗorawa gudun kada a banzantar musu da abin da suka sha wahala wajen tarawa. Amma shawarata ga mutane masu abin hannu su yi haƙuri su nemi nagartattun mutane su ɗora su a kan kasuwancinsu, su koya musu yadda za su dogara da kansu ko su ba su jari.

In ka zama dalilin arzikin wani ba ka san iya ladan da za ka samu ba a wajen Allah, lallai akwai mutanen kirki waɗanda babu ruwansu da abin da ba nasu ba, suna tsayawa tsayin daka wajen kulawa da duk abin da aka ɗora su a kansa, ba su san ha'inci ba, ba su san mugunta ba, ba su san cin amana ba, abinda su sani kaɗai a nan shi ne ba a yi wa mutane jam'i duk lalacewarsu domin kuwa tabbas sai an sami na kirki a cikinsu.

Ka'ida ta ƙarshe; duk wanda ya ci kuɗin da ba nashi ba sai ya biya a ranar da ba shi da abin biya sai kyakkyawan aikinsa, zai kuma riƙa gamuwa da bala'i kala daban-daban a cikin kabarinsa tun kafin a tashe shi ranar biya, wannan ƙa'idar ce za ta tabbatar maka da cewa   cin dukiyar mutane ba abin yi ba ne ga musulmi na ƙwarai!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user